Musulunci Ya Samu Karuwa, Babban Mawaki a Birtaniya Ya Karbi Kalmar Shahada

Musulunci Ya Samu Karuwa, Babban Mawaki a Birtaniya Ya Karbi Kalmar Shahada

  • Fitaccen mawakin Birtaniya, Central Cee, ya sanar da karɓar addinin Musulunci tare da furta kalmar shahada
  • Mawakin ya bayyana sauyin rayuwarsa ne a wani bidiyon kai tsaye, inda ya ce ya canja suna kuma yanzu shi Musulmi ne
  • Wannan mataki ya zama babbar alama ta sauyin rayuwa gare shi inda abokansa suka taya shi murna bayan ya tabbatar da karɓar Musulunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

London, England - Fitaccen mawakin na kasar Birtaniya, Central Cee, ya sanar da cewa ya karɓi addinin Musulunci.

Mawakin da aka fa sani da sunan Oakley Neil Caesar-Su ya tabbatar da karbar kalmar shahada wanda ke tabbatar da ya koma addinin Musulunci.

Mawaki a Birtaniya ya karbi addinin Musulunci
Matashin mawaki daga Birtaniya, Central Cee da ya karbi Musulunci. Hoto: Central Cee.
Source: Instagram

Matashin mawaki a Birtaniya ya karbi Musulunci

Mawakin wakar “Band 4 Band” ya bayyana hakan ne a wani bidiyon kai tsaye da ya yi kwanan nan, wanda jaridar Royal News ta bibiya.

Kara karanta wannan

Bayan kyautar N100m, gwamna Abba ya dauki matakai a kan gobara a kasuwar Kano

Jim kadan bayan kammala bidiyon da ya yi, abokansa da dama sun taya shi murna bayan ya tabbatar da karɓar Musulunci.

Central Cee ya ce:

“Na sauya sunana kuma na karɓi shahada, yanzu ni Musulmi ne.”

Kafin wannan sanarwa, mawakin bai taba bayyana a bainar jama’a wane addini yake bi ba, sabuwar sanarwar tasa ta nuna wani muhimmin sauyi a rayuwarsa ta addini.

Takaitaccen tarihin mawakin da ya karbi Musulunci

An haifi Central Cee a ranar 4 ga watan Yuni, 1998, a birnin Landan, mahaifiyarsa ’yar Ingila ce, yayin da mahaifinsa ke zama dan asalin Guyana da China.

Iyayen mawakin sun rabu tun yana da shekaru bakwai, inda aka tashe shi a unguwar Shepherd’s Bush tare da mahaifiyarsa da ’yan uwansa maza biyu ƙanana.

Central Cee ya fara harkar waka tun shekarar 2014, inda ya fara fitowa a shirin 'Fire in the Streets' wanda ya samu daukaka sosai.

Matashin mawakin ya samu karɓuwa sosai bayan fitar wakarsa “Day in the Life” a watan Yunin shekarar 2020 wanda ya kara daga darajarsa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kunyata matarsa a bainar jama'a bayan ta yi kokarin kin sumbatarsa

Tun daga lokacin, mawakin ya zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman wakar UK drill, inda ya yi fice a duniya baki ɗaya, cewar rahoton Daily Post.

Musulunci ya samu karuwa a Birtaniya bayan shigar mawaki
Mawaki a Birtaniya da ya yi suna a Birtaniya, Central Cee. Hoto: Central Cee.
Source: Instagram

Martanin da mutane suka yi kan lamarin

Har ila yau, wani ami amfani da kafar X, BASITO ya wallafa faifan bidiyon da mawakin yake tabbatar da shiga Musulunci.

Wannan sauyi da mawakin ya samu a rayuwa ya samu ra'ayoyi mabambanta daga al'umma da suka tofa albarkacin bakinsu.

Mafi yawan wadanda suka yi tsokaci sun taya shi murna da cewa yana yan 'yancin zabar rayuwar da ya ga ta fi masa.

An kammala shirin mayar da coci masallaci

A wani labarin da ke da alaka da Birtaniya da Musulunci, an ji cewa hukumomi a Watford sun amince da shirin sauya tsohon cocin St Thomas zuwa masallaci.

Majalisar ta ce amfanin da al’umma za su samu ya fi matsalar ajiye motoci da wasu suka nuna hakan zai taimaka wa mutane a yankin.

Sabon masallacin zai kunshi makarantar yara da wuraren taron al’umma, kuma ana sa ran bude shi a wannan bazarar da ke tafe domin ci gaban yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.