Shugaban Amurka, Trump Ya Kara Daukar Zafi, Ya Kira Najeriya da Kalma Mara Dadin Ji
- Shugaba Donald Trump ya kara fusata game da hare-haren da 'yan ta'adda ke kai wa kan fararen hula musamman kiristoci a Najeriya
- Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan farmakin da 'yan bindiga suka kai tare da sace dalibai da dama a jihohin Kebbi da Neja
- Trump ya bayyana Najeriya a matsayin abin kunya, tare da barazanar cewa Amurka za ta dakatar da tallafin da take ba kasar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump ya kara daukar zafi kan kashe-kashen da ake yi a Najeriya, yana mai barazanar dakatar da tallafin da kasarsa ke bayarwa.
Shugaba Trump ya sake nanata cewa ana kashe dubban kiristoci ba gaira babu dalili kuma gwamnatin Najeriya ta gaza daukar matakin da ya dace.

Source: Getty Images
Donald Trump ya soki gwamnatin Najeriya
Donald Trump ya yi wannan furuci ne a shirin ‘The Brian Kilmeade Show’ na Fox News Radio ranar Juma’a, 22 ga watan Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Ina tunanin Najeriya ta zama abin kunya, komai abin kunya ne. Ana kashe mutane dubbai a kasar, wannan kisan kare dangi ne. Kuma ina matuƙar fushi da hakan.
“Muna tura masu kuɗi, kun san muna bai wa Najeriya tallafi sosai wanda za mu daina bayarwa.
"Gwamnatin Najeriya ta gaza tabuka komai, ba su da amfani. Ana kashe Kiristoci babu kakkautawa. Kafin na shiga al’amarin makonni biyu da suka wuce, ba wanda ma yake magana akai.”
Furucin na Trump na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amurka ke ƙara nuna damuwa kan yawaitar hare-haren ta’addanci a Najeriya.
Sace dalibai a makarantar Katolika
A ranar Juma’a, ‘yan bindiga sun kai hari makarantar St. Mary’s Catholic Primary and Secondary School, da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwarra a Jihar Neja.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: An kai karar Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya kan 'kisan Kiristoci'
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Neja ta ce mutum 315 ne aka sace, ciki har da dalibai 303 da malamai 12, kamar yadda The Cable ta kawo.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an tura jami’an ‘yan sanda na musamman, sojoji da sauran jami’an tsaro yankin domin ceto daliban Neja.
Garkuwa da dalibai mata a Kebbi
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan sace dalibai mata 25 daga makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke garin Maga, Jihar Kebbi.
A lokacin harin, mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, ya rasa ransa yayin da Ali Shehu, ma’aikacin tsaro, ya jikkata a hannunsa.

Source: Twitter
Shugaba Trump ya taso Najeriya
A ranar 1 ga Nuwamba, Trump ya yi barazanar tura sojojin Amurka zuwa Najeriya saboda abin da ya kira cin zarafin Kiristoci.
Amma a ranar Juma'a, Shugaba Trump ya sake nuna damuwa kan hare-haren 'yan ta'adda kan kiristoci, inda ya kira da Najeriya da, "Abin kunya."
Amurka ta fara aiki da Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Harkokin Tsaron Amurka, Pete Hegseth ya gana da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
Pete Hegseth ya ce ma’aikatar yaki ta Amurka na aiki cikin gaggawa tare da Najeriya domin kawo ƙarshen abin da ya kira cin zarafin Kiristoci a kasar.
Tun da farko, Shugaba Donald Trump ya yi barazanar tura dakarun Amurka zuwa Najeriya “da makamai domin kawar da ‘yan ta’adda” da yake zargin suna kashe Kiristoci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

