Turkiyya Ta Shirya Taimakon Najeriya bayan Kisan Musulmi kusan 200 a Kwara

Turkiyya Ta Shirya Taimakon Najeriya bayan Kisan Musulmi kusan 200 a Kwara

  • Gwamnatin kasar Turkiyya ta bayyana baƙin ciki tare da kakkausar suka kan hare-haren ‘yan bindiga a ƙauyukan Kwara
  • Akalla mutane 78 aka riga aka birne, yayin da ake fargabar adadin mamatan zai kai kusan 170 kuma ana ci gaba da gano wasu
  • Harin ya tashi hankalin mutanen Kwara da sauran sassan Najeriya bayan 'yan ta'addan sun kwana suna zubar da jinin bayin Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara – Gwamnatin ƙasar Turkiyya ta bayyana jimami da matuƙar baƙin ciki kan munanan hare-haren ‘yan bindiga da suka auku a ƙauyuka biyu na jihar Kwara.

Wani mummunan hari da 'yan ta'adda suka kai a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairu, 2026 ya yi sanadin salwantar rayukan jama’a da dama.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Turkiyya ta yi tir da harin yan ta'adda a jihar Kwara
Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyib Erdogan da Shugaban Najeriya Bola Tinubu Hoto: Anadolu/Getty
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa hare-haren sun girgiza al’umma, inda rahotanni suka nuna cewa daruruwan mazauna yankin sun tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu.

Gwamna ya yi tir da kashe Musulman Kwara

The Nation ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa an kashe mutanen ne bayan da suka ƙi miƙa wuya ga masu tsattsauran ra’ayi da ke wa’azin wata baƙuwar akida.

Ya ce lamarin ya nuna irin ta’addancin da ke ƙara bazuwa a wasu sassan ƙasar nan, tare da barazana ga zaman lafiya da haɗin kan al’umma.

Gwamna AbdulRazaq ya ce:

“An yi wa Musulmai 75 na kisan kiyashi a cikin gidajensu.”

Martanin Turkiyya kan harin Najeriya

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Turkiyya ta yi kakkausar suka kan harin, tare da jaddada goyon bayanta ga Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci.

Turkiyya za ta kara taimaka wa Najeriya bayan kisan Musulmi a Kwara
Taswirar jihar Kwara inda aka kashe Musulmi kusan 200 Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga uku, sojoji sun sha alwashi kan harin Kwara

“Muna matuƙar baƙin ciki kan asarar rayuka sakamakon harin ta’addanci da ya faru a jihar Kwara, Najeriya. Muna kakkausar suka kan wannan mummunan hari, tare da miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma ga al’ummar Najeriya. Turkiyya za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya a yaƙinta da ta’addanci.”

Tuni gwamnatin Najeriya ta bayyana takaici tare da ikirarin nemo mutanen da suka aikata wannan danyen aiki domin su fuskanci hukunci.

Wannan hari na biyo makamancinsa da yan ta'adda suka yi a garin Borgu a jihar Neja, inda suka bi mutane a kasuwanni da gidaje suka yi masu yankan rago.

Sojoji na neman maharan Kwara

A baya, mun wallafa cewa ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai hare-haren ta’addanci a wasu sassan jihar Kwara, lamarin da ya girgiza al’umma matuka.

Rahotanni sun nuna cewa irin wannan hari bai taba faruwa a yankunan ba, inda aka kashe mutane da dama tare da lalata gidaje da dukiyoyin jama’a.

Harin ya faru ne a daren wata rana, lokacin da maharan suka rika shiga kauyuka suna harbi ba tare da kakkautawa ba, tare da toshe hanyoyin tsira ga mutanen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng