Amurka Ta Fara Canza Tunani kan Shirin Kawo Farmaki Najeriya bayan Ganawa da Ribadu
- Alamu sun nuna Amurka ta fara canza tunani kan batun kawo farmaki Najeriya domin dakile kisan da ake yi wa kiristoci
- Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth ya gana da mai ba shugaban Najeriya shawara kanharkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu
- Bayan tattaunawarsu, Hegseth ya ce Amurka na aiki tare da Najeriya domin kawo karshen kisan da ake wa mabiya addinin kirista
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - A ranar Alhamis da ta gabata, 20 ga watan Nuwamba, 2025, Ministan Harkokin Tsaron Amurka, Pete Hegseth ya gana da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
Wannan ganawa dai wani bangare ne na kokarin da Najeriya take yi na warware zargin kisan kiristoci da Amurka ta yi a kwanakin baya.

Source: Twitter
The Cable ta tattaro cewa taron ya gudana a rana ɗaya da majalisar dokokin Amurka ta gudanar da zaman sauraron zargin cin zarafin Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan
Magana ta fito, an ji abin da ya hana Shugaba Tinubu zuwa Amurka ya gana da Trump
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa shugaban hafsoshin rundunar tsaro ta Amurka, Dan Caine, ma ya halarta.
Amurka da Najeriya za su hada kai
Bayan ganawarsa da Nuhu Ribadu, Ministan tsaron Amurka ya fito ya yi bayani kan halin da ake ciki game da yiwuwar kawo farmaki Najeriya.
Pete Hegseth ya ce ma’aikatar yaki ta Amurka na aiki “cikin gaggawa” tare da Najeriya domin kawo ƙarshen abin da ya kira “cin zarafin Kiristoci da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi ke yi”
Hegseth ya rubuta a shafinsa na X ranar Juma’a cewa:
“Jiya na gana da Mai Ba Shugaban Najeriya Shawara Kan Tsaron Ƙasa da tawagarsa domin tattauna kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a ƙasarsu.
"A ƙarƙashin jagorancin POTUS, Ma’aikatar Yaƙi na aiki tuƙuru tare da Najeriya domin kawo ƙarshen cin zarafin Kiristoci da ‘yan ta’adda ke yi.”
Tun da farko, Shugaba Donald Trump ya yi barazanar tura dakarun Amurka zuwa Najeriya “da makamai domin kawar da ‘yan ta’adda” da yake zargin suna kashe Kiristoci.
Abin da ya kai Nuhu Ribadu Amurka
A kan wannan batu ne shugaban kasa Bola Tinubu ya tura wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin Ribadu zuwa Amurka domin tattaunawa da fahimtar juna.
A cikin tawagar akwai Karamar Ministar Harkokin Waje, Bianca Ojukwu, Sufeto Janar na Ƴan Sanda, Kayode Egbetokun, Antoni Janar kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede.

Source: Twitter
A ranar Laraba, tawagar ta gana da mamba a majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, a birnin Washington.
A yayin zaman, Jonathan Pratt, babban jami’i a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce za su yi aiki tare da gwamnatin Najeriya wajen ɗaukar matakai, ciki har da kafa rundunar hadin guiwa domin magance zargin cin zarafin Kiristoci.
Me ya hana Tinubu ganawa da Trump?
A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan shirin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na kai ziyara Amurka domin gana wa da Donald Trump.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar Tinubu ya je har Amurka ya tattauna da Shugaba Trump.
Ya ce Shugaba Tinubu zai kai ziyara Amurka kuma ya gana da Donald Trump ne a lokaci da kuma yanayin da ya dace da hakan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

