Tofa: Trump Zai Dauki Mataki Mai Tsauri kan 'Yan Najeriya Masu Son Komawa Amurka

Tofa: Trump Zai Dauki Mataki Mai Tsauri kan 'Yan Najeriya Masu Son Komawa Amurka

  • Donald Trump ya ce tsarin hijira zuwa Amurka ya haddasa matsaloli ga tsaro, da cunkuso a makarantu, asibitoci da gidaje
  • Shugaban kasar ya ce zai dakatar da shigowar masu neman zama a Amurka daga ƙasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya
  • Trump ya yi alƙawarin soke takardun zama, korar masu laifi, da kuma ɗaukar matakai masu tsauri kan bakin haure a Amurka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - A wani jawabi da ya yi yayin bikin ibada, shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin maganar da ta jawo cece-kuce a soshiyal midiya.

A yayin taron, Trump ya ce zai hana ’yan ƙasashen da ya kira “Third World countries”, watau ƙasashe masu tasowa, da suka shafi Afrika, Asia da Latin Amurka komawa Amurka da zama.

Kara karanta wannan

Trump zai sake tunani kan kasashe 19 karkashin CPC bayan harin 'White House'

Shugaba Trump ya yi barazanar hana shigowar 'yan Najeriya da wasu kasashe Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump ya shirya sauya tsarin hijiran kasar Hoto: @WhiteHouse
Source: Twitter

Trump na shirin sauya tsarin shiga Amurka

Trump ya yi zargin cewa tsarin shiga da zama a Amurka da ya shafe shekaru yana aiki ya gurgunta tsaron ƙasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya ce tsarin harin ya kuma ɗora nauyi mai tsanani kan makarantu, gidaje da asibitoci a sassan Amurka saboda zuwan 'yan kasashen.

Ya ce yawan ’yan ƙetare da ke shiga Amurka “ya haura miliyan 53”, wanda ya jawo matsalolin da kasar ke fama da su, kamar aikata laifuffuka, kungiyoyin 'yan ta'adda da matsalolin zamantakewa.

Trump ya yi misali da jihar Minnesota, inda ya ce ce ’yan hijira daga Somalia sun canja tsarin rayuwar jihar ta hanyar abin da ya kira “tasiri marar kyau”.

A cewarsa, saboda aika aikar 'yan gudun hijra, wasu mazauna jihar yanzu sun fara tserewa suna barin gidajensu, don tsoron kai musu hari.

Matakan da Trump zai dauka kan bakin Amurka

Kara karanta wannan

Sojar Amurka ta rasu bayan harin da dan bindiga ya kai musu, Trump ya fusata

Ya kuma ce ana samun tsaiko a asibitoci, cunkoso a makarantu da hauhawar kuɗin gidaje saboda tsarin hijirar da yake zargi gwamnatin baya ta bari ya yi sakwa-sakwa.

Jaridar NBC News ta rahoto Trump ya bayyana cewa zai ɗauki matakan da suka haɗa da:

  • Dakatar da ba ’yan ƙetare duk wani tallafi na gwamnati.
  • Hana waɗanda ya ce “suka saba da tsarin Amurka” zama a kasar.
  • Korar duk mutumin da aka ga yana barazana ga tsaron kasar.
  • Hana shigowar sababbin baki daga duk ƙasashen da ya kira masu tasowa, ciki har da Najeriya.

Ya ce “dakatar da shigowar mutane daga ƙasashe masu tasowa” ita ce hanyar da za ta dawo da abin da ya kira daidaito ga ci gaban Amurka.

Jawabin Trump na hana 'yan wasu kasashe zuwa Amurka na zuwa bayan harin Washington DC.
Shugaba Donald Trump ya na jawabi a lokacin yakin neman zabensa. Hoto: @realDonaldTrump
Source: Twitter

Barazanar Trump bayan harin Washington DC

Jawabin Trump ya biyo bayan wani hari da aka kai a birnin Washington, DC, inda aka harbi dakarun sojojin tsaro na kasa, har guda biyu, in ji rahoton Reuters.

An ruwaito cewa mutumin da ake zargi da kai wannan harin, ya shiga Amurka ne a 2021 karkashin shirin ceton sojojin Afghanistan lokacin mulkin Joe Biden.

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana a fusace bayan 'dan bindiga ya harbi sojojin Amurka

Harin Washington DC ya ƙara tayar da muhawara kan tsare-tsaren karbar baki, musamman yadda ake karɓar masu neman kariya daga kasashen da ke fama da rikice-rikice a duniya.

Sojar Amurka ta rasu a harin White House

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata sojar Amurka ta rasu, yayin da wata kuma ke cikin mawuyacin hali bayan harin da aka kai musu a Washington DC.

Hukumomi sun ce wanda ake zargi, Rahmanullah Lakanwal daga kasar Afghanistan, ya jikkata lokacin da jami'an tsaro suke kokarin cafke shi.

Lamarin ya sa Donald Trump ya sake kira da tsaurara dokokin shige-da-fice, har da dakatar da shigowar 'yan wasu kasashe, ciki har da Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com