Bayan Najeriya, Trump Ya Gana da Netanyahu kan kai Hare Hare Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargaɗi mai tsanani ga Hamas kan ajiye makami, yana cewa lokaci ya yi da za a dauki wannan mataki
- Trump ya kuma yi barazana ga Iran, yana cewa Amurka za ta sake kai hari idan ta yi yunƙurin farfaɗo da shirin nukiliyarta da ya kai wa hari a baya
- Wadannan kalamai sun biyo bayan ganawar Donald Trump da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a birnin Florida na kasar Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake ɗaukar tsattsauran matsayi kan rikicin Gabas ta Tsakiya, inda ya yi barazana ga ƙungiyar Hamas da kuma ƙasar Iran bayan wata ganawa da ya yi da Benjamin Netanyahu.
Trump ya yi wadannan kalamai ne bayan tattaunawa da Netanyahu a gidansa na hutu da ke Mar-a-Lago a jihar Florida, inda suka mayar da hankali kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma damuwar Isra’ila kan Iran da kuma Hezbollah a Lebanon.

Source: Getty Images
Al-jazeera ta wallafa cewa tattaunawar ta shafi matakan da za a ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya, sai dai ya jaddada cewa dole Hamas ta ajiye makamai.
Gargaɗin Donald Trump ga kungiyar Hamas
Trump ya yi ikirarin cewa Isra’ila na cika nata ɓangaren yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, duk da hare-haren da ake kaiwa kusan kullum wanda rahotanni suka ce sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.
Ya bayyana cewa an tattauna sosai kan makomar Hamas, inda ya ce za a ba ƙungiyar ɗan kankanin lokaci ne kawai domin ta ajiye makamai. A cewarsa, idan Hamas ta gaza yin hakan, za ta fuskanci sakamako mai tsanani.
Duk da abubuwan da Trump ya fada, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani martani kai tsaye daga ɓangaren Hamas.
Shugaba Trump ya ce zai kai hari Iran
A bangaren Iran, Trump ya yi ikirarin cewa yana jin labarin ƙasar na ƙoƙarin sake shirinta na gina nukiliya bayan hare-haren sama da Amurka ta kai a watan Yunin 2025.
Trump ya ce idan Iran na ƙoƙarin farfaɗo da shirin, Amurka ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake murƙushe shi. Ya ce za su “rushe shi gaba ɗaya.”
Batun goyon bayan harin Isra’ila a Iran
Da aka tambaye shi ko Amurka za ta mara wa Isra’ila baya idan ta kai hari kan shirin makaman linzamin Iran, Trump ya ce idan Iran ta ci gaba da wannan shiri, to babu shakka Amurka za ta goyi bayan matakin.

Source: UGC
Rahoton Reuters ya nuna cewa ya bayyana cewa batun nukiliya kuwa ba zai ɗauki lokaci ba, domin a cewarsa, za a ɗauki mataki cikin gaggawa idan an ga alamar barazana.
Magana kan harin Amurka a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi bayani na musamman bayan shugaban Amurka ya sanar da kawo hari Najeriya.
Shehu Sani ya bayyana cewa ta'addanci ba abin so ba ne, saboda haka za a iya neman taimako daga ko ina domin magance shi.
Ya kara da cewa Najeriya za ta iya karbar taimako daga manyan kasashe kamar Rasha da China ko wasu yankunan Afrika domin yaki da 'yan ta'adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

