Yan Majalisar Amurka Sun Kwaye wa Najeriya baya kan Kwangilar Kamun Kafar Trump
- Kwamitin Majalisar Dokokin Amurka ya soki yarjejeniyar kamun kafa na $9m da gwamnatin Najeriya ta kulla a Washington
- ‘Yan majalisa sun ce ana iya amfani da wannan tsari wajen rage girman keta ‘yancin addini da take-hakkokin dan Adam
- An yi kira da a hada sanya Najeriya a jerin CPC da takunkumi masu tsauri domin tilasta sauyi a kan zargin kisan kiristoci a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
America – Majalisar Dokokin Amurka ta yi kakkausar suka kan yarjejeniyar kamun kafa da aka ruwaito gwamnatin tarayyar Najeriya ta kulla da wani kamfani a Washington.
Rahotanni sun ce Najeriya ta bayar da kwangilar $9m domin a yi kokarin wanke zargin da Shugaban Amurka, Donlad Trump da wasu jiga-jigai a Amurka ke yi wa Najeriya.

Kara karanta wannan
Zance ya kare, hedkwatar tsaro ta yi magana kan sojojin Amurka da aka turo Najeriya

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa ‘yan majalisan Amurka sun bayyana damuwa cewa ana iya amfani da yarjejeniyar wajen rage girman keta ‘yancin addini da take-hakkokin dan Adam da ake zargin suna faruwa a Najeriya.
'Yan majalisar Amurka sun dura a kan Najeriya
'Yan majalisa sun bayyana rashin jin dadi a kan kwangilar ne a wani zaman sauraron ra’ayi na hadin gwiwa tsakanin Kwamitin Majalisar Wakilai kan Afrika da kuma Kwamitin Yankin Yammacin Duniya.
Zaman ya karbi shaidar tsohon Jakadan Amurka na Musamman kan ‘Yancin Addini a Duniya, Sam Brownback, da kuma tsohon shugaban Hukumar hukumar USCIRF, Dr. Stephen Schneck.
Shugaban Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Wakilai kan Afrika, Chris Smith, ya kare matakin da aka dauka a watan Oktoban 2025 na sanya Najeriya cikin jerin kasashe da ake da damuwa a kansu.
Ƴan majalisa sun yi tir da kwangilar Najeriya
Sai dai Smith ya bayyana damuwa matuka kan kokarin da ake yi na kalubalantar wannan matsayi ta hanyar amfani da kamfanin kamun kafa.

Kara karanta wannan
Kalaman Kwankwaso na taimaka wa Abba Kabir a shari'ar 2019 sun jefa shi a matsala
Ya ce Najeriya ta dauki hayar kamfanin DCI a kan $9m, wato kimanin $750,000 a kowane wata domin kokarin wanke zargin da ake yi mata na kashe kiristoci.

Source: Getty Images
Ya kuma bayyana cewa wani attajirin Najeriya ya shiga yarjejeniyar $120,000 a wata da kamfanin Valcour da ke Washington domin yin tasiri ga Majalisa da bangaren zartarwa.
A cewarsa, irin wadannan kamfanoni na rubuta bayanai masu kyau da ke kokarin nuna cewa babu matsala, alhali ana kokarin rage girman matsalolin da ke akwai ne.
Sai dai a ra'ayinta, 'yar majalisa da ke wakiltar ‘yan adawa a kwamitin, Sara Jacobs, ta soki yadda ake mayar da rikicin Najeriya kan Kiristoci kadai.
Jacobs ta yi gargadi cewa saukaka rikicin Najeriya zuwa bangare guda na addini kadai na iya kara hura wutar sabani a kasa.
Ta kuma soki hare-haren sojin Amurka da aka kai a Sakkwato a lokacin Kirsimeti, tana cewa ba su taimaka wa al’ummomin da ke fama da rikici ba.
'Dan majalisar Amurka ya yi magana kan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa 'dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya bayyana damuwa kan duk wani yunƙuri da ke neman rikitar da Najeriya ta hanyar ƙarfafa ra’ayin ’yan aware.

Kara karanta wannan
An samu sabani tsakanin Majalisar Dattawa da ta wakilai wajen gyara dokar zaben Najeriya
Moore ya yi wannan gargadi ne bayan kammala wata ziyara ta bincike da ya kai Najeriya, inda ya ce manufarsa ita ce fahimtar zarge-zargen cin zarafin Kiristoci da ake cewa na faruwa a wasu sassan ƙasar.
Ya jaddada cewa duk wani yunƙuri na raba Najeriya ko hura wutar rikici zai iya haifar da mummunan sakamako ba ga Kiristoci kaɗai ba, har ma da Musulmi da sauran al’ummomin ƙasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng