Shugaban Venezuela da Trump Ya Cafke Zai Gurfana a Kotun Amurka kan Zarge Zarge

Shugaban Venezuela da Trump Ya Cafke Zai Gurfana a Kotun Amurka kan Zarge Zarge

  • Wani Sanatan Amurka ya ce an kama Shugaban Venezuela Nicolás Maduro, kuma za a gurfanar da shi a kotun kasar
  • Sanata Mike Lee ya bayyana cewa sojojin Amurka sun yi amfani da ƙarfi ne domin kare jami’an da ke aiwatar da sammacin kama Maduro
  • Bayan sanarwar Donald Trump, Venezuela ta ayyana dokar ta-baci, yayin da mazauna Caracas suka ce sun ji fashe-fashe da gobara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Sanatan Jam’iyyar Republican daga Utah, Mike Lee, ya yi magana bayan kama Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro.

Sanatan ya ce Maduri zai fuskanci shari’a kan zargin aikata manyan laifuffuka a Amurka wanda zai fuskanci hukunci.

Za a gurfanar da shugaban Venezuela a kotun Amurka
Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro da Donald da Trump. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

A wani rubutu da ya wallafa a shafin X, Lee ya ce ya yi magana kai tsaye da Marco Rubio kafin ya fitar da sanarwar.

Kara karanta wannan

Trump ya jefa bama bamai a Venezuela, ya cafke shugaban kasa Maduro da matarsa

Ikirarin cafke Maduro da Trump ya yi

Wannan ya biyo bayan ikirarin Shugaba Donald Trump cewa sojojin Amurka sun kama Maduro da matarsa.

Trump ya ce an yi wannan ne bayan wani babban farmakin soji da Amurka ta kai wa Venezuela.

Bayan sanarwar, gwamnatin Venezuela ta ayyana dokar ta-baci tare da yin Allah-wadai da abin da ta kira hari na soja.

Rahotanni daga Caracas sun nuna cewa mazauna birnin sun ji fashe-fashe da kuma gobara a wurare da dama.

Wani ganau ya shaida wa yan jarida cewa zuciyarsa na bugawa sosai yayin da ƙafafunsa ke rawa sakamakon tashin hankali.

Amurka ta dade tana zargin Maduro da jagorantar wata babbar ƙungiyar fataucin miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Shugaba Maduro dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa daga gwamnatin Amurka wanda ya ce shaci fadi ne.

Trump ya tabbatar da cafke shugaban Venezuela
Shugaban Amurka, Donald Trump yayin kamfe. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Getty Images

Ikon da Trump ke da shi game da lamarin

Lee ya ce Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ne ya sanar da shi cewa jami’an Amurka sun cafke Maduro bisa samun sammacin kama shi.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: 'Yan bindiga sun daɓawa malaman addini 2 wuka kusa da Abuja

Ya bayyana cewa an yi amfani da matakin sojoji ne domin kare jami’an da ke aiwatar da sammacin kama shugaban Venezuela.

Lee ya ce Rubio ya tabbatar masa cewa Maduro yanzu yana hannun gwamnatin Amurka domin gurfanar da shi a kotu.

Ya ƙara da cewa matakin sojoji da aka gani ya kasance ne domin kare jami’an Amurka daga yiwuwar hari ko barazana kai tsaye.

Sanatan ya ce wannan mataki yana cikin ikon shugaban ƙasa na Amurka ƙarƙashin sashe na biyu na kundin tsarin mulki.

Lee ya gode wa Rubio saboda sanar da shi abubuwan da ke faruwa, yana mai cewa ba a sa ran ƙarin matakan sojoji a Venezuela.

Amurka ta kai hari Venezuela

Kun ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dakarun ƙasarsa sun kai hari ta ƙasa a Venezuela, abin da ya ƙara tsananta rikicin tsakanin kasashen.

Trump ya bayyana cewa harin ya auka ne kan wani wurin lodin jiragen ruwa da ake zargin ana amfani da shi wajen safarar miyagun ƙwayoyi.

Matakin ya tayar da rade-radin yiwuwar faɗaɗar rikici, musamman ganin Venezuela na cewa Amurka na fakewa da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.