Babbar Magana: Trump zai Turo Daruruwan Sojojin Kasar Amurka Najeriya

Babbar Magana: Trump zai Turo Daruruwan Sojojin Kasar Amurka Najeriya

  • Amurka ta shirya turo sojoji akalla 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin kasar kan yaki da ‘yan ta’adda a yankuna daban-daban
  • Matakin na zuwa ne bayan hare-haren sama da Donald Trump ya bayar da umarni aka kawo wuraren da ake zargin na mayakan ISIS ne
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu manya a Amurka na matsa lamba ne kan yadda Najeriya ke tafiyar da batun tsaro da kare rayukan jama’a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Gwamnatin kasar Amurka na shirin turo sojoji kusan 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin kasar wajen yakar 'yan ta'adda.

Wannan na zuwa ne bayan shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin kai hare-hare a wuraren da ya bayyana a matsayin sansanonin kungiyar ISIS a Arewa ta Yamma.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na wani jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Reuters ya nuna cewa wani jami’in kasar Amurka ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 10, Faburairu, 2026 a wata sanarwa.

A makon da ya gabata, rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa ta tura karamar tawaga ta sojoji zuwa Najeriya, duk da cewa ba ta fayyace adadin ba.

Amurka za ta tura sojoji Najeriya

New York Times ta rahoto cewa sojojin Amurka 200 da za a turo za su kara karfi ne ga wasu jami’an sojin kasar da tuni suke Najeriya domin taimaka wa dakarun cikin gida.

Shugaba Trump ya sha bayyana cewa akwai yiwuwar karin matakan soja a Najeriya, yayin da rahotanni suka nuna cewa Amurka na leken asiri a sararin samaniyar Najeriya daga kasar Ghana tun daga karshen 2025.

Sai dai rundunar sojin Amurka da ke Afrika ba ta yi martani ba kan bukatar karin bayani da aka nema dangane da shirin tura karin sojojin.

Kara karanta wannan

Barazanar yaki: Trump ya bayyan yadda tattaunawar Amurka da Iran ta kasance

Matsin lamba da Amurka ke yi

Najeriya ta fuskanci matsin lamba daga Amurka bayan Trump ya zargi kasar da gaza kare Kiristoci daga hare-haren 'yan ta'adda.

Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa ana tsananta wa Kiristoci, tana mai cewa sojojin kasar na kai farmaki kan ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai.

Kungiyoyin Boko Haram da ISWAP na cigaba da kai hare-hare kan sojoji da fararen hula a yankin Arewa maso Gabas da wasu sassan Arewa maso Yamma.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wani taro a 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tasirin sojojin Amurka a Najeriya

Masu sharhi kan harkokin tsaro na ganin cewa tura karin sojojin Amurka na iya taimaka wa wajen inganta kwarewar sojojin Najeriya ta fuskar dabarun yaki, tattara bayanan sirri da kuma dakile hare-haren kwanton bauna.

Sai dai wasu na gargadin cewa dole ne matakin ya girmama martabar kasa da kuma tabbatar da cewa jagorancin yaki da ta’addanci ya ci gaba da kasancewa a hannun hukumomin Najeriya.

Sojojin Amurka sun dura Abuja

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta bullo, an yi hasashen abin da sojojin Amurka za su yi a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya karbi tawagar sojojin Amurka a fadar Aso Rock Villa.

Fadar shugaban kasa ta sanar da ganawa da sojojin a Abuja, duk da cewa bata fitar da sanarwa game da abubuwan da suka tattauna ba.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da wasu manyan sojojin Najeriya sun halarci zaman da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng