Amurka Ta kai Hari Venezuela, Trump Ya Tayar da Fargabar Barkewar Yaƙi

Amurka Ta kai Hari Venezuela, Trump Ya Tayar da Fargabar Barkewar Yaƙi

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dakarun ƙasarsa sun kai hari ta ƙasa a Venezuela, abin da ya ƙara tsananta rikicin Washington da Caracas
  • Trump ya bayyana cewa harin ya auka ne kan wani wurin lodin jiragen ruwa da ake zargin ana amfani da shi wajen safarar miyagun ƙwayoyi
  • Matakin ya tayar da rade-radin yiwuwar faɗaɗar rikici, musamman ganin Venezuela na cewa Amurka na fakewa da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa dakarun Amurka sun kai wani hari ta ƙasa a Venezuela, lamarin da ke nuna sabon mataki mai tsanani a dangantakar da ke tsakanin Amurka da ƙasar.

Trump ya ce harin ya shafi wani wurin sauke jiragen ruwa da ake amfani da shi wajen lodin jiragen da ke jigilar miyagun ƙwayoyi, sai dai har zuwa yanzu hukumomin Venezuela ba su tabbatar da faruwar harin ba.

Kara karanta wannan

Bam a masallaci: Wanda ake zargi ya fadi makudan kudi da aka ba shi a Borno

Sojojin Amurka suna shawagi a sama
Shugaban Amurka, Donald J. Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ce harin na zuwa ne a lokacin da rikici tsakanin Washington da Caracas ke ƙara tsananta tun bayan watannin baya, inda Amurka ke kai hare-hare kan jiragen ruwan Venezuela a yankunan Caribbean da Tekun Pacific.

Abin da Donald Trump ya faɗa kan harin

A yayin taron manema labarai da ya gudanar tare da Benjamin Netanyahu a gidansa na Mar-a-Lago da ke Florida, Trump ya yi amfani da damar wajen sanar da kai harin.

BBC ta rahoto ya ce:

“Mun kai hari yankin tashar jiragen ruwa inda ake lodin jiragen da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi. Mun kai hari kan jiragen, sannan muka kai hari kan wurin da ake lodi. Mun shafe wajen a yanzu.”

Trump bai bayyana ainihin inda harin ya auku ba, haka kuma bai faɗi wace hukuma ce ta aiwatar da shi ba. Ya ce ya san wanda ya kai harin, amma bai ga dacewar faɗin sunan ba, yana mai cewa harin ya faru ne a bakin teku.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damƙe ƴan ƙunar baƙin wake 2 kan tashin bam a masallacin Maiduguri

Rikici tsakanin Amurka da Venezuela

Tun watan Satumban 2025 ne rikici ya fara ƙara tsananta, lokacin da gwamnatin Trump ta fara jerin hare-hare kan jiragen ruwan Venezuela da take zargin suna safarar miyagun ƙwayoyi.

Duk da cewa Amurka ta kai hare-hare ta sama kan fiye da jiragen ruwa 20, inda rahotanni suka nuna mutuwar aƙalla mutane 100, har yanzu ba a gabatar da hujjoji a fili da ke tabbatar da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi ba.

Wasu dakarun kasar Amurka
Sojojin Amurka a bakin fama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Baya ga hakan, dakarun Amurka sun ƙwace wasu manyan tankokin mai na Venezuela, suna masu cewa suna ɗauke da man da aka sanya masa takunkumi.

Trump zai kai hari kasar Iran

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa zai kai hari kasar Iran matukar ta cigaba da kera nukiliya.

Donald Trump ya yi bayani ne ga manema labarai bayan wani zama da ya yi da Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Ya kara da cewa zai cigaba da taimakon kasar Isra'ila idan ta kai hari Iran, muddin Tehran ya cigaba da hada makamai masu linzami.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng