Zohran Momdani da Wasu Musulmai 4 da ke rike da manyan mukamai a Amurka
United States - Musulmai na ci gaba da samun nasara a zabubbuka tare da karbar ragamar shugabanci a muhimman mukamai a kasar Amurka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wannan na zuwa ne bayan rantsar da sabon Magajin Garin birnin New York da ke kasar Amurka, Zohran Momdani, wanda ya kasance Musulmi kuma matashi.

Source: Getty Images
Musulmi ya zama Magajin Garin New York
Al-Jazeera ta ruwaito cewa Momdani ya karbi rantsuwar kama aiki da Alkur'ani mai girma a ranar Alhamis, 1 ga watan Janairun 2026, wanda hakan ya sa ya zama musulmi na farko da zai jagorancin New York.
Wasu masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na alaƙanta hakan da irin samun karɓuwa da yaduwar da Addinin Masulunci ke yi a ƙasashen Yammacin duniya.
Sai dai wasu masana kuma na ganin hakan ta faru ne saboda 'yancin addinin da kasashen suka ba kowane dan adam.
Musulman da ke rike da mukami a Amurka
Ba Zohran Momdani ba ne Musulmi na farko da ya samu babban mukami a kasar Amurka, akwai wasu da dama da suka samu damar da za su ba da gudummuwa a harkokin mulki.
A wannan rahoton, mun tattaro muku akalla musulmai biyar da ke rike da mukamai daban-daban a kasar Amurka, ga su kamar haka:
1. Zohran Momdani
A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, 2025 ne matashi dan shekara 34 a duniya ya samu nasara a zaben Magajin Garin New York, daya daga cikin birane mafi girma a duniya.
Momdani ya zama musulmi na farko a tarihi da ya taka wannan mataki, kuma matashi mai karancin shekarau da zai jagoranci New York a cikin shekaru 100.
Rahotanni sun nuna cewa an haife shi ne a birnin Kampala na kasar Uganda, amma iyayensa sun dauke shi sun koma zama a birnin New York tun yana 'dan shekara bakwai a duniya.

Source: Getty Images
Zohran Mondani ya yi karatu a wata makarantar fasaha da ke garin Bronx, bayan nan kuma ya yi digiri kan nazarin ƙasashen Afirka a makaratar Bowdoin.
Matashin dai ya zama Musulmi na farko kuma dan asalin Kudancin Asiya da ya zama Magajin Garin New York bayan rantsar da shi a makon jiya, cewar rahoton AP News.
2. Lateefah Simon
A watan Janairun shekarar 2025 ne Lateefah Aaliyah Simon ta zama wakiliya ta 12 da Jihar California ta tura zuwa Majalisar Wakilan Amurka.
Hakan ya sa Lateefah daga jam'iyyar Democrat ta kafa tarihin zama musulma mace ta farko da ta zama 'yar Majalisa daga jihar California da duka yankin Yammacin tsakiyar Amurka, cewar The Muslim News.
An haife ta a Yammacin birnin San Francisco kuma a wannan yanki ta taso, inda ta yi karatun sakandire a Makarantar Washington.
Lateefah Simon ta shahara wajen yin kakkausar suka kan hare-haren sojojin Isra’ila a Gaza, tare da yin tir da irin tallafin kuɗi da na soja da gwamnatin Amurka ke bai wa Isra’ila.
3. Ilhan Omar
Ilhan Omar na daya daga cikin Masulmai kuma mata da suka kafa tarihin lashe kujerar Majalisar Wakilai a kasar Amurka.
A watan Nuwamba na shekarar 2018, aka ayyana ta a matsayin mace ta farko kuma Musulma da ta ci zaben 'yar Majalisar a tarihin kasar Amurka karkashin inuwar jam'iyyar Democrat.
Ilhan, wacce ta kasance yar asalin kasar Somaliya, ta samu karbuwa a wurin matasa maza da mata, kuma ta shahara wajen adawa da galibin shugabannin Amurka musamman kan Falasdinawa.
Shugaban Amurka, Donald Trump na daya daga cikin manyan abokan hamayyarta na siyasa da suke musayar yawu, kuma Ilham ta sha fama da barazana kisa, kamar yadda BBC News ta kawo.

Source: Twitter
4. Rashida Tlaib
Rashida Tlaib ta samu nasarar zama 'yar majalisar wakilan Amurka lokaci guda da Ilhan Omar a watan Nuwamba, 2018.
Matan guda biyu kuma Musulmai sun yi fice wajen sukar kisan kiyashin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza, hakan ya sa aka hana su shiga kasar Yahudawan.
Sai dai ita Rashida Tlaib, wacce ta kasance yar asalin kasar Falasdinu ta ci zaben 'yan Majalisar wakilai ne daga jihar Machigan, kamar yadda CBS News ta kawo.
5. Keith Ellison
Asalin Keith Ellisonba ba musulmi ba ne amma ya karbi addinin musulunci a shekarar 1982 kafin ya tsunduma harkokin siyasa.
Ellison, wanda fitaccen lauya ne dan asalin kasar Amurka, shi ke rike da mukamin babban Antoni Janar na jihar Minnesota, cewar rahoton MPR News.
A watan Oktoba, 2025 Ellison ya sanar cewa zai sake tsayawa takarar Antoni Janar, yana mai cewa yana da sha'awar ci gaba da matsa lamba kan gwamnatin Trump da kuma kokarin rage tsadar rayuwa.
Ya rike mukamin ɗan majalisar wakilai daga jihar Minnesota daga shekarar 2007 zuwa 2019, inda ya zama musulmi na farko da ya rike wannan kujera.
Mamdani ya fara soke dokoki a New York
A wani rahoton, kun ji cewa sabon magajin birnin New York, Zohran Mamdani, ya soke wasu dokokin da tsohon Magajin gari Eric Adams ya sanya masu alaƙa da kasar Isra’ila.
Mamdani ya soke dukkan dokokin da Eric Adams ya kawo bayan 26, Satumba, 2024, ranar da aka gurfanar da Adams a gaban kotu.
Rahoto ya nuna cewa Mamdani ya kuma rattaba hannu kan sababbin dokokin a ranar Alhamis, jim kaɗan bayan bikin rantsar da shi a City Hall.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




