Rasha Ta Shiga Rikicin Amurka da Iran, Trump na barazanar kai Hari Tehran

Rasha Ta Shiga Rikicin Amurka da Iran, Trump na barazanar kai Hari Tehran

  • Gwamnatin Rasha ta bayyana barazanar kai hare-haren soji da Amurka ke yi kan Iran a matsayin abu mai hatsari da ba za a amince da shi ba
  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya ci gaba da yin kira ga masu zanga-zanga a Iran da su ci gaba da matsin lamba, yana cewa taimako na tafe
  • A yayin da ake ta kai-komo, Amurka da wasu ƙasashen Yamma sun fara janye wasu ma’aikatansu daga sansanonin soji a Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Russia - Gwamnatin Rasha ta yi kakkausar suka ga abin da ta kira tsoma baki don lalata a harkokin cikin gidan Iran, tana mai gargaɗin cewa hari daga Amurka zuwa Iran zai iya jefa yankin Gabas ta Tsakiya da tsaron duniya cikin mummunan hali.

Kara karanta wannan

Mutanen kauyuka za su kaura domin luguden wuta kan 'yan bindiga a dazuka

Wannan martani na Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ke ta yin kalamai masu zafi game da yiwuwar tsoma baki domin goyon bayan masu adawa da gwamnati a Iran.

Jagororin Iran, Amurka da Rasha
Ali Khamenei, Donald Trump da Vladimr Putin. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Reuters ya nuna cewa rikicin cikin gida da Iran ke fuskanta ne ya janyo hankalin manyan ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kasa da kasa.

Gargadin Rasha ga Amurka kan Iran

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta fitar da sanarwa inda ta bayyana cewa duk wani yunƙurin amfani da tashin hankalin cikin gida a Iran a matsayin hujjar kai sabon hari abu ne da ba za a amince da shi ba.

Kasar ta ce irin wannan mataki zai haifar da mummunan sakamako ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kuma tsaron kasa da kasa.

A cewar Rasha, duk wanda ke shirin maimaita abin da ta kira farmaki da aka yi wa Iran a watan Yuni, 2025, dole ne ya fahimci girman illar da hakan zai haifar.

Amurka na janye soji a Gabas ta Tsakiya

A gefe guda, rahotanni sun nuna cewa Amurka ta fara janye wasu daga cikin ma’aikatanta daga manyan sansanonin soji a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Trump na barazana ga Iran, zanga zanga ta barke a Amurka, ana ta arangama

Wannan mataki ya biyo bayan gargadin da jami’an Iran suka yi cewa za su kai hari kan sansanonin Amurka idan aka kai musu hari.

BBC ta rahoto cewa wasu jami’an soji na kasashen Yamma sun bayyana cewa duk da alamu na shirin kai hari, salon tafiyar gwamnatin Trump na cike da rashin tabbas.

Wasu sojojin Amurka a Qatar
Dakarun Amurka da ke sansani a kasar Qatar. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai Fadar White House ta ce Trump yana sa ido kan lamarin, yana duba yadda abubuwa za su kaya kafin daukar mataki na gaba.

Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin zama kan batun Iran, biyo bayan bukatar Amurka, domin tattauna halin da ake ciki.

Ana zanga-zanga a Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa matasa na cigaba da gudanar da zanga-zanga a biranen Amurka bayan kashe wata mata da aka yi.

Masu zanga-zanga suna yawo a kan tituna suna Allah wadai da kashe matar tare da kira a dakatar da jami'an shige da fice na Amurka.

A wurare da dama, matasa sun yi arangama da jami'an Amurka, inda aka rika fesa musu borkonon tsohuwa da abubuwa masu saka kaikayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng