Trump Zai Sake Tunani kan Kasashe 19 Karkashin CPC bayan Harin ‘White House’
- Hukumar kula da baki a Amurka (USCIS) ta yi magana kan yiwuwar sake fasali kan wadanda kasar ta amince musu sun zauna a cikinta
- USCIS ta ce ta fara duba damar da aka ba mutanen ƙasashe “masu babbar matsala”, bisa umarnin Donald Trump bayan harbin sojoji
- Ma’aikatar Tsaro ta bayyana cewa tana duba dukkan buƙatar mafaka da aka amince da su a zamanin Joe Biden, bayan gano bayanan wanda ake zargi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washinton DC, Amurka - Daraktan hukumar kula da baki a Amurka ya ce akwai yiwuwar sake fasali game da kwararowar baki zuwa cikin kasar.
Ya ce ya ba da umarnin a sake duba duk damar da aka bayar ga mutanen ƙasashen da ake sanya cikin “masu babbar matsala”, bisa umarnin Shugaba Donald Trump.

Source: Getty Images
Donald Trump zai hana wasu baki zuwa Amurka
Rahoton Al'jazeera ya tabbatar da cewa hakan bai rasa nasaba da harin da aka kai kusa da fadar shugaban kasar kan sojoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lokacin da aka tambaye shi waɗanne ƙasashe ake nufi, ya yi nuni ga jerin ƙasashe 19 da wata sanarwar shugaban ƙasa a watan Yunin 2025.
Trump ya yi amfani da harbin sojojin da ke gadin Washington DC domin kare matakin tsauraran dokokin shige-da-fice.
Ma’aikatar Tsaro ta bayyana wa CNN cewa tana duba dukkan abin da ya shafi neman mafaka da aka amince da su a lokacin gwamnatin Joe Biden.
Hukumar ta ce wanda ake zargi da harbin ya shigo Amurka a 2021 karkashin 'Operation Allies Welcome' bayan taimaka wa Amurka a Afghanistan.
Mutumin ya samu mafaka a watan Afrilun 2025, inda jami’an gwamnati suka ce ya wuce duk binciken tsaro tun yayin shigarsa ƙasar.

Source: Getty Images
Kasashen da Amurka za ta sanyawa takunkumi
An jero ƙasashen da ke iya fuskantar barazanar a Amurka kamar haka: Afghanistan, Burma, Chad, Congo, Equatorial Guinea da Eritrea.
Sauran sun hada da Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, Yemen, Burundi, Cuba, Laos, Sierra Leone, Togo, Turkmenistan, Venezuela.
Har ila yau, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta dakatar da shigowar baki daga dukkan ƙasashe masu tasowa gaba ɗaya.
Kasashen da ba su ci gaba ba, waɗanda ke fama da matsalolin tattalin arziƙi, siyasa, zamantakewa da muhalli.
Sauran matsalolin da ake dangantawa da kasashe masu tasowa sun hada da talauci, rashin arziki da ƙarancin manyan albarkatun kasa da za su kawo ci gaba.
Wasu daga cikin irin waɗannan ƙasashe sun haɗa da Sudan, Chadi, Nijar, Benin, Pakistan da Najeriya.
Kisan Kiristoci: Tinubu ya ware tawaga zuwa Amurka
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa tawaga daga Najeriya da za ta shiga kwamitin hadin guiwar tsaro da Amurka.
An ce tawagar za ta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a ziyarar da manyan jami’an tsaro na Najeriya suka kai Washington DC.
Sabon tsarin ya samo asali ne bayan barazanar Donald Trump na aika sojojin Amurka zuwa Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


