Trump Ya Yi Magana a Fusace bayan 'Dan Bindiga Ya Harbi Sojojin Amurka
- Harbin da aka yi wa wasu sojojin Amurka 'yan jihar West Virginia a birnin Washington DC ya sa Shugaba Donald Trump ya sake fusata
- Trump ya danganta lamarin da manufofin gwamnatin Joe Biden, yana cewa an shigo da wanda ake zargin lokacin janyewar sojojin Amurka a Afghanistan
- Ya kuma faɗaɗa suka zuwa ga wasu ’yan gudun hijira daga sauran ƙasashe, ciki har da Somaliya, duk da babu alaka da abin da ya faru da su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaba Donald Trump ya yi sabon alƙawarin tsaurara dokokin shige-da-fice bayan harbin da ya yi sanadin jikkatar wasu sojojin Amurka a Washington DC.
Sojojin sun je birnin Washington DC ne domin aikin da gwamnatin Trump ta fara na ƙarfafa jami’an tsaro.

Source: Getty Images
Fadar White House ta wallafa a X cewa an tsare mutumin da ake zargi, wanda Trump ya bayyana a matsayin ɗan asalin Afghanistan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin bidiyo daga Mar-a-Lago, Trump ya fara yin ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, sai kuma ya karkata zuwa suka kan gwamnatin da ta gabace shi.
Kalaman Donald Trump bayan harbin sojoji
Trump ya yi amfani da harin wajen jingina laifin ga manufofin shige-da-fice na baya, yana cewa wannan ya nuna gagarumar barazana ga tsaro.
Ya yi zargin cewa 'yan Afghanistan da dama da aka karɓo bayan janyewar Amurka suna buƙatar sake tantancewa, yana mai cewa dole ne a duba bayanansu ɗaya bayan ɗaya.
Sai dai kalamansa sun zarce Afghanistan, inda ya yi magana kan wasu ’yan Somaliya da ke Minnesota, duk da rashin wata alaka da abin da ya faru a birnin DC.
Ya bayyana cewa suna “cutar da ƙasa” tare da rusa jihar, yana kuma bayyana Somaliya a matsayin ƙasa marar doka da tsari.
Karin bayani kan harbin sojojin Amurka
Wasu rahotanni daga CNN sun bayyana cewa har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba.
An tabbatar da cewa FBI na bincike, kuma ana fuskantar tambayoyi kan yadda aka tantance mutumin da ake zargi lokacin da ya shiga ƙasar.
A halin yanzu dai, ana ci gaba da neman karin bayani, musamman ganin cewa ɗaruruwan ’yan Afghanistan da aka karɓa sun taimaka wa sojojin Amurka a yakin da ya ɗauki shekaru da dama.
Sabon alƙawarin binciken ’yan Afghanistan
Trump ya yi alƙawarin “sake bincike ɗaya bayan ɗaya” ga duk wani baƙo daga Afghanistan da ya shiga Amurka tun bayan janyewar sojojin Amurka.
Masu suka na ganin wannan zai iya tayar da tsoro ga dubban mutane masu bin doka waɗanda suka yi aiki tare da Amurka da hadarin rayukan su da iyalansu.
An karyata zuwan sojojin Amurka Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa bincike ya gano cewa ikirarin cewa sojojin Amurka sun iso Najeriya ba gaskiya ba ne.
Wani bidiyo aka rika yadawa a kafafen sada zumunta da cewa sojojin Amurka ne suka isa jihar Borno.
An fara yada karyar ne bayan barazanar da shugaban Amurka ya yi ta cewa zai kawo farmaki Najeriya da sunan kare Kiristoci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

