Gwamnatin Tinubu Ta Yaye Jami'ai 7,000 a Jihohin Arewa 7 Domin Inganta Tsaro

Gwamnatin Tinubu Ta Yaye Jami'ai 7,000 a Jihohin Arewa 7 Domin Inganta Tsaro

  • Gwamnatin Tarayya ta yaye sama da jami’an tsaron dazuka 7,000 domin ci gaba da yaki da ta'addanci a Najeriya
  • Jami'an da aka yaye sun fito ne daga jihohi bakwai domin dakile ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda
  • Nuhu Ribadu ya tabbatar da fara tura jami’an aiki nan take, tare da fara biyansu albashi domin ƙarfafa tsaron cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da kammala horas da sababbin jami’an tsaron dazuka sama da 7,000.

Gwamnatin ta ce an yaye jami'an ne ƙarƙashin shirin Tsaron Dazuka na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An kaddamar da jami'an kula da dazuka domin inaganta tsaro
Ministan tsaro, Christopher Musa da Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

A wasu jihohi aka yaye jami'an?

Hakan na cikin wata sanarwa da shafin ministan yada labarai, Mohammed Idris ya wallafa a manhajar X.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta soki gwamna da ya yi gum da bakinsa bayan harin Amurka a jiharsa

Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) ya bayyana cewa an ɗauko jami’an ne daga jihohi bakwai masu fama da matsalolin tsaro.

An gudanar da bukukuwan yaye jami’an a ranar 27 ga Disamba, 2025, a jihohin Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Niger, Kwara da Kebbi.

Manhajar horon ta haɗa ilimin kare muhalli da dabarun tsaro na zamani, domin samar da jami’ai masu da’a da cikakken shiri.

An yi wa masu horon gwaje-gwajen jiki da tunani, ciki har da dogayen sintiri, tsallake shinge da horon jure wahala.

Dabarun da aka koyawa jami'an kula da dazuka
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a taro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Horon da jami'an tsaron suka samu

Haka kuma, an koya musu dabarun yaƙi a fili, kai ɗauki, ceto, kai farmaki da kare kai a yayin haɗuwa da abokan gaba.

An ba da muhimmanci sosai ga ɗabi’a, bin doka da ƙwarewa, inda aka koyar da haƙƙin ɗan Adam da kare fararen hula.

Da yake jawabi a wajen taron, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce shirin mataki ne na dawo da ikon gwamnati.

Ya tabbatar da cewa za a fara tura jami’an aiki nan take, ba tare da jinkiri tsakanin yaye su da fara aiki ba.

Kara karanta wannan

Sharudan da Tinubu ya bayar kafin harin Amurka kan 'yan ta'adda a Sokoto

A cewarsa, za a fara biyansu albashi da alawus-alawus ba tare da bata lokaci ba, kuma kowanne jami’i zai je wurin aikinsa da aka ware masa.

Rahoton ya nuna cewa kashi 98.2 cikin 100 na masu horon sun kammala shirin cikin nasara.

An kori jami’ai 81 saboda rashin da’a, yayin da wasu biyu suka rasu sakamakon matsalolin lafiya da suka riga suka kasance.

Sababbin jami’an tsaron dazukan ’yan asalin yankunansu ne, lamarin da zai ba su damar amfani da sanin gari da amincewar jama’a.

Shirin Tsaron Dazukan Najeriya na aiki ne tare da Ma’aikatar Muhalli, DSS, Hukumar Kula da Gandun Daji da sauran hukumomin tsaro.

Tinubu zai karbo jiragen yaki daga Amurka

An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shirin gwamnatinsa wurin tabbatar yaki da ta'addanci domin wanzar da zaman lafiya.

Tinubu ya ce Najeriya ta sayi jiragen yaƙi huɗu masu saukar ungulu daga Amurka, waɗanda za su iso ƙasar nan nan gaba kaɗan.

Shugaban ya ce matsalar tsaro ta kai matakin damuwa a duniya, lamarin da ya jawo haɗin gwiwa da ƙasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.