Jirgin Sama Dauke da Dan Majalisa da Wasu Mutum 14 Ya Bace bayan Tashinsa

Jirgin Sama Dauke da Dan Majalisa da Wasu Mutum 14 Ya Bace bayan Tashinsa

  • An tabbatar da bacewar wani jirgin sama na kamfanin Satena a kusa da iyakar kasar Colombia da Venezuela ranar Laraba
  • Rahotanni sun nuna cewa an rasa sadarwa da jirgin mintuna kadan kafin ya sauka a garin Ocana bayan ya tashi daga birnin Cucuta
  • Hukumomi sun ce jirgin na dauke da fasinjoji 13 da ma'aikata biyu, cikinsu har da dan Majalisar Colombia da dan takarar kujerar Majalisa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Colombia - Wani jirgin sama mai dauke da mutane 15, ciki har da wani dan majalisa, ya bace a kusa da iyakar kasar Colombia da Venezuela mai fama da tashe-tashen hankula a ranar Laraba.

Kamfanin jiragen sama na kasar, Satena, da hukumomin kula da sararin samaniya ne suka tabbatar da faruwar lamarin.

Jirgin kamfanin Satena
Jirgin kamfanin Satena bayan sauka filin jirgin sama a kaaar Colombia Hoto: Getty images
Source: Getty Images

Jirgin kamfanin Satena ya bace a sama

Kara karanta wannan

Ana batun komawar Abba APC, an kama wanda zai bada shaida mai karfi a shari'ar Ganduje

Rahoton jaridar India Today ya ce Jirgin, wanda ke dauke da fasinjoji 13 da ma'aikata biyu, ya tashi ne daga birnin Cucuta da ke kan iyakar kasashen biyu.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa jirgin ya daina tuntubar ofishin sadarwa jim kadan kafin lokacin da ya kamata ya sauka a garin Ocana da ke makwabtaka da shi.

Yankin da jirgin sama ya bace

Wannan yanki na Ocana, cike yake da duwatsu kuma babbar kungiyar 'yan tawayen Colombia, wato National Liberation Army (ELN), ce ke iko da sassa da dama na yankin.

"An tsara jirgin zai sauka da misalin karfe 12:05 na rana amma aka neme shi aka rasa," in ji kamfanin Satena a cikin wata sanarwa.

Hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen saman Colombia sun bayyana cewa an riga an kaddamar da bincike tare da daukar matakai domin gano inda jirgin ya makale.

Dan Majalisa na cikin jirgin Satena

Ana fargabar cewa akwai wani dan majalisa da kuma wani dan takarar majalisar a cikin jirgin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Dan majalisa a Colombia, Wilmer Carrillo ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

"Mun samu labarin wannan lamari da ya faru da jirgin saman, hakan ba karamin abun damuwa ba ne. Abokin aiki na Diogenes Quintero, Carlos Salcedo da tawagarsu suna cikin jirgin."

Quintero mamba ne a majalisar wakilai ta kasar Colombia, yayin da Salcedo ke takara a zabe mai zuwa.

Jirgin sama.
Jirgin sama a lokacin da yake tsakiyar tafiya a sararin samaniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Dan Majalisa Carrillo ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu tare da jiran bayani a hukumance daga hukumomin da suka dace.

Wannan bacewar jirgin sama a yankin da 'yan tawaye ke iko da shi ya kara jefa damuwa kan ko hadari ne ko kuma wani abu ne daban.

Jirgin sama ya yi hatsari a Yammacin India

A wani rahoton, kun ji cewa wani jirgin sama dauke da babban jami’in gwamnati ya yi hatsari a yammacin kasar India ranar Laraba.

Rahoto ya nuna cewa kataimakin babban minista, Ajit Pawar ya rasu tare da mutane hudu a wannan mummunan hadarin jirgin sama da ya auku.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta tabbatar da rasuwar Ajit Pawar, mai shekaru 66, wanda shi ne mataimakin babban ministan jihar Maharashtra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262