Dan Majalisa a Amurka Ya Fadi Amfanin Harin da Kasarsa Ta Kawo a Najeriya
- Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi tsokaci kan harin da kasarsa ta kawo Najeriya kan 'yan ta'adda a ranar Kirsimeti
- Riley Moore ya bayyana cewa a wannan shekarar Amurka ta ba 'yan ta'adda masu tsatstsauran ra'ayi kyauta a lokacin Kirsimeti
- Dan majalisar ya nuna cewa harin ya yi nasarar hana abin da ya kira kisan da ake yi wa Kiristoci a lokacin Kirsimeti a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Amurka - Wani dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi magana kan harin da kasarsa ta kawo a Najeriya lokacin Kirsimeti.
Riley Moore ya kwatanta hare-haren Kirsimeti da ake kai wa a Najeriya da matakin soji da Amurka ta dauka na kawo hari kan 'yan ta'addan ISIS.

Source: Getty Images
Riley Moore ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Asabar, 27 ga watan Disamban 2025.
Me dan majalisar Amurka ya ce kan harin?
Dan majalisar ya ce a bana an yi amfani da sojojin Amurka wajen kai farmaki kan ’yan ta’adda maimakon sake ganin wani bikin Kirsimeti na zubar da jinin Kiristoci a Najeriya.
Ya bayyana cewa a lokutan Kirsimeti biyu da suka gabata an kashe Kiristoci a Najeriya, amma a bana harin da Amurka ta kawo ya karkata ne kan kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
“Tsawon Kirsimeti biyu da suka wuce, ana kashe Kiristoci a Najeriya. Amma a bana, godiya ga shugaban Amurka, ’yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi sun samu ‘kyautar’ makamai masu linzami na Tomahawk guda 12."
“Wadannan hare-haren da aka yi cikin nasara kan ISIS, tare da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya, su ne mataki na farko wajen tabbatar da tsaron kasar da kuma kawo karshen kisan gillar ’yan’uwanmu Kiristoci."
- Riley Moore

Source: Twitter
Amurka ta kawo hari a Najeriya
Idan za a tuna cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Alhamis cewa sojojin kasarsa sun kai munanan hare-hare kan ’yan ta’addan ISIS a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Donald Trump ya yi alkawarin kara kai farmaki idan har ’yan ta’addan suka ci gaba da kashe Kiristoci.
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a shafinsa na Truth Social, inda ya kara da cewa ma’aikatar yaki ta Amurka ta aiwatar da jerin hare-hare masu inganci sosai.
Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da hare-haren da Amurka ta kawo a ranar Juma’a, 26 ga watan Disamban 2025.
An bukaci Amurka ta kara kawo hari a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi kira ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya fadada hare-haren da kasarsa ta kawo Najeriya.
Shugaban kungiyar Mzough U Tiv, Iorbee Ihagh, ya roƙi Shugaba Donald Trump da ya faɗaɗa hare-haren saman da aka fara a Arewa maso Yamma zuwa jihar Benue.
Cif Iorbee Ihagh ya ce ya rubuta wasiƙa zuwa ga Shugaba Trump domin gode masa bisa matakin da ya ɗauka, tare da roƙon a turo dakarun Amurka zuwa Benue.
Asali: Legit.ng

