Ana Wata ga Wata: Kasar Amurka Ta Kakaba wa Najeriya Sabon Takunkumi
- Shugaban kasa Donald Trump ya sanya Najeriya a cikin jerin kasashe 15 da aka kakaba wa takunkumin balaguro zuwa Amurka
- Fadar White House ta ce ayyukan Boko Haram da IS suna kawo cikas ga tantance masu neman biza daga kasar Najeriya
- Trump ya kakabawa wasu kasashen Afrika uku cikakken takunkumin shiga Amurka bisa wasu dalilai da suka girmi na Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Gwamnatin Amurka ta saka Najeriya cikin jerin kasashen da aka kakaba wa takunkumin balaguro, saboda wasu matsaloli na tsaro da kuma takardun shige-da-fice.
Fadar White House ta bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da ta fitar da sabuwar sanarwar shugaban kasa game da kasashen da ke fuskantar cikakken takunkumi ko na wani bangare wajen shiga Amurka.

Source: Getty Images
Amurka ta kakaba wa Najeriya takunkumi
Najeriya na cikin kasashe 15, wadanda galibinsu daga nahiyar Afirka, da aka kakaba masu takunkumi mara tsauri, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga Najeriya, sauran kasashen da ke cikin jerin sun hada da Angola, Antigua and Barbuda, Benin, Côte d’Ivoire, Dominica, Gabon da Gambia.
Sauran kasashen kuwa su ne Malawi, Mauritania, Senegal, Tanzania, Tonga, Zambia da Zimbabwe.
Fadar White House ta ce an dauki wannan mataki ne bisa la’akari da rahotannin tsaro da na shige-da-fice da ke nuna matsaloli a wasu kasashen.
Dalilin saka Najeriya cikin jerin
A cewar Fadar White House, kungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da IS na ci gaba da aiki a wasu sassan Najeriya, lamarin da ke tsananta wahala wajen tantancewa da binciken mutanen da ke neman shiga Amurka.
A sanarwar da aka wallafa a shafinta na intanet, fadar shugaban kasar ta ce:
“Kungiyoyin ta’addanci masu tsattsauran ra’ayi kamar Boko Haram da IS na cin karensu ba babbaka a wasu sassan Najeriya, wanda ke haifar da matsaloli wajen tantancewa da binciken bayanan masu neman shiga Amurka.”
Har ila yau, Amurka ta ambaci rahoton Overstay Report, inda ta ce Najeriya tana da 5.56% na mutanen da ke wuce wa’adin bizar B-1/B-2, yayin da 11.90% na masu bizar F, M da J ke wuce wa’adin zaman su.

Source: Getty Images
Kasashe 5 sun fuskanci cikakken takunkumi
Kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar daga yankin Sahel na cikin kasashe biyar da aka kakaba musu cikakken takunkumin shiga Amurka.
Fadar White House ta danganta hakan da ayyukan kungiyoyin ta’addanci a kasashen. Sauran kasashen biyu da aka saka cikin wannan mataki su ne Sudan ta Kudu da Syria.
A halin yanzu, takunkumin shiga Amurka gaba daya na ci gaba da aiki kan ‘yan kasashen Afghanistan, Myanmar (Burma), Chad, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan da Yemen.
Haka kuma, Laos da Sierra Leone, wadanda a baya ke cikin jerin masu takunkumi mara tsauri, yanzu an saka su cikin cikakken takunkumi.
'Yan bindiga sun kashe dalibai a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Donald Trump, ya yi jimamin mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu tara a wani harbin bindiga da ya faru a jami’ar Brown.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin liyafa a Fadar White House, inda ya ce ya wajaba a fara taron da addu’a da girmamawa ga wadanda suka rasa rayukansu.
A jawabin da ya yi, Trump ya ce wadanda suka mutu yanzu suna “kallonmu daga Aljanna,” yana mai nuna alhini da ta’aziyya ga iyalansu da al’ummar jami’ar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


