Trump na Shirin Kawo Hari, Faransa Ta Fadi Taimakon da Za Ta Yi wa Najeriya

Trump na Shirin Kawo Hari, Faransa Ta Fadi Taimakon da Za Ta Yi wa Najeriya

  • Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce ya tattauna da Shugaba Bola Tinubu kan karuwar barazanar ta’addanci a Arewacin Najeriya
  • Faransa ta yanke shawarar cewa za ta taimaka wa Najeriya tare da yin kira ga sauran kasashe su ba da tasu gudunmawar a yaki da ta'addanci
  • Wannan na zuwa ne bayan karin hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane, da kuma matsin lamba daga Shugaba Donlad Trump

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Faransa - Shugaba Emmanuel Macron, ya bayyana cewa Faransa sa na tare da Najeriya wajen fuskantar matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Emmanuel Macron ya ce kasar Faransa za ta ba Najeriya dukkanin gudunmawar da take bukata don magace matsalar ta’addanci a yankin Arewa.

Emmannuel Macron ya ce Faransa za ta taimakawa Najeriya
Shugaba Bola Tinubu tare da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron. Hoto: @officialABAT
Source: Facebook

Faransa za ta taimakawa Najeriya kan tsaro

Macron ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya ce ya tattauna da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kai tsaye.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunayen jakadun kasashe 21 da suka mika wa Tinubu takardu a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Macron, Najeriya na fuskantar kalubale masu tsanani, kuma Faransa na da niyyar karfafa hulda da gwamnatin Tinubu domin tunkarar matsalolin da suke addabar manyan yankuna.

Ya bayyana cewa Tinubu ya roki karin hadin gwiwarsa, kuma gwamnatin Faransa za ta dauki matakai masu inganci don taimaka wa al’ummomin da ke fuskantar tasirin rikice-rikicen tsaro.

Macron ya rubuta cewa:

“Na yi magana da Shugaba Tinubu na Najeriya. Na mika sakon goyon bayan Faransa kan kalubalen tsaro da ake fuskanta, musamman barazanar ta’addanci a Arewa.”

Faransa ta nemi hadin kan kasashen duniya

Ya kara da cewa Faransa za ta kara zurfafa huldar ta da hukumomin Najeriya tare da tallafawa al’ummomin da rikice-rikicen suka shafa.

Shugaban ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da sauran kasashe masu ruwa da tsaki za su kara matsa lamba don dakile yaduwar ta’addanci.

“Muna kira ga dukkan abokan hulda da su karfafa tsarin gudunmawarsu a wannan fanni. Ka da a zura idanuwa ana kallo kawai.”

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

- Emmanuel Macron.

Wannan furuci na Macron ya biyo bayan jerin hare-haren ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, lamarin da ya ja hankalin kungiyoyin kasa da kasa da gwamnatocin waje.

Faransa ta ce akwai bukatar kasashen duniya su taimakawa Najeriya a yaki da matsalar tsaro.
Shugaba Bola Tinubu tare da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Taimakon Faransa bayan barazanar Trump

A lokaci guda, barkewar ra’ayoyi daga kasashen waje ya kara daukar hankali, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Najeriya da cin zarafin Kiristoci da kuma yi masu kisan kare dangi.

Sai dai, gwamnatin Najeriya ta musanta zargin Trump, tana mai cewa rashin tsaro na shafar addinai da kabilu daban-daban, ba bangare daya kadai ba.

Masana harkokin tsaro na ganin cewa irin wannan tattaunawa tsakanin Tinubu da Macron zai kara wa Najeriya damar samun kayayyakin aiki, bayanan leken asiri, da sauran muhimman dabaru da ke taimakawa wajen dakile tsaro wanda ya dade yana addabar kasar nan.

Kasashen da ke taimakawa Najeriya kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce ƙasashen duniya na haɗa kai da Najeriya wajen yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro

Nuhu Ribadu ya ce mutane da dama daga sassan duniya na zuwa domin taimakawa Najeriya a magance rashin tsaro, ciki har da Amurka Faransa, Birtaniya da wasu da dama.

Ribadu ya ƙara da cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyi, daga duk wata barazana ta tsaro da za su iya fuskanta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com