Uwa ba Wasa ba: Yaro Ya Yi Iyo na Awa 4, Ya Ceto Mahaifiyarsa, Kannensa a Teku
- Wani yaro dan shekara 13 ya yi iyo na tsawon awa hudu a tekun Australia domin ceton mahaifiyarsa da kannensa biyu
- Hakan ya biyo bayan iska ta kwashe su zuwa teku inda yaron ya yi nisan kusan kilomita 4 yana fama da guguwar ruwa
- Jirgin sama mai saukar ungulu da jiragen ruwa sun samu nasarar ceto mahaifiyar da kannensa biyun, inda jami’ai suka yaba masa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Quindalup, Australia - Wani matashi dan shekara 13 ya ceto mahaifiyarsa da kannensa biyu bayan ya yi iyo na tsawon awa hudu a kasar Australia.
Iyalan sun je hutu ne a Quindalup, kimanin kilomita 200 kudu da birnin Perth, lokacin da iska mai karfi ta tura kwale-kwalen wasan ruwa da suke kai tsaye zuwa cikin tekun 'Geographe Bay'.

Source: Facebook
Yadda yaro ya ceto mahaifiyarsa, kannensa a teku
Yaron, mai suna Austin Appelbee, ya yi kokarin komawa gabar teku domin neman taimako, amma ruwan ya fara shiga jirgin, cewar The Guardian.
Lamarin ya tilasta wa yaron barin bakin teku ya fara iyo zuwa gabar kogin, nisan kusan kilomita hudu.
Da yake magana da gidan talabijin na ABC, Austin ya ce ya sha fama da igiyar ruwa mai karfi yayin da yake iyo sanye da rigar kariya ta rayuwa.
Bayan awa biyu, ya cire rigar domin samun saukin iyo, ya ce ya tsorata matuka lokacin da ya ga wani abu a cikin ruwa.
Austin ya kara da cewa yana tunanin abubuwan da suka fi faranta masa rai a rayuwa domin kar ya yanke kauna, duk da cewa jikinsa ya gaji sosai.

Source: Getty Images
Famar da karamin yaron ya sha a teku
Bayan ya isa gabar teku, yaron ya fadi kasa saboda gajiya, daga nan kuma ya sake gudu nisan kusan kilomita biyu domin ya samu waya ya kira lambar gaggawa ta.

Kara karanta wannan
Gwamna ya sare gwiwoyin 'yan adawa, ya haska dalilan da za su sa APC lashe zabe a 2027
Ya ce ya nemi a turo jiragen sama masu saukar ungulu, jiragen ruwa da jiragen sama, yana sanar da jami’ai cewa iyalansa suna cikin teku.
‘Yan sandan yanki a Australia sun ce sun samu rahoto da misalin karfe 6:00 na yamma, inda suka hada gwiwa da jami’an ruwa, masu aikin ceto da jirgin sama mai saukar ungulu.
Da misalin karfe 8:30 na dare, jirgin sama ya gano mahaifiyar mai shekara 47 da yaro dan shekara 12 da yarinya ‘yar shekara 8 suna manne da kwale-kwalen ruwa, kimanin kilomita 14 daga gabar teku.
Jirgin ceto ya isa wurin, inda aka samu nasarar ceto dukkaninsu lafiya, an kai su asibitin Busselton domin duba lafiyarsu.
Shugaban kungiyar ceto ta sa-kai, Paul Bresland, ya ce bayanin da yaron ya bayar kan launi da nau’in kayayyakin ruwan ya taimaka matuka wajen samun nasarar aikin ceto.
Jami’an lafiya sun bayyana lamarin a matsayin abin ban mamaki, yayin da ‘yan sanda suka yaba da jarumta da jajircewar yaron, suna cewa kokarinsa ne ya ceci rayukan mahaifiyarsa da kannensa.
Mutane 19 sun mutu a teku

Kara karanta wannan
'Yan Najeriya na cikin alheri, sun fara cewa arahar abinci ta yi yawa a mulkin Tinubu'
A baya, an ji cewa rahotanni daga jihar Bayelsa sun nuna cewa an yi nasarar tsamo gawarwakin fasinjoji 19 daga teku bayan haɗarin jirgin ruwa.
Wani jirgin ruwa da ya ɗauko ƴan kasuwa galibi mata da kayansu ya kama da wuta a hanyar zuwa Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa.
Yanzu haka dai an kai gawarwakin waɗanda suka mutu ɗakin ajiyar gawa da ke babban asibitin tarayya FMC a babban birnin jihar Bayelsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
