Jerin Kasashe 9 da Kudadensu Suka Fi Dalar Amurka Daraja a Duniya

Jerin Kasashe 9 da Kudadensu Suka Fi Dalar Amurka Daraja a Duniya

Darajar kuɗi ba wai tana nuna girman tattalin arzikin ƙasa ba ne kawai, har ma tana nuna ƙarfin sayayya da kuma yadda duniya ta amince da wannan kuɗin.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Duk da cewa dalar Amurka ce aka fi amfani da ita a fadin duniya, amma akwai kuɗaɗen wasu kasashen da suka nunka ta daraja a kasuwannin duniya.

Dinarin Kuwait ne kudi mafi daraja a duniya a 2026
Mohammad al-Hashel, gwamnan babban bankin kasar Kuwait yana nuna hotunan sababbin takardun Dinarin Kuwait a ranar 19 ga Mayun 2014. Hoto: YASSER AL-ZAYYAT / Stringer
Source: Getty Images

Kudin kasashe 10 mafi daraja a duniya

Mujallar Forbes ta fitar da jerin kuɗin ƙasashe 10 mafiya daraja a duniya, inda aka yi amfani da wani ma'auni bisa ga bayanai da aka tattara a kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗen duniya.

Ga jerin kuɗin ƙasashe 10 mafiya daraja a duniya a kasa:

1. Dinarin Kuwait (KWD)

Dinarin Kuwait ne kuɗi mafi daraja a faɗin duniya, inda dinari ɗaya yake daidai da dalar Amurka 3.25 a halin yanzu.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke fitacciyar jarumar Kannywood, Samha Inuwa, ta aikata babban zunubi

Wannan kuɗi ya samu daraja ne sakamakon tsarin tattalin arzikin ƙasar wanda ya ginu a kan babban rumbun danyen mai.

Ƙasar Kuwait tana fitar da kaso mai yawa na man fetur zuwa duniya, wanda hakan ke sa kullum kuɗaɗe n ƙasashen waje suna shiga ƙasar.

Yawaitar shigar kudaden wasu kasashe ya sa dalar Amurka ɗaya take daidai da kobo 30 na dinarin Kuwait, lamarin da ya sa ya zama zakara.

2. Dinarin Bahrain (BHD)

Dinarin Bahrain yana matsayi na biyu, inda dinari ɗaya na ƙasar yake daidai da dalar Amurka 2.65 a kasuwar canji ta duniya. An fara amfani da wannan kuɗi ne a shekarar 1965.

Bahrain tana samun ƙarfin tattalin arziki ne daga ɓangarori daban-daban, inda kashi 85 na kuɗaɗenta ba sa fitowa daga man fetur kai-tsaye. Har ila yau, ƙasar ta kasance cibiyar harkokin banki da kasuwanci a yankin Gabas ta Tsakiya.

3. Riyal ɗin Oman (OMR)

An fara amfani da wannan kuɗi ne a shekarar 1970, kuma a yau riyal ɗaya yana daidai da dalar Amurka 2.60. Oman tana tsakanin ƙasar Yemen da Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma tana da tsayayyen tsarin gudanarwa.

Kara karanta wannan

A karon farko bayan Abba ya koma APC, kotu ta yi zama kan shari'ar Ganduje a Kano

Kamar sauran maƙwabtanta, Oman tana dogara ne da arzikin man fetur da iskar gas domin tabbatar da darajar kuɗin ƙasar. Haka kuma, gwamnatin ƙasar tana gudanar da tsauraran matakai domin hana darajar kuɗin yin ƙasa.

4. Dinarin Jordan (JOD)

Dinarin Jordan ya kasance kudi na hudu mafi karfi a duniya.
Takardar dinari 10 na kasar Jordan. Hoto: Ullstein bild / Contributor
Source: Getty Images

Dinarin Jordan ya kai darajar dala 1.41, wanda hakan ya sanya shi zama kuɗi na huɗu mafi ƙarfi a duniya baki ɗaya. An fara amfani da dinarin ne a shekarar 1950, kuma ya dade yana fafatawa da manyan kudaden kasashen Turai.

Duk da cewa Jordan ba ta da man fetur kamar sauran Larabawa, tsayayyen tsarin tattalin arzikinta ya kare darajar kuɗin ƙasar.

Gwamnatin Jordan ta dogara ne da tallafin ƙasashen waje da kuma kudaden da ƴan ƙasar dake waje suke aiko gida, a cewar rahoton BBC Hausa.

5. Fam na Ingila (GBP)

Fam ɗin ƙasar Birtaniya ya wanzu tun ƙarni na 15, kuma a yau ana canja fam ɗaya a kan dalar Amurka 1.34 a kasuwar canji. Wannan kuɗi ya fuskanci canje-canje da dama, musamman bayan ficewar Birtaniya daga ƙungiyar Turai (Brexit).

Wannan shi ne kuɗi mafi tsufa da ake ci gaba da amfani da shi a matsayin jigon kasuwancin ƙasashen Turai da duniya baki daya.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban ƙasa ta kashe N34bn a kan canjin kuɗi don tafiye tafiyen Tinubu

Har yanzu, Fam na Ingila yana da babban tasiri a kasuwannin hannun jari dake birnin London da sauran manyan biranen duniya.

6. Fam ɗin Gibraltar (GIP)

Darajar fam ɗin Gibraltar tana tafiya ne kafada da ƙafada da ta fam ɗin Ingila, inda duka suke da darajar dalar Amurka 1.34. Wannan yana nufin duk lokacin da kudin Ingila ya tashi, kudin Gibraltar ma tashi yake yi.

Yankin Gibraltar yana ƙarƙashin ikon Birtaniya ne duk da cewa yana kudancin kasar Sifaniya, wanda hakan ya sa kuɗin su yake da ƙarfi. Tattalin arzikin yankin ya dogara ne da yawon buɗe ido da kuma harkokin kasuwancin teku.

7. Franc na Switzerland (CHF)

Franc ɗin Switzerland yana da darajar dala 1.24, kuma ana ɗaukar sa a matsayin kuɗi mafi aminci ga masu zuba jari a duniya. An dade ana amfani da shi a matsayin "mafaka" lokacin da ake samun tashin hankali ko yakin duniya.

Zaman lafiyar siyasar Switzerland da ƙarfin bankunan su ne suka sa kuɗin ya zama garkuwa ga masu son adana dukiya. Tsarin bankunan ƙasar ya shahara wajen sirri da kuma riƙon amana ga abokan hulda.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

8. Dalar Tsibirin Cayman (KYD)

Tsibirin Cayman dake yankin Caribbean yana da kuɗi mai daraja, inda dalar ƙasar ɗaya take daidai da dalar Amurka 1.24. Wannan yanki yana karkashin ikon kasar Birtaniya ne kuma ya shahara sosai a fannin harkar kudi.

An san yankin wajen samar da sauƙin haraji, wanda hakan yake jawo hankalin manyan masu kuɗi na duniya su adana dukiya a wurin. Wannan tarin dukiya dake kwarara zuwa tsibirin shi ne babban ginshikin darajar kudin kasar.

9. Kuɗin Yuro (EUR)

Euro ne kudi na biyu da aka fi amfani da shi a duniya bayan dalar Amurka.
Takardun kudin Yuro da ake cinikayya da su a kasashe 20 na kungiyar Turai. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Kuɗin Yuro ne jigon cinikayya a ƙasashe 20 na ƙungiyar Turai, inda yuro ɗaya yake daidai da dalar Amurka 1.16 a yau. An fara amfani da wannan kudi ne a hukumance a shekarar 2002 domin hade tattalin arzikin nahiyar Turai.

A halin yanzu, shi ne kuɗi na biyu da aka fi amfani da shi a duniya bayan dalar Amurka, kuma yana da matukar tasiri. Karfin kudin Yuro yana dogara ne da tattalin arzikin manyan kasashe irinsu Jamus da Faransa.

Kara karanta wannan

Bayan zama sojan Rasha, 'dan Kano ya rasu yana gwabza yaki da Ukraine

10. Dalar Amurka (USD)

Dalar Amurka ce ta rufe jerin kudaden goma, kuma ita ce jigon da ake amfani da ita wajen cinikin zinare da man fetur a duniya. An fara amfani da dalar ne a shekarun 1700, kuma yanzu ita ce kudin da duniya ta fi amincewa da ita.

Tattalin arzikin Amurka shi ne mafi girma a duniya, wanda hakan ya sa dalar ta zama kuɗin da kowace ƙasa ke buƙata. Kusan kashi 80 na kasuwancin duniya ana yin sa ne da dalar Amurka.

Darajar Naira ta karu a kan Dala

A wani labari, mun ruwaito cewa, a ranar 28, Oktoba, 2025, Naira ta dan kara daraja a kasuwar musayar kudi ta NFEM yayin da kasuwar bayan fage ta ci gaba da zama daram.

Farashin Dala a NFEM ya tsaya a kusan N1,457.06 kan kowace $1, yayin da na kasuwar bayan fage ke tsakanin N1,450 zuwa N1,480.

Masana sun ce daidaiton na nuna tasirin matakan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dauka wajen rage bambanci tsakanin kasuwannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com