2026: An Yi Hasashen Ranar da Za a Fara Azumi, Tsawon Wata da Ranar Karamar Sallah

2026: An Yi Hasashen Ranar da Za a Fara Azumi, Tsawon Wata da Ranar Karamar Sallah

  • Ana sa ran al'ummar Musulmi za su fara azumin Ramadan na shekarar 2026 ne a ranar 19 ga watan Fabrairu cikin sanyin yanayi
  • Sa'o'in da Musulmi za su dauki azumi zuwa shan ruwa za su kasance matsakaita tsakanin awa 12 zuwa 13 a mafi yawan kasashen duniya
  • Yanayin kaka da sanyi zai taimaka wa Musulmi gudanar da ibada cikin sauki ba tare da fuskantar tsananin kishirwa ko wahalar zafi ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daukacin al'ummar Musulmi a fadin duniya sun fara shirin tunkarar watan Ramadan 2026, inda a wannan karon ake sa ran samun saukin yanayi bayan shafe shekaru ana azumi a lokacin zafi da kuma tsawon rana.

Binciken masana ilimin taurari ya nuna cewa watan na Ramadan zai zo ne a daidai lokacin sanyi da kuma farkon bazara, wanda hakan zai sanya sa'o'in azumi su zama matsakaita a mafi yawan kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Awanni da shigar Abba APC, kotu ta garkame wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Kano

Ana sa ran za a fara azumin watan Ramadan na 2026 a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu.
Watan azumin Ramadan ya fito a sararin samaniya, yayin da ake ganin husumiyar masallacin Malegaon, Maharashtra, a India. Hoto: Dinodia Photo
Source: Getty Images

Hasashen ranar fara azumi na 2026

A bisa lissafin taurari, ana sa ran za a fara azumin watan Ramadanne a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026, kamar yadda rahoton Times of India ta ruwaito.

Idan aka yi azumin kwanaki 30 cif cif, ana sa ran ranar sallah (Eid Al Fitr) za ta fada ne a Juma'a, 20 ga Maris, 2026, sai dai hakan ya dogara da ganin wata.

Saboda lokacin sanyi ne, Musulmi za su gudanar da ibada cikin yanayi mai dadi, ba tare da fuskantar tsananin kishirwa ko wahalar rana kamar yadda aka saba gani a shekarun baya ba.

Sa'o'in azumi a kasashen Larabawa

A mafi yawan kasashen Larabawa da yankin Gabas ta Tsakiya, tsawon lokacin azumi zai kasance tsakanin sa'o'i 12 zuwa 13.

Wannan shi ne daya daga cikin mafi gajeren lokacin azumi da aka taba samu a cikin shekaru 10 na baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Ilhan Omar: Bidiyon yadda aka farmaki 'yar majalisar Amurka a taron jama'a

A kasashen Masar, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Musulmi za su fara azumi ne na sa'o'i 12 da mintuna 40. Lokacin zai rika karuwa kadan-kadan har zuwa kusan sa'o'i 13 a karshen watan yayin da rana take kara tsawo.

Me yasa tsawon lokacin azumi yake bambanta?

Dalilin da ya sa tsawon lokacin azumi yake bambanta shi ne yanayin tazarar kasa daga ma'aunin Equator. Kasashen da ke kusa da wannan ma'aunin suna samun sa'o'in rana kusan daya a duk tsawon shekara, yayin da kasashen da ke nesa (Arewa ko Kudu) ke samun babban bambanci.

A kasashen Turai kamar Birtaniya, Jamus, da kasashen yankin Scandinavia, sa'o'in azumi za su fi tsayi idan aka kwatanta da na Afirka da Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran Musulmi za su yi azumi cikin sanyin yanayi a bana
Al'ummar Musulmi a cikin masallaci yayin gudanar da ibada. Hoto: Raymond Sheffield via Getty Images
Source: Getty Images

Matakin Musulmi a kasashen Rasha, Greenland

A yankuna masu nisa sosai na Arewa kamar Rasha, Greenland, da Iceland, inda sa'o'in rana kan wuce sa'o'i 16, Musulmi sukan bi fatawowin malamai wajen amfani da lokacin birni mafi kusa da su ko kuma bin lokacin birnin Makkah domin samun sauki.

Baki daya, azumin 2026 zai kasance mai cike da albarka da sauki ga daukacin al'umma, sakamakon haduwar gajeren lokaci da kuma sanyin yanayi, wanda hakan zai bai wa mutane damar mayar da hankali ga ayyukan ibada.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun take yarjejeniyar sulhu, sun afkawa Katsinawa

Izala ta fitar da malaman tafsir

A wani labari, mun ruwaito cewa, kungiyar Izala karkashin Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ta tura malamai tafsirin Al-Kur’ani jihohi da kasashe a Ramadan 1447/2026.

Sanarwar ta fito ne daga hedkwatar kungiyar, inda ta ce shirin yana daga cikin manyan ayyukan da JIBWIS ke gudanarwa a duk shekara domin ilmantarwa, tarbiyya da kuma yada Musulunci.

A cewar sanarwar, shugabancin JIBWIS ya kammala dukkan tsare-tsare tun kafin shigowar watan Ramadan, domin bai wa malamai damar isa wuraren da aka tura su tafsir cikin lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com