2025: Cikakken Jerin Kasashen Afrika 6 da babu Ruwansu da Bikin Kirismeti
- Bikin Kirsimeti a Afirka na bambanta sosai, wanda tasirinsa kan dogara ga gwargwadon addini, al’adu da manufofin gwamnati na kowace ƙasa
- Rahotanni sun nuna cewa ba dukkan ƙasashen duniya ke bikin Kirsimeti ba, duk da cewa ana shagulgulansa a kasashe kamar Amurka
- Legit Hausa ta yi nazari game da wasu kasashen Afrika shida da babu ruwansu da bukukuwan Kirsimeti da dalilan da suka jawo hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rahotanni sun nuna cewa ba dukkan ƙasashe 206 na duniya ke bikin Kirsimeti ba, duk da cewa ana shagulgulansa a ƙasashen Kirista irin su Birtaniya da Amurka, har ma da wasu ƙasashen Musulmi kamar Iraki, Siriya, abin mamaki kuma har da Daular Larabawa (UAE).
A nahiyar Afirka, al’adun Kirsimeti na bambanta matuƙa. Ƙasashe irin su Zambiya, Ruwanda da Najeriya na ba da hutun aiki domin jama'a su yi shagulgula a tsanake.

Source: Getty Images
Bikin Kirsimeti a wasu kasashen Afrika
Sai dai a wasu sassan nahiyar, ranar 25 ga Disamba kan zo ta wuce salin alin, ba tare da wani biki ko samun hutu ba, sakamakon akidu na addini, al’adun gargajiya da manufofin gwamnatinsu, in ji rahoton Business Insider.
A Najeriya, alal misali, Kirsimeti babbar rana ce ta ƙasa, inda ake gudanar da ibadar coci, tarukan iyali da shagulgulan jama’a, lamarin da ke nuna yawan Kiristoci a ƙasar.
Haka nan a Afirka ta Kudu, Seychelles, har ma da Masar, ana shirya bukukuwa, raye-raye da tarukan al’umma, abin da ke nuna muhimmancin Kirsimeti ga rayuwar zamantakewa da al’adu.
Ƙasashen Afirka da ba sa bikin Kirsimeti
Akwai ƙananan ƙasashen Afirka da ba sa ɗaukar Kirsimeti a matsayin hutun jama’a ko bikin ƙasa. Daga cikinsu akwai Aljeriya, Libiya, Somaliya, Muritaniya, Guinea-Bissau da Moroko.
Ko da yake akwai al’ummomin Kirista a waɗannan ƙasashe, yawansu kaɗan ne, kuma bukukuwan su kan kasance a boye, cikin shiru, ko kuma ana shirya su ne domin baƙi da yawon buɗe ido, ba a matsayin bikin ƙasa ba.
A Aljeriya, alal misali, Kiristoci ba su wuce kashi 2 cikin 100 na jama'ar kasar ba, kuma ranar 25 ga Disamba kan wuce kamar kowace rana ta yau da kullum.
A Libiya, inda kimanin kashi 2.7 cikin 100 na jama’a Kiristoci ne, bukukuwan Kirsimeti kan takaita ne ga gidaje da tarukan sirri, sau da yawa cikin yanayin rashin tsaro ga ƙananan al’umma.
Haramta bukukun Kirsimeti a Somaliya
Ƙasashen Somaliya da Muritaniya, waɗanda kusan duka al’ummarsu Musulmi ne, ba sa bai wa Kirsimeti muhimmanci, inda ranar 25 ga Disamba ke kasancewa ranar aiki ta yau da kullum.
A Somaliya ma, an haramta duk wani biki na Kirsimeti a bainar jama’a, sakamakon tsauraran fassarar dokar Musulunci, a cewar rahoton World Population Review.
Sai dai Moroko da Guinea-Bissau na da ɗan bambanci. A Moroko, manyan biranen yawon buɗe ido kamar Marrakech da Casablanca na ganin ado na bukukuwa, tsarin cin abinci na musamman a otal-otal da kuma ibadar tsakar dare ga ’yan kasashen waje Kiristoci, inda al’adun Turai ke haɗuwa da na gida.
A Guinea-Bissau kuwa, ƙananan Kiristoci kan yi bikin cikin shiru a gidajensu, tare da sauƙaƙan abinci da ƙananan kyaututtuka.

Source: Getty Images
Dalilan bambancin bikin Kirsimeti a Afrika
Bambancin yadda ake bikin Kirsimeti a Afirka na da alaƙa da addini, al’adu da manufofin gwamnati. Ƙasashe masu yawan Kiristoci kamar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Lesotho da Namibiya na ɗaukar Kirsimeti a matsayin babban biki na ƙasa, tare da hutun jama’a, ibada, tarukan iyali da shagulgulan al’umma.
A ƙasashen da Musulmi suka fi rinjaye, Kirsimeti yawanci biki ne na sirri ko kuma ba a wani damuwa da shi. Dokokin addini da na gwamnati kan takaita bukukuwa a bainar jama’a, yayin da dalilan siyasa ko tsaro ke ƙara ƙuntatawa.
A ƙarshe, wannan bambanci na nuna yadda Kirsimeti, duk da kasancewarsa biki da duniya ta sani, ke fuskantar fahimta da aiwatarwa iri-iri bisa ga addini, al’adu da tsarin mulki.
A wasu ƙasashen Afirka, Kirsimeti na zuwa da haske, waka da shagulgula; a wasu kuma, yana kasancewa biki na sirri, ko kuma ya wuce kamar kowace rana ta yau da kullum.
Sakon Tinubu a ranar bikin Kirsimeti
A wani labarin, mun ruwaito ecwa, Shugaba Bola Tinubu ya jaddada kudirin kare ’yancin addini tare da kiran ’yan Najeriya su rungumi zaman lafiya da juna a bikin Kirsimeti.
Sakon Kirsimetin shugabannin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsin tattalin arziki da kalubalen tsaro, inda aka jaddada muhimmancin juriya da fahimtar juna.
A sakon Kirsimetin da ya fitar, Tinubu ya ce juriya da mutunta addinai su ne ginshikan hadin kai. Ya ce bai kamata wani dan Najeriya ya sha wahala ko rasa ransa saboda addininsa ba.
Asali: Legit.ng



