Majalisar Amurka Ta Ki Hakura, Za a Kuma Zama kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya

Majalisar Amurka Ta Ki Hakura, Za a Kuma Zama kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya

  • Majalisar Dokokin Amurka za ta sake gudanar da zama kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
  • Wasu Kiristoci a Najeriya da suka je bayar da shaida sun ce kasar na fuskantar barazanar rikicin addini
  • Wannan zama da za a sake na zuwa ne bayan da Amurka ta aiko sojojinta zuwa Najeriya awanni kadan da suka wuce

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Majalisar Dokokin Amurka na shirin gudanar da wani zama na musamman a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairu, 2026 domin sauraron shaidu kan zargin kisan kiyashi da tsananta wa Kiristoci a Najeriya.

Zaman, wanda aka sanya wa suna “kare 'yancin addini a fadin duniya”, zai gudana ne a gaban Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Wakilai.

Kara karanta wannan

Bayan turo sojoji Abuja, Amurka ta yi maganar yakar 'yan ta'adda a Najeriya

Amurka za ta sake zama a kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto; Donald J Trump
Source: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa za a gudanar da zaman ne tare tsakanin ƙaramin kwamitin Afrika da kuma ƙaramin kwamitin Yankin Yammacin Duniya na Majalisar Wakilai.

Amurka na ci gaba da zarginta kan Najeriya

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kafin zaman, an riga an fitar da bayanan shaidun da za su gabatar da hujjoji, inda suka yi gargaɗi akwai maganar rikicin Musulmi da Kiristoci a kasar.

Daga cikin shaidun da ake sa ran za su bayyana a gaban kwamitin akwai tsohon jakadan Amurka kan ’yancin addini a duniya, Sam Brownback da Grace Drexel, ’yar fasto Ezra Jin.

Haka kuma Dr. Stephen F. Schneck, tsohon shugaban Hukumar Amurka kan ’Yancin Addini ta Duniya, shi ma zai bayyana domin bayar da bayanan da ya shirya.

A cikin rubutacciyar shaidarsa da aka fitar kafin zaman, Brownback ya yi zargin cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na kai hari kan Najeriya a matsayin wani ɓangare na yaƙin addini na duniya.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Amurka ta turo karin wasu sojoji wata 1 bayan hari a Najeriya

'Yan majalisar Amurka za su karbi jawabai daga shaidun da suka aminta da su a kan Najeriya
Riley Moore, daya daga cikin yan gaba da ke zargin ana kisan Kiristoci a Najeriya bayan ya zo kasar Hoto: Riley Moore
Source: Twitter

Ya ce ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na ci gaba da ƙoƙarin kawar da sauran addinai a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika, inda ya bayyana Najeriya da Siriya a matsayin manyan wuraren da suke mayar da hankali.

An yi gargadi a kan Najeriya

Brownback ya kuma yi gargaɗi cewa alamun yaƙin Musulmi da Kiristoci na ƙara bayyana a nahiyar Afrika, yana mai cewa Najeriya ce kasa mafi haɗari a duniya ga Kiristoci.

Haka kuma ya yi iƙirarin cewa gwamnatin Najeriya na neman tallafi daga ƙasashe irin su China, Rasha, Turkiyya da Saudiyya.

A nasa ɓangaren, Dr. Schneck ya bayyana cewa rashin tsaro da raunin shugabanci na haifar da yanayin tsananta wa addinai.

Ya ce ƙasashe masu rauni na zama mafaka ga ƙungiyoyin ’yan bindiga, na kabilanci ko na addini, tare da ƙara jaddada cewa Najeriya na cikin ƙasashen da irin wannan yanayi ya riga ya bayyana.

Schneck ya kuma nuna damuwa kan jinkirin fitar da rahotannin ’yancin addini na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, da kuma rashin sabunta jerin ƙasashen da ake zargi.

Kara karanta wannan

Barawon motar Naira miliyan 75 ya yi wa 'yan sanda barkwanci a Kano

Gwamnatin Najeriya ta sha musanta zargin matsa wa Kiristoci, tana mai cewa matsalar tsaro na shafar ’yan ƙasa ne ba tare da la’akari da addini ba.

Tawagar Amurka ta ziyarci Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa tawagar majalisar dokokin Amurka ta shiga Najeriya a wani yunkuri na ci gaba da bincike da tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci.

Shugaban Amurka da wasu daga cikin kusoshin gwamnatinsa sun sako Najeriya a gaba da zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi, kuma da gayya.

A ranar Lahadi, 7 ga watan Disamba 2025, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya karɓi tawagar a Abuja, inda suka tattauna kan batutuwan tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng