Amurka Ta kai Hari Ta Kashe Mutane bayan Trump Ya Sa wa Najeriya Takunkumi

Amurka Ta kai Hari Ta Kashe Mutane bayan Trump Ya Sa wa Najeriya Takunkumi

  • Sojojin Amurka sun ce sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ake zargin yana safarar miyagun ƙwayoyi a gabashin Tekun Pacific
  • Harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wani makamancinsa da aka kai a farkon makon nan, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane
  • Matakin na cikin wani shiri da gwamnatin Donald Trump ta ce tana yi da nufin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi a Kudancin Amurka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa ta sake kai wani hari kan jirgin ruwa da ake zargin yana da alaƙa da safarar miyagun ƙwayoyi a gabashin Tekun Pacific, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu.

A cewar rundunar sojin Amurka, harin ya gudana ne a ranar 17, Disamban 2025, bayan umarni kai tsaye daga Ministan yaki, Pete Hegseth.

Kara karanta wannan

Benin ta dawo hayyacinta, an daure sojoji da wasu mutum 30 bisa yunkurin juyin mulki

Shugaba Trump da sojojin Amurka
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rundunar sojin Amurka ta bayyana a shafinta na X cewa jirgin ruwan yana aiki ne a ruwan duniya, ba ƙarƙashin ikon wata ƙasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka ta kai hari tekun Pacific

Rahoton CNN ya nuna cewa rundunar sojin Amurka ta ce dakarun JTFSS ne suka kai farmakin, inda suka kai harin kai tsaye kan jirgin ruwan da suka danganta da wata ƙungiya da aka ayyana a matsayin 'yar ta’adda.

Rundunar ta ƙara da cewa babu wani jami’in sojan Amurka da ya samu rauni ko aka mutu a yayin farmakin da suka kai.

Wannan harin ya zama na biyu cikin mako guda, bayan harin da aka kai a ranar Litinin da ta gabata kan wasu jiragen ruwa uku, inda aka kashe mutum takwas.

Wadanda Amurka ta kashe a hare-hare

Rahotanni daga Amurka sun nuna cewa akalla mutum 99 ne aka kashe tun bayan fara jerin hare-haren da ake kai wa kan jiragen ruwa da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye coci suna harbe harbe, sun sace mutane a Kogi

An bayyana cewa hare-haren na ƙarƙashin wani shiri na musamman da Amurka ta kira Operation Southern Spear.

Gwamnatin Trump ta ce shirin yana da nufin rage shigowa da miyagun ƙwayoyi zuwa Amurka tare da karya hanyoyin safarar da ke gudana a Tekun Pacific da yankunan Kudancin Amurka.

Wannan ya zo ne tare da ƙara yawan sojoji da kayan yaƙi da Amurka ke turawa yankin Caribbean bayan umarnin shugaba Trump.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke ƙara matsin lamba kan ƙasar Venezuela bayan zargin kasar da satar “man fetur, ƙasa da wasu dukiyoyi” Amurka.

Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, ya mayar da martani yana zargin Amurka da ƙoƙarin kifar da gwamnatinsa tare da mallakar albarkatun ƙasarsa.

Trump ya kakabawa Najeriya takunkumi

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin shugaba Donald Trump ta sanya Najeriya cikin kasashen da za su fuskanci takunkumin biza.

Matakin na zuwa ne bayan ofishin jakadancin Amurka ya gargadi 'yan Najeriya game da tura bayanan bogi yayin neman biza.

Kara karanta wannan

Hankalin Trump ya tashi, kungiyar ISIS ta kashe sojojin Amurka a tsakiyar Syria

Yayin da a ake bayyana dalilin saka Najeriya a jerin kasashen, Amurka ta ce matsalolin Boko Haram da ISWAP sun yi yawa a kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng