An Fara: Amurka Ta Harbo Jirgin Leken Asirin Kasar Iran a tsakiyar Teku

An Fara: Amurka Ta Harbo Jirgin Leken Asirin Kasar Iran a tsakiyar Teku

  • Sojojin Amurka sun ce sun harbo wani jirgin leƙen asirin Iran bayan ya kusanci jirgin ruwan yaki na USS Abraham Lincoln cikin yanayi mai tayar da hankali
  • Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake zargin cewa sojojin kasar Iran sun tsoratar da wani jirgin kasuwanci mai tutar Amurka a mashigar Hormuz
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun saka a dangantaka tsakanin Amurka da Iran kan batun tsaro da shirin mallakar makamin nukiliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran – Sojojin ruwan Amurka sun tabbatar da cewa sun harbo wani jirgin leƙen asirin Iran maras matuki bayan ya kusanci jirgin ruwan yaki na USS Abraham Lincoln a Tekun Arabia.

Sojojin Amurka sun bayyana cewa jirgin ya ki ja da baya a lokacin, duk da matakan sassautawa da aka ɗauka domin kauce wa rikici.

Kara karanta wannan

Trump ya saki sunayen 'yan Najeriya 79 da za su fuskanci fushinsa

Ayatollah Khamenei da shugaban kasar Amurka
Ayatollah Khamenei a hagu, jirgi maras matuki a tsakiya da Donald Trump a dama. Hoto: Getty images
Source: Getty Images

Rahoton AP News ya nuna cewa wannan lamari na iya ƙara tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman a wannan lokaci da ake ci gaba da barazanar ɗaukar matakin soja.

Amurka ta harbo jirgin kasar Iran

Rundunar sojojin Amurka ta bayyana cewa jirgin leƙen asirin Iran ya kusanci jirgin ruwan yaki na USS Abraham Lincoln a cikin ruwan kasa da kasa ba tare da bayyanannen dalili ba.

Kakakin rundunar, Kyaftin Tim Hawkins, ya ce jirgin ya ci gaba da matsowa kusa duk da gargadi da matakan sassautawa da sojojin Amurka suka ɗauka.

Daga bisani, wani jirgin yaki samfurin F-35C daga cikin jiragen USS Abraham Lincoln ne ya harbo jirgin leƙen asirin domin kare lafiyar jirgin ruwan da ma’aikatansa.

Dalilin Amurka na harbo jirgin Iran

Sojojin Amurka sun ce lokacin da aka harbo jirgin, USS Abraham Lincoln na tafiya ne kimanin mil 500 daga gabar kudancin Iran.

An bayyana cewa babu wani sojan Amurka da ya jikkata, haka kuma babu wani kayan aikin soja da ya lalace sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Binciken yunkurin juyin mulki ya sa an kama tsohon Janar mai rike da sarauta

Rundunar ta ce matakin da aka ɗauka ya dace da dokokin kare kai da kuma kiyaye tsaron jiragen ruwa a ruwan kasa da kasa.

Martanin Iran kan harbo jirginta

Kafafen yada labaran gwamnatin Iran sun ruwaito cewa dakarun juyin juya halin kasar suna binciken abin da suka kira katsewar aikin jirgin leƙen asirin.

Kafar yada labarai ta Tasnim da ke da alaka da gwamnati ta ce kafin harbo shi, jirgin ya samu damar tura bayanan hotunan da ya ɗauka zuwa ga hukumomin Iran.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump ya bata rai bayan wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta tsorata jirgin kasuwanci

Bayan harbo jirgin leƙen asirin, sojojin Amurka sun ce wasu jiragen ruwa na Iran tare da wani jirgin leƙen asiri sun tsoratar da wani jirgin kasuwanci mai suna Stena Imperative a mashigar Hormuz.

Rahoton ya ce jiragen sun kusanci jirgin kasuwancin cikin sauri tare da barazanar shiga ciki da kwace shi, jirgin yaki na USS McFaul ya kai ɗauki tare da rakiyar jirgin kasuwancin har sai da ya ci gaba da tafiya lafiya.

Trump ya tura jirage kusa da Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka ya bayyana cewa ya tura karin jiragen yaki yankin Gabas ta Tsakiya a shirin fada da Iran.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda aka tsara harbe ministan tsaro, Janar Christopher Musa

Hakan na zuwa ne bayan cigaba da magana a kan cewa zai hana Iran mallakar makamin nukiya saboda barazanar tsaro a duniya.

Donald Trump ya bayyana cewa zai dauki matakin kai hari Iran matukar ba ta ajiye shirin mallakar makamin nukiliya da ya ce ta fara ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng