An Ware Musulmi a Gefe da Najeriya Ta Rattaba Hannu kan Wata Yarjejeniya da Amurka
- Kasar Amurka da Najeriya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta shekaru biyar da za ta maida hankali wajen inganta harkokin kiwon lafiya
- Gwamnatin Amurka ta tabbatar da lamarin, ta ce za ta zuba jarin kusan Dala biliyan 2.1 a Najeriya amma za a fi bai wa asibitocin kiristoci fifiko
- Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta faɗaɗa damar samun muhimman rigakafi da magani, ciki har da kula da cutar kanjamau da tarin fuka (TB)
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙasar Amurka ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) ta tsawon shekara biyar da Najeriya, domin ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar ƙasar nan.
Sai dai yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta cimmawa da Amurka ta nuna cewa za a maida hankali ne wajen inganta asibitocin kiwon lafiya na mabiya addinin kirista a Najeriya.

Source: Twitter
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta wallafa a shafinta na yanar gizo.
Amurka da Najeriya sun kulla yarjejeniya
Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta faɗaɗa damar samun muhimman rigakafi da magani, ciki har da kula da cutar kanjamau, tarin fuka (TB), zazzabin cizon sauro, lafiyar uwa da jariri, da kuma shirin rigakafin shan inna.
Sanarwar ta bayyana cewa a ƙarƙashin wannan yarjejeniya, gwamnatin Amurka na shirin zuba kusan Dala biliyan 2.1 cikin shekaru biyar masu zuwa a Najeriya.
“Bugu da ƙari, Najeriya za ta ƙara kuɗaɗen da take kashewa a ɓangaren lafiya da kusan Dala biliyan 3 a lokacin da yarjejeniyar za ta gudana.
"Wannan shi ne mafi girman haɗin gwiwar zuba jari da wata ƙasa ta taɓa yi a ƙarƙashin Tsarin Lafiya na Duniya na America First,” in ji sanarwar.
Amurka za ta bai wa kiristoci fifiko
Yarjejeniyar ta kunshi ba da muhimmanci ga cibiyoyin lafiya na addini, waɗanda kiristoci ke gudanarwa, domin suna taka muhimmiyar rawa a tsarin kiwon lafiyar Najeriya.
A cewar sanarwar,
“A halin yanzu, akwai asibitoci da cibiyoyin lafiya na kiristoci sama da 900 a Najeriya kuma su ke kula da kiwon lafiyar kashi 30 cikin 100 na ‘yan ƙasar."
Gwamnatin Amurka ta ƙara da cewa zuba jari a irin waɗannan cibiyoyi na da matuƙar muhimmanci wajen cike giɓi da ƙarfafa asibitocin gwamnati, tare da bunƙasa tsarin kiwon lafiyar ƙasa gaba ɗaya.

Source: Getty Images
The Cable ta tattaro cewa an cimma matsaya kan wannan yarjejeniyar ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke kokarin aiwatar da gyare-gyare da nufin kare rayukan kiristoci daga miyagun 'yan ta'adda.
Amurka za ta turo sojojinta Najeriya?
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Majalisar Amurka sun bayyana cewa kasar ba ta da shirin tura sojojinta zuwa Najeriya, duk da sanya kasar a jerin kasashen da ake tauye hakkin addini.
’Yan majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyun Republican da Democrat da suka kawo ziyara Najeriya ne suka bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Shugaban tawagar, dan majalisa Bill Huizenga, ya ce Najeriya na bukatar taimako wajen magance matsalolin tsaro, amma hakan ba ya nufin shigowar sojojin Amurka.
Asali: Legit.ng

