Benin: An Tsare Tsohon Ministan Tsaro kan Zargin Yunkurin Juyin Mulki
- Gwamnatin Jamhuriyar Benin na ci gaba farautar manyan mutane a kasar da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki
- Kasar ta tsare tsohon Ministan tsaro, Candide Azannai, bisa zargin hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Patrice Talon
- An zargi Azannai mai shekara 66 da shirya makirci kan kasa da kuma tayar da bore, bayan kama shi a birnin Cotonou
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Cotonou, Benin - Gwamnatin kasar Benin ta tsare tsohon ministan tsaro kuma jigo a jam’iyyar adawa bayan zargin yunkurin juyin mulki.
An tsare Candide Azannai 'dan shekara 66 a kokarin ci gaba da bincike kan yunkurin juyin mulki da aka dakile a farkon watan Disambar 2025.

Source: Twitter
Rahoton Arab News ya ruwaito cewa an tuhumi Azannai da shirya makirci kan kasa da kuma tayar da bore, bayan kama shi a makon da ya gabata a hedikwatar jam’iyyarsa da ke birnin Cotonou.
Yunkurin juyin mulki da aka yi a Benin
Hakan ya biyo bayan yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon wanda bai yi nasara ba.
A ranar 7 ga Disamba 2025, wasu sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasa suna ikirarin kifar da Shugaba Patrice Talon, amma dakarun da ke biyayya ga gwamnati sun dakile yunkurin cikin kankanin lokaci, tare da taimakon rundunar sojin saman Najeriya.
Rahotanni sun ce mutane da dama sun mutu yayin rikicin, yayin da wasu daga cikin wadanda ake zargi da jagorantar juyin mulkin, ciki har da Laftanar Kanal Pascal Tigri, suka tsere.
Lamarin ya tayar da hankula a kasashe masu makwabta da Benin da kuma kungiyar ECOWAS a yankin.
Daga bisani, gwamnatin kasar ta fitar da bayani inda ta ce komai ya lafa kuma ba a yi nasarar kifar da gwamnatin ba.

Source: Getty Images
An raka Candide Azanna zuwa gidan yari
Tsarewar Azannai, wanda shi kansa ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin, na zuwa ne bayan an daure mutane da dama wandanda yawancinsu sojoji, bisa laifin cin amanar kasa.

Kara karanta wannan
Benin ta dawo hayyacinta, an daure sojoji da wasu mutum 30 bisa yunkurin juyin mulki
Bayan shafe sa’o’i ana masa tambayoyi a kotun yaki da ta’addanci ta Benin, ‘yan sanda sun raka Azannai zuwa gidan yari da asubahi, cewar France 24.
Duk da yabon da ake yi wa Shugaba Talon kan bunkasa tattalin arziki, masu suka na zarginsa da tafiya da salon mulkin kama-karya, a kasar da a baya aka santa da dimokuradiyya.
A halin yanzu, kasar Benin na fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Arewa, yayin da Talon ke shirin mika mulki a watan Afrilu bayan kammala wa’adin mulkinsa na biyu.
Benin: An daure sojoji da wasu mutum 30
A baya, mun ba ku labarin cewa Jamhuriyar Benin ta yanke wa mutane kusan 30 hukunci bayan zarginsu da yunkurin juyin mulki da tarwatsa gwamnati mai-ci a kasar.
Yawancin wadanda aka kama sojoji ne, kuma ana ci gaba da sa ido a kan Chabi Yayi, ɗan tsohon shugaban kasar Benin kuma jagoran adawa.
An murkushe yunkurin ne da taimakon Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da sojojin Faransa bayan samun labarin shirin juyin mulkin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
