'Yan Sanda Sun Tono Wata Doka, Za a Iya Hukunta Matar da Ta Ki Saduwa da Mijinta
- 'Yan sanda sun gargadi ma'aurata kan kin saduwa da abokin aure da gangan a kasar Ghana, sun ce hakan ya zama karya doka
- Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda (ACP) Dennis Fiakpui ne ya bayyana hakan, ya ce doka ta tanadin hukunci kan hana abokin aure jima'i
- Ya ce mata da ke hana mazajensu kan su na iya fuskantar tuhuma, kuma idan aka same su da laifi, za iya yanke musu hukuncin daurin shekaru biyu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ghana - Rundunar 'yan sandan kasar Ghana ta yi gargadi ga ma'aurata kan illa da hadarin hana abokin zama damar saduwar aure musamman idan ya nemi hakan.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta binciko gaskiya, ta kori manyan jami'ai 38 daga aiki a NSCDC
'Yan sandan sun bayyana cewa mata ta hana mijinta saduwa da ita, ko miji ya ki kwanciya da matarsa laifi ne a kundin tsarin mulkin Ghana, kuma ana iya daure mutum a gidan yari.

Source: Getty Images
Leadership ta rahoto cewa 'yan sandan Ghana sun bayyana cewa yawan hana tarawa a cikin aure na iya kasancewa a matsayin cin zarafin zuciya, wanda doka ta tanadi hukunci a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun gargadi ma'aurata a Ghana
Wani mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda (ACP) Dennis Fiakpui ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Ghana.
Fiakpui, wanda ke riƙe da muƙamin Mataimakin Kwamandan ’Yan Sanda na Yankin Oti, ya ce Dokar Hana Cin Zarafi a Aure ta Ghana ta 2007, ta ce wasu dabi’u a mu'amalar aure na iya zama cin zarafin zuciya.
A cewarsa, idan ɗaya daga cikin ma’aurata ya hana ɗayan damar kwanciyar aure da gangan ta yadda hakan ke janyo damuwa da raɗaɗin zuciya, to ana iya ɗaukar mataki a kansa idan an kai ƙara kuma aka tabbatar da laifin a gaban kotu.
“Hana abokin aure jima’i na iya zama cin zarafin zuciya,” in ji Fiakpui.
Ya ƙara da cewa matan da ke hana mazajensu wannan hakki na iya fuskantar tuhuma, kuma idan aka same su da laifi, hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari na iya hawa kansu.
Za a iya hukunta miji kan cin abinci
Sai dai ya jaddada cewa dokar ba ta shafi mata kaɗai ba, domin maza ma na iya fuskantar irin wannan tuhuma idan suka ki sauke hakkin matayensu.
“Idan miji ya ƙi cin abincin da matarsa ta dafa, ya jefa ta cikin damuwa da raɗaɗin zuciya, za ta iya kai ƙara.
Haka kuma idan miji na yawan dawowa gida da dare yana janyo mata damuwa, za ta iya kai ƙara ga sashen DOVSSU,” in ji shi.

Source: Getty Images
ACP Fiakpui ya kuma ƙarfafa gwiwar ma’auratan da ke fama da cin zarafin zuciya a aurensu da su nemi taimako ta hanyoyin doka da suka dace, maimakon ci gaba da jurewa da rayuwa cikin damuwa, rahoton Daily Post.
'Yan sanda sun kama amarya a Delta
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun 'yaan sanda sun kama amarya bisa zargin yin garkuwa da kanta domin biyan bashin N3.6m a jihar Delta.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bright Edafe, ya bayyana cewa sun samu rahoton garkuwa da matar a ranar 21 ga Yuli, 2025.
Edafe ya ƙara cewa bayan cafke waɗanda ake zargi, ɗaya daga cikinsu ya amsa cewa ba a yi garkuwa da matar ba, illa dai sun haɗa baki ne da ita don karɓar kuɗin fansa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

