Trump: Sashen Kamfanin Tiktok Zai Koma Karkashin Kulawar Amurka

Trump: Sashen Kamfanin Tiktok Zai Koma Karkashin Kulawar Amurka

  • Kamfanin TikTok ya amince da yarjejeniyar ware reshensa a Amurka, inda za a kafa sabon kamfani tare da gungun masu zuba jari 'yan kasar
  • Yarjejeniyar na nufin ceto makomar TikTok a kasar Amurka, bayan dokar da ta bukaci a raba shi da ByteDance ko a haramta shi gaba daya
  • Rahoto ya ce sabon tsarin mallaka zai bai wa Amurkawa damar ci gaba da amfani da manhajar, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan kammala yarjejeniyar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Kamfanin TikTok ya sanar da cewa ya kulla yarjejeniya ta ware reshen aikinsa a Amurka, domin kafa sabon kamfani tare da wasu manyan masu zuba jari ’yan kasar.

Shugaban TikTok, Shou Chew, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikawa ma’aikata, inda ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar, ko da yake har yanzu ba a kammala dukkan matakan shari’a da na doka ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke bokaye da kudin kasashen waje na boge bayan damfarar 'yan Najeriya

Shugaba Donald Trump da Tiktok
Donald Trump na Amurka da tambarin Tiktok. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CNN ta wallafa cewa matakin na zuwa ne bayan dokar da aka zartar a bara, wadda ta bukaci TikTok ya ware 'yan Amurka a karkashin kulawar asalin kamfaninsa na ByteDance, ko kuma a dakatar da ayyukansa a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon tsarin mallakar TikTok a Amurka

A cewar Shou Chew, yarjejeniyar ta tanadi kafa sabon kamfani na TikTok a Amurka, wanda kashi 50 cikin 100 na hannun jarinsa zai kasance a hannun masu zuba jari a Amurka.

Wadanda za su mallaki hannun jarin sun hada da kamfanin Oracle, kamfanin zuba jari na Silver Lake, da kuma MGX mai samun goyon bayan masu zuba jari daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sauran kaso na mallaka, a cewar bayanin, za su kasance a hannun wasu masu hannun jari da ke da alaka da ByteDance, yayin da ByteDance da kan shi zai rike kaso 19.9 cikin 100 na sabon kamfanin.

BBC ta rahoto Chew ya ce har yanzu akwai sauran aiki kafin a rufe yarjejeniyar gaba daya, amma ana sa ran kammala dukkan matakai kafin 22 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Bayan suka ta ko ina, an dakatar da yi wa dogarin Shugaba Tinubu karin girma

Dalilin kawo dokar TikTok a Amurka

Dokar Amurka ta tanadi cewa dole ne ByteDance ya raba kusan kashi 80 cikin 100 na kadarorin TikTok na Amurka ga masu zuba jari marasa alaka da China.

An ce Shugaba Donald Trump ya jinkirta aiwatar da dokar sau da dama, yayin da ake kokarin cimma yarjejeniya da za ta mika ikon TikTok na Amurka ga hannun ’yan kasar.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A Satumban 2025, gwamnatin Trump ta sanar da cimma matsaya kan yarjejeniyar, tare da sanya hannu kan umarni na musamman da ya bai wa kamfanin wa’adin karin kwanaki domin kammala shirin.

Tsaro da kula da bayanai a TikTok

A karkashin sabon tsarin, za a sake sauya fasalin TikTok bisa bayanan masu amfani na Amurka, yayin da kamfanin Oracle zai kula da adana bayanan ’yan kasar.

Sabon kamfanin na Amurka kuma zai dauki nauyin kula da abun da ake wallafawa da tsare-tsaren amfani da manhajar a cikin kasar.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Borno da wani ya tashi bam, ya kashe sojojin Najeriya

Sai dai sanarwar Chew ta nuna cewa reshen TikTok na duniya da ke karkashin ByteDance zai ci gaba da kula da harkokin kasuwanci kamar talla, kasuwancin intanet da dabarun tallata manhajar.

Amurka ta kai hari Tekun Pacific

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Amurka ta sanar da cewa ta kai wani hari mai zafi a tekun Pacific.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin Amurka sun yi nasarar kashe mutane hudu a jirgin ruwan da suka farmaka.

Kwamandan rundunar ya bayyana cewa sun kai harin ne bisa umarnin ministan yaki na Amurka kan zargin da ake yi wa jirgin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng