Bayan Amurka da Turai, Kasar Australia ma ta maida ofisoshin jakadancinta na Israila Birnin Qudus

Bayan Amurka da Turai, Kasar Australia ma ta maida ofisoshin jakadancinta na Israila Birnin Qudus

- Kasar Australia ta maido ofishin jakadancinta Jerusalem a wani yanki na babban birnin Israel

- Kowanne tsakanin Israel da Palestine ayyana Jerusalem a matsayin babban birnin su

- Da yawa daga cikin kasashen waje sunki maida ofishin jakadancin su zuwa wajen

Bayan Amurka da Turai, Kasar Australia ma ta maida ofisoshin jakadancinta na Israila Birnin Qudus

Bayan Amurka da Turai, Kasar Australia ma ta maida ofisoshin jakadancinta na Israila Birnin Qudus
Source: UGC

Australia ta zamo kasa ta baya-bayan nan da ta maido da ofishin jakadancinta babban birnin Israila, daga Tel-Aviv, zuwa Jerusalem, birni da kowacce kasa a tsakanin Israel da Palestine suka ayyana a matsayin cewa babban birnin su ne.

Da yawa daga cikin kasashen ketare sunki maida ofishin jakadancin su zuwa wajen dan gudun cece-kuce sai a wannan shekarar ne Trump ya maida ofishin jakadancin US zuwa wajen.

DUBA WANNAN: Yawan mata daga Arewa wadanda bassu zuwa makaranta a sabon bincike

"Mun shirya maida ofishin jakadancin mu zuwa Jerusalem bayan gudanar da wasu gwaje-gwaje da shirye-shirye" cewar Marrison.

Sannan ya kara da cewa nan bada dadewa ba za'a fara gudanar da aikin kma wa Jerusalem din, watau birnin Qudus..

Prime Ministan Australia yace, kasarsa zata samar da wani ofishin tsara huldar kasuwanci kuma a cikin birnin.

Sannan ya kara da cewa bisa yarjejeniyar da kasashen biyu sukayi dan samar da mafita gwamnatin Australia zata bawa Palestine damar yin bukatun su a wani bangare na Jerusalem.

A da dai, an ayyana cewa yaki ne kadai zai wakana, watakil na duniya, muddin duniya ta mika wa Yahudun Israila babban birnin, wadda musulmi ke ganin nasu ne.

Shekaru kusan dubu kenan ana yaki a kan birnin, tun zamanin Crusades, amma yanzu kam, lamarin ya sha kan larabawa, sun hakura sun barwa duniya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel