Trump Ya Yi Magana kan Musulmin Najeriya yayin Barazanar Kawo Hare Hare
- Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na iya sake kai hare-haren soji a Najeriya idan aka ci gaba da kashe Kiristoci a ƙasar
- Ya yi ikirarin cewa hare-haren baya-bayan nan da sojojin Amurka suka kai a Najeriya ba na ƙarshe ba ne, yana mai cewa lamarin na iya maimaituwa
- Yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai kan kawo harin, Donald Trump ya yi magana game da Musulman Najeriya kai tsaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cewa ƙasarsa na iya sake kai hare-hare Najeriya, idan aka ci gaba da kashe Kiristoci.
Hakan na zuwa ne duk da matsayar da gwamnatin Najeriya ta dauka na cewa babu tsangwama na addini da ake yi wa wata ƙungiya da addini a kasar.

Source: Getty Images
Rahoton Retuers ya nuna ceewa Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi, inda ya danganta yiwuwar kai ƙarin hare-hare da yadda yake kallon halin tsaro da kuma kashe-kashen da ke faruwa a Najeriya.
Wannan kalamai na zuwa ne bayan wani harin soji da Amurka ta kai a ranar Kirsimeti, wanda aka ce an kai shi ne kan mayaƙan kungiyar ISIS a Arewa maso Yammacin Najeriya bisa bukatar gwamnatin ƙasar.
Donald Trump zai kai hare-hare Najeriya
Trump ya ce da farko yana fatan harin Kirsimeti ya zama na lokaci guda, amma ya nuna cewa hakan ba lallai ba ne idan kashe-kashen Kiristoci suka ci gaba.
Rahoton da BBC Hausa ta wallafa ya nuna cewa Donald Trump ya ce idan lamarin ya ci gaba, to Amurka za ta iya sake kai hare-hare sau da dama a Najeriya.
Maganar Trump kan Musulmin Najeriya
'Yan jarida sun tambayi Trump kan matsayarsa game da abin da hadiminsa ya taba fada a baya cewa an fi kashe Musulmi a Najeriya.
A amsar da ya bayar, ya bayyana cewa ya amince cewa a Najeriya Musulmi ma na fuskantar hare-hare, amma ya dage cewa mafi yawancin waɗanda ake kashewa Kiristoci ne.
Ya ce:
"Ina ganin cewa ana kashe Musulmi a hare-haren da ake kai wa a Najeriya, amma an fi kashe Kiristoci."
Wannan furucin ya kara tayar da muhawara, musamman ganin cewa rahotanni daga hukumomi da masu bincike sun nuna cewa rikicin tsaro a Najeriya na shafar mutane daga addinai daban-daban.
Tun a Disamban 2025 binciken Sky Sports ya nuna babu kanshin gaskiya a irin wadannan maganganu da Trump yake yi na cewa Kiristoci aka fi kashewa.

Source: Facebook
Hukumomin Najeriya sun sha musanta zargin cewa ana tsananta wa Kiristoci kai-tsaye, suna mai cewa matsalolin tsaro sun hada da ayyukan ’yan ta’adda, sace-sace da rikice-rikicen da ke shafar Musulmi da Kiristoci baki daya.
An kai hari kan Kiristoci a Amurka
A wani labarin, kun ji cewa wani dan bindiga ya kai hari wajen wani coci a kasar Amurka, inda aka tabbatar ya kashe mutane nan take.
Rahoton da rundunar 'yan sandan yankin ta fitar ya nuna cewa dan bindigan ya jikkata wasu mutane da yanzu haka suke asibiti.
Jami'an tsaro sun bayyana cewa ana cigaba da bincike domin gano wanda ya kai harin, domin a cewarsu, ya cika rigarsa da iska.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


