Wasu 'Yan Najeriya 2 Sun Damfari Gwamnatin Amurka, Sun Girbi abin da Suka Shuka

Wasu 'Yan Najeriya 2 Sun Damfari Gwamnatin Amurka, Sun Girbi abin da Suka Shuka

  • Wata kotun Amurka ta yanke wa wasu ’yan Najeriya biyu hukunci bayan kama su da laifuffukan zambar da ta kai $470,000
  • An ce, wadanda aka yanke wa hukuncin, Temitope Bashua da Uchechukwu Eze sun zambaci gwamnatin kasar Amurka kudin
  • Amurka ta ce ana samun yawaitar zambar yanar gizo da ta neman tallafin gwamnati, tare da bayyana matakin da aka dauka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Ma'aikatar shari'ar Amurka ta yanke wa wani dan Najeriya, Temitope Bashua hukunci bayan ya amsa laifin aikata damfara da ta shafi bayanan jama’a.

An tabbatar da cewa ya karɓi fiye da dala 290,000 daga shirye-shiryen tallafi daga gwamnatin Amurka ba tare da izini ko sahihin bayanai ba.

Ma'aikatar shari'a ta yanke wa wasu 'yan Najeriya hukunci kan laifuffukan damfara.
Ministar shari'a kuma Antoni Janar ta Amurka, Pamela Bondi ta na jawabi a Washingdon DC. Hoto: @TheJusticeDept
Source: Twitter

A rahoton da aka wallafa a shafin USAO, kotu ta ce Bashua ya yi amfani da bayanan mutane wajen cika takardun neman bashi da tallafi, wanda hakan ya jawo mummunar asara ga gwamnati.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya gyarawa shugabannin Arewa zama kan rufe makarantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Bashua ya damafari gwamnatin Amurka

Bayan amsa laifinsa, an yanke masa hukuncin watanni 30 a gidan yari da kuma tsatstsauran sa ido bayan ya fito daga kurkuku.

Rahotanni daga kotu sun bayyana cewa Bashua ya yi amfani da bayanan mutane da aka sace domin neman tallafin gwamnati cikin sauki.

An bayyana cewa ya aikata laifin tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022 lokacin da shirye-shiryen tallafi suka kara yawa a Amurka.

Ma'aikatar ta ce ya yi aiki da wasu daga kasashen waje wajen kirkirar bayanan bogi na neman tallafin gwamnati.

Bayan gwamnati ta gano damfarar, an cafke shi tare da duk wasu hujjoji da suka taimaka wajen gudanar da bincike kan damfarar.

Kotun ta daure wani dan Najeriya, Gideon Eze

Hakazalika, rahoton shafin USAO na Amurka ya rahoto cewa kotu ta kama dan Najeriya, Uchechukwu Gideon Eze da laifin damfara ta imel.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Amurka ta yi magana kan sace dalibai a Kebbi da Neja

Rahoton ya nuna cewa ya karɓi kusan dala 182,000 ta hanyar bude asusun bogi da sunan Blue Horizon Automobile LLC.

Kotun Amurka ta tabbatar da cewa ya karɓi kuɗin kamfani ne bayan ya kwaikwayi adireshin imel na asalin kamfanin.

Rahoto ya nuna cewa an kama Eze, dan Najeriya a lokacin da ya ke kokarin sake shiga Amurka bayan ya aikata damfara.
Jami'an hukumar FBI na Amurka sun iza keyar wani laifi. Hoto: @FBI
Source: Twitter

Eze ya gudu daga Amurka amma an kama shi

Bayan kamfanin da aka damfara ya gano badakalar, kuma ya fara bincike, sai Eze ya tsere daga Amurka cikin gaggawa.

Rahoton ya ce Eze ya yi ƙoƙarin sake shiga Amurka ta kan iyakar Kanada bayan watanni shida amma jami’an tsaro suka gane shi.

Bayan cafkarsa, ya amsa laifin damfara kuma aka yanke masa hukuncin watanni 21 a kurkuku tare da biyan diyya.

Mai'aikatar shari'ar Amurka ta ce irin wadannan zamba suna kara yawaita, don haka za a cigaba da sa ido sosai a kan yanar gizo.

An kama dan Najeriya da laifin damfara a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an kama dan Najeriya mai suna, Ehis Lawrence Akhimie da laifin damfarar mutane Dala miliyan 6 a kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Ana maganar Najeriya, an gano yadda Trump ke gallazawa wasu Kiristoci a Amurka

Kotun ta yanke Akhimie hukuncin fiye da shekaru takwas a gidan yari bayan kama shi da laifi a damfarar kudin gado daga fiye da mutum 400.

Bisa bayanan kotu, Akhimie tare da abokan aikinsa sun rika tura wasiku na yaudara ga mutane a Amurka suna yin karyar cewa su jami’an banki daga ƙasar Spain.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com