Rukunin 'Yan Najeriya da Takunkumin Trump na Hana Shiga Amurka zai Shafa
- Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump ta sanar da kakaba takunkumin shiga kasar ga ’yan Najeriya saboda dalilan tsaro
- Takunkumin ya shafi masu neman shiga Amurka da katin zama na dindindin da kuma wasu rukunin biza da aka fi amfani da su
- Matakin ya haifar da damuwa a tsakanin ’yan Najeriya, musamman dalibai, ’yan kasuwa da masu shirin yawon bude ido zuwa kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ta sanar da kakaba wasu sababbin takunkuman tafiye-tafiye ga ’yan Najeriya da ke fatan shiga kasar.
A cewar bayanan da aka fitar, an dauki wannan mataki ne bisa hujjar matsalolin tsaro da kuma wahalar tantance bayanan wasu ’yan kasashen waje, ciki har da Najeriya.

Source: Twitter
Premium Times ta rahoto cewa takunkumin ya shafi ’yan Najeriya masu neman shiga Amurka a matsayin masu zama na dindindin da kuma masu rike da wasu nau’o’in biza da aka ayyana.
Bizar B-1 ta shafi 'yan kasuwa
Ma'aikatar harkokin gida ta Amurka ta wallafa cewa bizar B-1 ita ce bizar da ake bai wa mutanen da ke son shiga Amurka domin harkokin kasuwanci na wucin gadi.
Masu wannan biza kan je Amurka ne domin halartar tarurruka, tattaunawar kasuwanci, ko kuma kulla yarjejeniyoyi, ba tare da yin aiki kai tsaye ba.
A karkashin sabon takunkumin, duk ’yan Najeriya masu wannan biza ba za su iya shiga Amurka ba a halin yanzu.
Ma'anar bizar Amurka ta B-2
Binciken da Legit Hausa ta yi ya gano cewa bizar rukunin B-2 kuwa ita ce ta mutanen da ke son zuwa kasar yawon bude ido.
Ana bai wa masu wannan biza damar shiga Amurka domin hutu, ziyartar dangi ko abokai, ko zuwa wurare masu muhimmanci, musamman na tarihi.
Takunkumin ya hana masu wannan biza daga Najeriya shiga kasar, lamarin da ya shafi masu shirin hutu da ziyara kasar.
A daya bangaren kuma, bizar B-1/B-2 ta hadaka ce wadda ke bai wa mutum damar yin kasuwanci da yawon bude ido a lokaci guda.
Bizar rukunin F ta shafi dalibai
Bizar rukunin F ita ce bizar dalibai masu zuwa Amurka domin karatun jami’a ko sauran manyan makarantu a fadin kasar.
Dalibai daga Najeriya da ke amfani da wannan biza kan je Amurka ne domin neman ilimi a fannoni daban-daban.
Takunkumin ya shafi wannan rukuni, wanda ke nuni da cewa daliban Najeriya ba za su iya shiga kasar a wannan lokaci ba.
Bizar Amurka ta rukunin M
Bizar M ana bai wa mutanen da ke son karatun koyon sana’o’i ko karatun da ake amma ba a makaranta mai tsari kamar jami’a ba.
Wannan ya hada da makarantu na koyon fasaha da sana’o’in hannu, kuma masu wannan biza daga Najeriya su ma sun shiga cikin takunkumin.
Bizar rukunin J ta shafi 'yan Najeriya
Bizar J kuwa ita ce bizar shirye-shiryen musayar al’adu da ilimi da ake daukar mutane daga Najeriya zuwa Amurka
Ana amfani da ita wajen shirye-shiryen musayar dalibai, masu bincike, malamai ko masu horaswa daga kasar nan zuwa can.

Source: Facebook
Sabon matakin shugaba Donald Trump ya hana ’yan Najeriya masu wannan biza shiga kasar Amurka.
Amurka ta gargadi 'yan Najeriya kan biza
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Amurka ta gargadi 'yan Najeriya kan mika bayanan bogi.
Jakadan Amurka a Najeriya ne ya bayyana haka, inda ya ce za su dauki matakai masu tsauri a kan wanda aka kama.
A bayanin da ya yi, jakadan ya shaida cewa duk wanda aka kama da laifin za a hana shi shiga Amurka har abada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


