Yadda Hadiman Buhari Suka So Ayyana Ahmad Lawan a matsayin Dan Takarar APC a Zaben 2023
- An kaddamar da wani littafi kan rayuwar tsohon shugaban kasar Najeriya marigayi Muhammadu Buhari a ranar 15 ga Disamba
- A cikin littafin an bayyana yadda wasu hadiman marigayi Buhari suka tafka masa karya dangane da zaben tsaida gwanin shugaban
- Hadiman dai sun yi karyar cewa Buhari ya zama Sanata Ahmad Lawan a matsayin dan takarar da yake goyon baya a zaben na APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu manyan hadiman tsohon Shugaba Muhammadu Buhari sun fitar da abin da aka bayyana a matsayin “umarnin shugaban kasa na bogi” kan zaben fitar da gwani na APC.
Hadiman sun fitar da umarnin ne ga Sufeto Janar na ’yan sanda (IGP), shugaban DSS da shugaban hukumar NIA, a jajibirin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC na shekarar 2023.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe a cikin wani littafi kan rayuwar Muhammadu Buhari da aka rubuta.
An kaddamar da littafin mai taken “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari”, wanda Dr. Charles Omole ya wallafa, a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025.
Yadda aka yi wa Muhammadu Buhari karya
A cikin littafin an bayyana cewa hadiman sun ba da umarnin ne domin a ayyana shugaban majalisar Dattawa na wancan lokaci, Ahmad Lawan, a matsayin zabin jam’iyyar don takarar shugaban kasa.
A cewar littafin, wasu manyan mutane da ke kusa da Buhari sun tuntubi Sufeto Janar na ’Yan Sanda (IGP), shugaban DSS da shugaban hukumar NIA a jajibirin zaben tsaida gwanin APC da aka gudanar a Abuja.
Manyan mutanen sun yi ikirarin cewa suna aiki ne bisa umarnin Buhari domin a tura jami’an tsaro don tabbatar da cewa Ahmad Lawan ya zama dan takarar jam’iyyar ta hanyar maslaha, jaridar The Guardian ta dauko labarin.
Tsohon IGP, Alkali Baba, wanda aka ambato a cikin littafin, ya ce ya yi watsi da wannan umarni kai tsaye, sannan ya shawo kan takwarorinsa cewa lamarin na bukatar a gaggauta neman karin bayani daga shugaban kasa da kansa.
A cewar marubucin:
“Su ukun sun yanke shawarar neman ganawa da Shugaban kasa cikin gaggawa. Da suka tambayi ko akwai wani karin umarni game da taron jam’iyya, Shugaban kasa ya ce babu.”
Me Buhari ya yi baya gano lamarin?
A cewar bayanin, Buhari ya yi dariya lokacin da aka shaida masa cewa tuni aka fara shagali a inda Ahmad Lawan yake bisa rade-radin cewa Shugaban kasa ya amince da shi a matsayin dan takarar APC.
“Ya fayyace a sarari cewa bai zabi kowa ba. ’Yan Najeriya su zabi wanda suke so, kuma hukumomin tsaro kada su tsoma baki."

Source: Facebook
Daga bisani, IGP ya koma ya sanar da wadanda ke bayan wannan yunkuri cewa Buhari ba shi da wani dan takara na musamman, kuma ba za a yi amfani da hukumomin tsaro wajen karkatar da zaben fidda gwanin jam’iyyar ba.
Marubucin ya ce wannan lamari ya nuna yadda Buhari ya dage wajen kin mayar da hukumomin tsaron kasa kayan aikin siyasa, ko da kuwa hakan na janyo masa bakin jini a cikin jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan
Bayan shekaru, an ji abin da ya hana Buhari bayyana wanda yake so ya gaje shi a 2023
Batun rashin lafiyar Buhari a 2017
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta yi magana kan rashin lafiyar da mijinta ya yi na tsawon lokaci a shekarar 2017.
Aisha Buhari ta bayyana cewa rashin lafiyar marigayi Buhari da ta tilasta masa daukar hutun jinya na tsawon kwanaki 154 a shekarar 2017 ta samo asali ne daga lalacewar tsarin cin abinci.
Matar tsohon shugaban kasar na Najeriya ta bayyana haka ne yayin da ta karyata cewa ba wai guba ko wata cuta ta dabam ba ce ta kama Buhari ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

