Trump na Barazana ga Najeriya, 'Dan Bindiga Ya Kashe Kiristoci a Cocin Amurka

Trump na Barazana ga Najeriya, 'Dan Bindiga Ya Kashe Kiristoci a Cocin Amurka

  • Wani 'an bindiga ya hallaka mutane tare da jikkata wasu da dama a wajen cocin Mormon a birnin Salt Lake City na jihar Utah a Amurka
  • Lamarin ya faru ne yayin da ake gudanar da jana’iza, inda ‘yan sanda suka ce ba a kama ko da mutum daya da ake zargi da aikata laifin ba
  • Yayin da ake cigaba da bincike, hukumomi sun ce ba su ganin harin ya zo ba tsammani kuma ba a alakanta shi kai tsaye da addini ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu bayan wani mummunan harbin bindiga da ya auku a filin ajiye motoci na cocin Mormon a birnin Salt Lake City.

Harbin ya faru ne a ranar Laraba, 7 ga Janairun 2026 a daidai lokacin da daruruwan mutane ke halartar jana’izar wani mamaci a cocin Jesus Christ of Latter-day Saints.

Kara karanta wannan

Dasa bam a masallaci: An kuma cafke mutane 8, an samu muhimman bayanai

'Yan sanda a wajen da aka kai hari a Amurka
Jami'an 'yan sanda sun isa wajen da aka kai hari Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Al-Jazeera ta ce lamarin ya jefa yankin cikin firgici, inda jami’an tsaro suka rufe wurin tare da fara farautar wanda ake zargi da aikata harin.

An kai hari a wajen cocin Amurka

‘Yan sanda sun bayyana cewa harbin ya faru ne a filin ajiye motoci na cocin, inda mutane da dama suka hallara domin jana’iza.

Rahoton da CCN ta fitar ya nuna cewa mutum biyu sun rasu kuma akalla mutane shida ne suka jikkata, kuma uku daga cikinsu na cikin mawuyacin hali a asibiti.

Jami’an tsaro sun ce bayan harbin, wanda ake zargi ya tsere daga wurin, lamarin da ya sa aka kaddamar da gagarumin samame domin cafke shi.

Martanin jami’an tsaron kasar Amurka

Shugaban ‘yan sandan Salt Lake City, Brian Redd babu wata alama da ke nuna cewa an kai harin ne saboda kiyayyar addini.

Ya ce duk da cewa lamarin ya faru a wajen coci, ba a ga wata shaida da ke nuna an kai hari kai tsaye kan masu ibada a Mormon ba.

Kara karanta wannan

An hango jirgin yakin Amurka ya sauka a Najeriya da dare

Rahotanni sun nuna cewa rundunar FBI ta Amurka ta nuna aniyar ba da hadin kai wajen bincike da kuma farautar wanda ake nema.

Abin da cocin Amurka ya ce kan harin

Mai magana da yawun cocin, Glen Mills, ya bayyana cewa kafin harbin ya faru, an lura da wata takaddama a wajen cocin. A cewarsa, rigimar ta faru ne a filin ajiye motoci, inda daga bisani aka ji karar harbin bindiga.

Cocin ya bayyana cewa yana aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin gano musabbabin lamarin da tabbatar da tsaron mambobin sa.

Martanin shaidun gani da ido da gwamnati

Wani mazaunin yankin, Brennan McIntire, ya ce ya iske wani mutum kwance a kasa yayin da mutane ke kuka da kokarin taimaka masa.

Magajin garin Salt Lake City, Erin Mendenhall, ta bayyana bakin ciki kan lamarin, tana mai cewa bai dace ba a ga irin wannan tashin hankali a wajen ibada ko wajen tunawa da rayuwar mamaci.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump
Donald Trump yana bayani a ofis. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka za ta kwace tsibirin Greenland

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta nuna sha'awar karbe ikon tsibirin Greenland da ke karkashin ikon kasar Denmark.

Kara karanta wannan

Kano: Wasu yara sun fadi dalilin murna da rasuwar mahaifinsu bayan shekaru 20

Fadar White House ta sanar da cewa yankin yana da matukar muhimmanci ga Amurka kuma da wahala a kawar da kai a kansa.

Ta bayyana cewa shugaba Donald Trump zai yi dukkan mai yiwuwa wajen karbar Greenland, ciki har da amfani da karfin soja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng