An Yanke wa Wani 'Dan Najeriya Hukuncin Kisa a Kasar Waje, Za a Rataye Shi
- Wata kotu a kasar Malaysia ta yanke wa dan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda wurgo jikansa kasa daga bene har ya mutu
- An kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar bayan an same shi da laifin yunkurin kashe dansa da kuma cin zarafin yar matarsa
- Alkalin kotun ya jaddada cewa ba za a amince da uzurin cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifuffukan ne a halin yana maye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Malaysia - Babbar Kotun Kuala Lumpur da ke ƙasar Malaysia, ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Ibekwe Emeka Augustine, ɗan shekara 48, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Alƙali K Muniandy ya yanke wannan hukunci ne bayan samun Augustine da laifin kisan jikan matarsa mai shekaru huɗu, ta hanyar wurgo shi kasa daga hawa na uku na wani gida shekaru shida da suka gabata.

Source: Twitter
Za a rataye 'dan Najeriya a kasar Malaysia
An zargi Augustine da aikata wannan danyen aikin a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2020, tsakanin ƙarfe 7:45 zuwa 8:15 na safe a yankin Setapak, in ji rahoton The Sun Malaysia.
A yayin gudanar da shari’ar, kotun ta saurari yadda Augustine ya aikata jerin manyan laifuffuka a rana ɗaya waɗanda suka bar iyalinsa cikin tsananin firgici.
Baya ga hukuncin kisa da aka yanke masa a ƙarƙashin Sashi na 302 na Dokar Hukunta Manyan Laifuffuka, kotun ta kuma yanke masa ɗaurin shekaru biyar a gidan yari.
Waɗannan ƙarin hukuncin sun biyo bayan samunsa da laifin yunƙurin kashe ɗansa na jininsa mai shekaru bakwai, yi wa matarsa rauni mai tsanani, yunƙurin kashe kansa, da kuma cin zarafin ’yar matarsa mai shekaru 25 ta hanyar lalata.
Kotu ta ki karbar uzirin 'dan Najeriyan
Alƙali Muniandy, a yayin fadin hukuncin, ya jaddada cewa kotu ba za ta yarda da uzurin cewa Augustine yana ƙarƙashin tasirin ƙwayoyi a lokacin da ya aikata laifuffukan ba.
A cewar alƙalin, Augustine ya ci gaba da kai wa iyalinsa hari ko da bayan matarsa ta yi ƙoƙarin tsawatar masa tare da shiga tsakani, inda ya ji mata raunuka masu tsanani kafin ya ɗauki jikan ya jefa shi ta taga daga bene mai hawa na uku.
Shaidu sun nuna cewa waɗanda abin ya shafa sun gudu daga gidan don tsira da rayukansu, sai daga baya suka tarar da gawar yaron a ƙasa.

Source: Twitter
Mutumin Najeriyan zai daukaka kara a Malaysia
Lauyan da ke kare Augustine, Zulkifly Awang, ya bayyana cewa za su ɗaukaka ƙara kan wannan hukuncin kisa da aka yanke wa wanda yake kariya, in ji rahoton Punch.
Sai dai, babban mai gabatar da ƙara, Zaileen Nadia Zubir, ta gabatar da gamsassun shaidu waɗanda suka tabbatar da cewa Augustine ya aikata waɗannan laifuka da gangan.
Wannan shari’a ta ja hankalin jama’a sosai a Malaysia, musamman duba da yadda aka ɗauki tsawon shekaru ana fafatawa kafin a kai ga yanke hukuncin ƙarshe a yau.
An yanke wa 'dan sanda hukuncin kisa
A wani labari, mun ruwaito cewa, Babbar kotun Filato ta yanke wa Sajen Ruya Auta hukuncin kisa ta hanyar rataya ko allura bayan an kama shi da laifin kashe ɗalibin jami'a.
Shaidu da bayanan shari’a sun tabbatar cewa Sajen Ruya Auta ya harbi dalibi a jami'ar UNIJOS, Rinji Bala a Kwankwaso, lokacin kullen COVID-19, wanda ya yi ajalinsa.
Iyalan marigayin da lauyoyin da suka tsaya masu sun bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga adalci, tare da fatan zai zama izina ga sauran jami’an tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


