Kisan Kiristoci: Amurka Ta Ware Wasu 'Yan Najeriya, Ta Sanya Masu Takunkumi
- Amurka ta fara daukar matakai da nufin kawo karshen kisan kiyashin da take zargin ana yi wa kiristoci a Najeriya da wasu kasashe
- A wata sanarwa da ma'aikatar wajen Amurka ta fitar, ta hana bada biza ga wadanda ke da hannu a ayyukan tauye 'yancin addini
- Ta jaddada cewa kamar yadda Shugaba Donald Trump ya fada, Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan kiristoci a duniya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Gwamnatin Amurka ta fara daukar matakai kan wasu 'yan Najeriya, wadanda take zargin suna goyon bayan kisan kiyashin da ake wa kiristoci a kasar.
Idan ba ku manta ba, Amurka ta sanya Najeriya a jerin kasahen da ake tauye hakkin addini saboda zargin kisan kiristoci.

Source: Getty Images
Rukunin mutanen da matakin Amurka ya shafa

Kara karanta wannan
Aski ya zo gaban goshi: Majalisar Amurka ta fara zama da bincike kan 'kisan Kiristoci'
The Nation ta ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta sanya takunkumin hana biza ga duk mutanen da suka jagoranta, suka ba da izini ko suke goyon bayan tauye ’yancin addini a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar a ranar Laraba mai taken “Yaki da Mugayen Hare-haren da ake kaiwa Kiristoci a Najeriya da Duniya."
Wannan mataki na zuwa ne bayan Majaliar Dokokin Amurka ta yi zama kan karuwar hare-hare a Najeriya, wanda ta bayyana da abin damuwa matuka.
Tun a baya dai Amurka ta ce ba za ta zuba ido tana kallo wasu kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin Islama na kokarin karar da kiristocin Najeriya ba, cewar The Cable.
Gwamnatin Najeriya ta fito a lokuta daban-daban ta musanta zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi, inda ta ce Amurka ba ta fahimci hakikanin matsalar tsaron kasar ba.
A wani bangaren matakan da ta shirya dauka domin kare rayuka kiristoci, gwamnatin Amurka ta sanar da nmtakin hana biza ga duk mai alaka da masu take hakkin addini a Najeriya.
Wane mataki gwamnatin Amurka ta dauka?
A sanarwar da gwamnatin ta fitar yau Laraba, ta ce:
"Sabon tsarin da muka kawo a karkashin Sashe na 212(a)(3)(C) na Dokar Shige da Fice ta Amurka zai bai wa Ma’aikatar Harkokin Waje damar hana bayar da biza ga mutanen da ke da hannu a ayyuka tauye 'yancin addini.
"Za mu hana biza ga mutanen da suke jagoranta, suka amince, suka bada gudunmawa, suka shiga ko suka aikata wani abu na tauye ’yancin addini. Wannan zai iya shafar iyalansu na kusa idan ta kama."
“Kamar yadda Shugaba Trump ya fada, Amurka ba za ta nade hannu ba yayin da irin wadannan abubuwa ke faruwa a Najeriya da wasu kasashe da dama.
"Saboda haka wannan mataki zai shafi Najeriya da kowace gwamnati ko mutum da ke da hannu a ayyukan take ’yancin addini.”

Source: Twitter
'Dan bindiga ya harbi sojojin Amurka
A baya, kun ji cewa wani dan bindiga ya bude wa sojoji wuta a kusa da fadar shugaba Amurka, White House da ke birnin Washington DC.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya kai ga rufe fadar shugaban kasar Amurka watau White House na wucin gadi a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba, 2025.
A lokacin da wannan lamari ya faru, Shugaba Trump yana Florida domin shirye-shiryen biki da aka saba yi a duk shekara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

