'Dan Adawar Kamaru, Bakary Ya Tsallake Tarkon Paul Biya, Ya Gudu Kasar Gambiya

'Dan Adawar Kamaru, Bakary Ya Tsallake Tarkon Paul Biya, Ya Gudu Kasar Gambiya

  • 'Dan adawar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary ya isa Gambiya domin neman tsira bayan zaben shugaban kasa da ya janyo tarzoma
  • Gwamnatin Gambiya ta ce ta karɓi Issa Bakary na ɗan lokaci bisa dalilan jin ƙai yayin da ake kokarin sasanta rikicin siyasa a ƙasar shi
  • Zaben da ya maido Paul Biya kan mulki karo na takwas ya haddasa zanga-zanga da mummunar barna a sassan ƙasar Kamaru

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Cameroon - Rikicin siyasa bayan zaben Kamaru ya sanya dan adawa Issa Tchiroma Bakary ya tsere zuwa Gambiya domin neman mafaka.

Zaben Oktoban 2025 ne ya maido Shugaba Paul Biya, mai shekaru 92, kan mulki karo na takwas, abin da ya tayar da kura ga kasancewar an rika zanga-zanga da tashin hankali a kasar.

Kara karanta wannan

Shugaban DSS ya fadi halin tsaron da kasa ke ciki yayin ganawa da Tinubu

Issa tchiroma Bakary na Kamary
Issa Bakary da ya tsallaka zuwa kasar Gambiya. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Al-Jazeera ta ce Tchiroma da ya samu kashi 35.2 na kuri’u, ya yi watsi da sakamakon, yana cewa an yi magudi kuma shi ne ainihin wanda ya ci zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya fara jawo rikici a Kamaru

Babban abin da ya fara tayar da kura a siyasar Kamaru shi ne ikirarin da Bakary ya yi na cewa ya lashe zaben shugaban kasa.

A bayaninsa bayan fitar da sakamakon hukuma, Tchiroma ya ce:

“Wannan ba dimokuradiyya ba ce. Sata ce kawai ta zabe, juyin mulki ne na kundin tsarin mulki a fili kuma abin kunya.”

Ya zargi gwamnati da tafka magudi tare da kiran magoya bayansa da su fito zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da sakamakon.

Ya kuma yi kira da a rufe shaguna da dakatar da harkokin yau da kullum a birane domin matsa lamba ga gwamnati.

Ana ganin cewa wannan umarnin da ya yi ne ya janyo mummunan rikici a wasu yankuna na kasar bayan zabe.

Kara karanta wannan

PDP ta fara adawa mai zafi, ta ragargaji Tinubu kan sace dalibai a Kebbi

Shugaban Kamaru da ya lashe zabe
Shugaban Kamaru, Paul Biya a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Martanin gwamnatin Kamaru ga Bakary

Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewa akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon tarzomar da ta barke.

Sai dai kungiyoyin farar hula da jam’iyyun adawa sun ce adadin ya fi haka, suna zargin jami’an tsaro da amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zanga.

Gwamnati ta sanar da cewa za ta gurfanar da Tchiroma a gaban kuliya bisa zargin “kira ga tayar da hankali da tayar da zaune tsaye.”

Issa Bakary ya gudu kasar Gambiya

A wata sanarwa da ta fitar, fadar shugaban kasar Gambiya ta ce ta karbi Tchiroma domin tabbatar da tsaron rayuwarsa, tare da kokarin neman sulhu a Kamaru.

Sanarwar ta ce Gambiya na aiki tare da kasashen yankin ciki har da Najeriya domin gudanar da tattaunawa da kuma wanzar da zaman lafiya bayan zaben da aka yi ta ce-ce-ku-ce a kai.

Rahoton Yahoo News ya ce wannan mataki na Gambiya ya zo a lokacin da rikicin siyasa ke barazana ga zaman lafiyar Kamaru.

Kara karanta wannan

Muhawara ta raba 'yan majalisar Amurka 2 kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya

Najeriya ta hana a kama Issa Bakary

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kamaru ta so kama dan adawar kasar, Issa Bakary yayin da ya fake a Najeriya.

Bayan fara neman shi a Kamaru, Bakary ya fake a birnin Yola na jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya.

A lokacin da jami'an gwamnatin Kamaru suka so kama shi a Yola, gwamnatin Najeriya ta ki yarda da bukatar hakan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng