'Kiran Allah': Saudiyya Ta Fadi Ranar da Za Ta Fara ba da Bizar Aikin Hajjin 2026
- Ma’aikatar Hajji da Umara ta Saudiyya ta sanar da cewa za ta fara bayar da bizar aikin Hajji na shekarar 2026 daga ranar 8 ga Fabrairu
- Kimanin maniyyata 750,000 ne suka yi rajista zuwa yanzu yayin da rukunin farko za su isa Saudiyya ranar 18 ga Afrilu, 2026
- Saudiyya ta ce ta kammala shirye-shiryen tarbar maniyyata daga kasashen waje yayin da ta gargadi hukukomin Hajji na duniya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Saudiyya - Ma'aikatar Hajji da Umrah ta ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa za ta fara bayar da bizar aikin Hajji na shekarar 2026 (1447 AH) daga ranar 8 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Wannan mataki yana daga cikin ƙoƙarin ma'aikatar na ganin an kammala shirye-shirye watanni kafin lokacin aikin Hajji ya yi domin sauƙaƙa wa maniyyata hanyoyin gudanar da ibada.

Kara karanta wannan
Saudiyya ta kafe kan bakarta, Musulmai za su fuskanci sharuda masu tsauri a Hajjin 2026

Source: Getty Images
An sanya ranar fara ba da bizar Hajji
Hukumomin Saudi Arabia sun bayyana cewa sun fara wannan shiri ne tun ranar 8 ga watan Yunin 2025, inda aka ba ofisoshin Hajji na duniya damar tsara ayyukansu cikin lokaci, in ji rahoton Gulf News.
A cewar jadawalin, an riga an kammala yarjejeniyoyin masauki a biranen Makka da Madina, tare da tsare-tsaren sufuri da sauran ayyuka a wurare masu tsarki tun a watan Janairu, 2026.
Bayan fara bayar da biza a ranar 8 ga Fabrairu 2026, ana sa ran kammala dukkan shirye-shiryen takardun tafiya a watan Maris 2026, tare da miƙa bayanan maniyyata kafin isowarsu.
Ma'aikatar ta sanar da cewa rukunin farko na maniyyata za su fara isa ƙasar Saudiyya ne daga ranar 18 ga watan Afrilu, 2026 (wato 1 ga watan Zul-Ƙada 1447 AH).
Nasarorin da aka samu kan shirin aikin Hajji
Zuwa wannan lokaci, kusan mutane 750,000 ne suka riga suka yi rajistar aikin Hajji, ciki har da mutum 30,000 da suka biya kuɗin aikin kai-tsaye daga ƙasashensu.
Hukumar ta ware kusan sansanoni 485 ga mahajjata daga ƙasashen waje a wurare masu tsarki, yayin da ofisoshin Hajji guda 73 suka riga suka kammala aiwata rda dukkan buƙatun kwangila.
Ma'aikatar ta jaddada amfani da manhajar Nusk Masar da asusun kuɗi na zamani domin gudanar da harkokin kuɗi cikin gaskiya da kuma guje wa rudani wajen yin odar wani abu, in ji rahoton Times of India.

Source: Getty Images
Gargaɗi ga hukumomin Hajji na duniya
Ma'aikatar ta yi kira ga hukumomin Hajji na kowace ƙasa da masu kula da mahajjata masu zaman kansu da su bi jadawalin da aka shimfiɗa daki-daki domin tabbatar da tsaro da ingancin aikin.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Yin shiri da wuri shine ginshiƙin gudanar da aikin Hajji mai inganci, aminci, da kuma daraja ga dukkan baƙin da suka kawo ziyara dakin Allah.”
Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da cewa an riga an kammala dukkan shiri na tarbar maniyyata a masauki da sansanonin da ke cikin kasa mai tsarki.
Musulmai za su fuskanci tsauraran sharudda
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma’aikatar Hajji da Umrah ta ƙasar Saudiya ta fitar da gargaɗi ga dukkan ƙasashen da ke shirin zuwa aikin Hajjin 2026.
Ma'aikatar ta jaddada cewa 8 ga Fabrairu, 2026, ita ce rana ta ƙarshe ga kowace kasa ta kammala tura bayanan mahajjata da kuma shigar da su a shafin Nusuk Masar.
Wannan mataki ne mai muhimmanci ga fitar da biza, yayin da hukumomin Saudiyya suka sanya 20 ga Maris, 2025 a matsayin rana ta ƙarshe na kammala ayyukan biza
Asali: Legit.ng

