Malaman Musulunci Sun Yi Ca da Malami Ya Yi Hasashen Tashin Duniya a 2026

Malaman Musulunci Sun Yi Ca da Malami Ya Yi Hasashen Tashin Duniya a 2026

  • Wani jagoran addini da ke duba a Pakistan, Riaz Ahmed Gohar Shahi, ya yi hasashen tashin duniya nan kusa
  • Shahi ya ce gingimemen tauraro zai hallaka duniya bayan ya ci karo da ita wanda zai kawo karshe rayuwa
  • Malaman Musulunci sun yi watsi da hasashen, suna kiran hakan bidi’a da kuma ikirarin annabci da ba ya da hujja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Islamabad, Pakistan - Wanda ya kafa ƙungiyoyin RAGS, Riaz Ahmed Gohar Shahi, ya yi hasashen wani abin tsoro da zai kawo ƙarshen duniya.

Shahi ya ce lamarin zai kawo karshe dukkan rayuwar mutane, hasashen da ake alakanta shi da suna “Nostradamus na Pakistan” ya tayar da hankula a duniya.

An hasashen tashin duniya a 2026
Gingimemen tauraro da ake hasashen zai ci karo da duniya. Hoto: @UAPWatchers, @MAstronomers/X.
Source: Twitter

Malami ya yi hasashen tashin duniya

Shahi ya bayyana cewa wani babban tauraro mai haɗari yana taho wa duniya, kuma zai yi mummunan karo da ita, wanda zai jawo “gagarumar barna, cewar India.com.

Kara karanta wannan

Bidiyon da ya sa wasu 'yan Najeriya ke neman sai Matawalle ya yi murabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, wannan tashin hankalin zai hallaka dukkan rayuka tare da kawo karshen mutane a duniya.

Rahoton The Comet a X ya ce Shahi ya yi wannan hasashe ne inda ya ce wani jigo daga sama zai bugi Duniya a shekarar 2026.

Majiyoyi sun ruwaito cewa jagoran masu duban ya dage kan cewa wannan lamari zai kawo ƙarshen rayuwa a duniya gaba ɗaya.

Haka kuma an ta tabbatar da cewa Shahi ya rubuta wannan hasashe tun cikin littafinsa na shekarar 2000 mai suna 'The Religion of God'.

Ɗaya daga cikin manyan ikiraran da ya yi shi ne cewa wannan tauraron zai jawo lalacewar rayuka amma ya ce ba zai zama cikakkiyar halaka ba, saboda Allah kawai yana son ya tsoratar da mutane.

An yi ca kan malamin duba bayan hasasehn tashin duniya
Malamin duba mai karyar Annabta da ya yi hasashen tashin duniya a 2026. Hoto: @NisarAhmad1981.
Source: Twitter

Malaman Musulunci sun ƙaryata hasashen malami

Malaman Musulunci da dama sun yi watsi da koyarwarsa, suna kiran hasashensa bidi’a da kuma rashin tushe.

Kara karanta wannan

An buga rikici da Matawalle a ma'aikatar tsaro kafin Badaru ya ajiye aiki

Sun soki ikirarin da yake yi na cewa shi annabi ne inda suka caccake shi game da abin da yake hasashe.

An haifi Shahi a Pakistan, ya kuma kafa kungiyar RAGS wanda yanzu aka fi sani da Messiah Foundation International (MFI).

An haramta littattafansa da koyarwarsa a kasar, kuma mabiyansa ba sa haduwa a bainar jama’a.

A cewar MFI, Shahi yana ikirarin cewa shi ne Mahdi, Almasihu, da kuma Kalki Avatar, manyan shugabanni da ake tsammanin zuwansu a ƙarshen zamani domin kawar da mugunta.

Shahi ya bace a yanayi mai cike da rikitarwa shekara guda bayan buga littafinsa, a birnin London a watan Satumbar 2001.

Bai sake bayyana ba tun daga lokacin, duk da haka mabiyansa suna iƙirarin yana raye a ɓoyayyen wuri. Idan yana da rai, yanzu zai kasance mai shekaru 84.

NASA ta musanta duk wata barazana

A halin yanzu, hukumar sararin samaniya ta Amurka, NASA, ta bayyana cewa babu wani tauraro da ke barazanar karo da duniya nan kusa. T

Kara karanta wannan

"Akwai abin da ba a karya da shi": Rarara ya fadi dalilin aikin alheri a kauyensu

auraron da aka fi tsoro shi ne Apophis a 2029, amma an tabbatar ba zai bugi duniya ba.

Haka kuma an yi zaton tauraro '2024 YR4' zai zama barazana a 2032, amma yanzu an tabbatar cewa ko da matsala za ta taso, zai iya karo da wata ba duniya ba.

Agogo da ke hasashen tashin duniya ya motsa

A baya, an ji cewa agogon da ke hasashen tashin duniya ya matsa da dakika daya, wanda hakan ke nufin cewa nan da dakiku 89 za ayi tashin alkiyama.

Kungiyar BAS ta ce yakin Ukraine da rikicin Gabas ta Tsakiya na iya haddasa mummunan yaki, yayin da ake kara amfani da nukiliya.

BAS ta jaddada cewa Amurka, China da Rasha suna da karfin ruguza duniyar, don haka su ne ke da alhakin dakile masifar da ke tunkarota.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.