An Kashe 'Yan Najeriya 4 bayan 'An Yaudare Su' Sun Taya Rasha Yaki da Ukraine

An Kashe 'Yan Najeriya 4 bayan 'An Yaudare Su' Sun Taya Rasha Yaki da Ukraine

  • An kashe ‘yan Najeriya hudu da aka dauka aiki a Rasha bayan an tura su fagen yaki a Ukraine yayin da ake ci gaba da gwabza fada
  • Rahotanni sun yaudare su da tayin za a ba su aikin tsaro kafin a tilasta masu shiga aikin soja bayan sun isa kasar
  • Iyalan mamatan sun ce ba a taba tuntubar su daga hukumomin Rasha ba duk da an kashe masu 'yan uwa a fagen daga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Rasha – Akalla ‘yan Najeriya hudu da aka dauka aiki domin yin fada a bangaren kasar Rasha a yakin Ukraine sun rasa rayukansu a fagen daga.

Bincike ya gano cewa ‘yan Najeriyan da aka kashe sun hada da Adam Anas, Akinlawon Tunde Quyuum, Abugu Stanley Onyeka da Balogun Ridwan Adisa.

Kara karanta wannan

'Mutane sun yi ta kansu,' Halin da ake ciki a garin da aka kashe sojan Najeriya

An zargi Rasha na yaudarar yan Najeriya su tafi aikin soja a yakinta da Ukraine
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin Hoto: Contributor
Source: Getty Images

Binciken da ya kebanta ga Daily Nigerian ya gano cewa an dauke su ne da sunan ba su aikin “tsaro”, amma bayan horo na makonni uku aka tilasta masu shiga aikin soja tare da tura su dagen daga.

'Yan Najeriya sun shiga yakin Rasha da Ukraine

Rahotanni sun nuna cewa Anas, Quyuum, Onyeka da kuma Abubakar Adamu, wanda shi kadai ya tsira sun yi tafiya tare a watan Nuwamba, 2025, yayin da Adisa aka dauke shi tun farkon shekarar.

Majiyoyi sun ce ‘yan Najeriyan sun mutu a fagen daga a lokuta mabambanta tsakanin Disamba, 2025 zuwa Janairu, 2026.

Binciken ya nuna cewa sojojin Rasha ba su tuntubi iyalan mamatan ba, sannan sun gargadi sauran ‘yan Afrika da ke fada kada su sanar da iyalai.

An yaudari 'yan Najeriya wajen shiga aikin soja

An gano cewa labarin mutuwar ‘yan Najeriyan ya fara fitowa ne a wata kungiyar WhatsApp ta ‘yan Afrika da ke yaki a Ukraine.

Kara karanta wannan

Harin Kwara ya kara muni, adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura 80

Wani dan uwan Adam Anas ya ce:

“Mun ji labarin mutuwarsa ne daga wani abokinsa. An wallafa hotonsa a dandalin WhatsApp na wata kungiyar yan Afrika. Ba a taba tuntubar iyalinmu daga hukumomin Rasha ba."

Matsalolin Anas da abokan tafiyarsa sun fara ne bayan sun amince da tayin aikin “tsaro” daga wani wakilin daukar ma’aikata dan Najeriya mai suna Emiola Muhammad.

Ana zargin Rasha da yaudarar yan Najeriya suna shiga yaki a kasar
Shugaban Rasha, Vladimir Putin Hoto: Contributor
Source: Getty Images

Jakadancin Rasha da ke Abuja, tare da hadin gwiwar wakilin daukar ma’aikatan, ya ba su bizar yawon bude ido sau daya kacal ba tare da daukar bayanansu ba.

An yi masu alkawarin albashin wata-wata na ruble 200,000, kimanin Naira miliyan 3.6, tare da alawus-alawus da sauran gata.

Da isarsu filin jirgin saman Sheremetyevo da ke Moscow, an karkatar da ‘yan Najeriyan daga layin binciken shige da fice zuwa wata hanya ta daban.

A cikin wata wasika da jaridar ta samu, ma’aikatar tsaron Rasha ta umarci jami’an iyaka da su ba su izinin shiga domin daukar kwangilar aikin soja.

Kara karanta wannan

Halin da iyalan mafarauta 16 da aka kashe a Edo suke ciki, sun magantu kan diyya

Mutane hudu sun rasu a yakin Ukraine da Rasha
Anas Adam, daya daga cikin mutanen da suka rasu a yakin Rasha da Ukraine Hoto: Jaafar Jaafar/Anas Adam
Source: Facebook

An tilasta masu sanya hannu kan kwangilar da aka rubuta da harshen Rasha ba tare da fassara zuwa Turanci ba.

Daga nan aka kai su sansanin soja inda suka yi horo na makonni uku kafin a tura su fagen daga.

A wata murya ta karshe da Anas Adam ya aika wa abokinsa, ya ce:

“Don Allah ku yi mana addu’a, muna tsakiyar daji. Tafiya ce ta makonni biyu a kafa, kuma hanyar tana da hatsari saboda jiragen yaki marasa matuka.”

A halin yanzu, dan Najeriyan da ya tsira, Abubakar Adamu, ya aika da kiran gaggawa ga gwamnatin tarayya ta hannun lauyansa, yana rokon a ceto shi da mayar da shi gida.

'Dan Najeriya ya mutu a yakin Rasha

A baya, mun wallafa cewa dan jarida mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Jafar Jafar, ya yi kakkausar gargadi ga matasan Najeriya da ke sha’awar barin ƙasar domin zuwa Rasha.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotanni na matasan Afrika, daga ciki har da ’yan Najeriya, da ke barin ƙasashensu zuwa waje domin shiga yaƙe-yaƙe.

Jafar Jafar ya bayyana cewa ya samu sahihan bayanai kan mutuwar wani matashi ɗan Najeriya daga Kano, Anas Adam, wanda ya tafi Rasha domin shiga aikin soja, inda aka kashe shi a fagen daga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng