Muhawara Ta Raba 'Yan Majalisar Amurka 2 kan Zargin Kashe Kiristoci a Najeriya

Muhawara Ta Raba 'Yan Majalisar Amurka 2 kan Zargin Kashe Kiristoci a Najeriya

  • Zaman sauraron korafi kan Najeriya ya raba ’yan majalisa, masana da shugabanni kan ko rikicin kasar na da alaka a addini
  • Wasu sun kare matakin shugaba Donald Trump, wasu kuma sun kira barazanar shigar sojoji Najeriya a matsayin ganganci
  • Rahotanni daga wasu 'yan majalisar Amurka sun ce tashin hankalin da ake a Najeriya ya shafi bangarori da dama a fadin kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - A ranar Alhamis, Majalisar wakilan Amurka ta gudanar da zaman sauraron korafi a kan matakin da shugaban ƙasa Donald Trump ya ɗauka na sake sanya Najeriya a CPC.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Amurka ya dauki matakin ne sakamakon zargin kisan Kiristoci da ya yi.

Donald Trump, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Amurka da Donald J. Trump. Hoto: Bayo Onanuga|The White House
Source: Getty Images

Punch ta ce zaman ya gudana ne a karkashin kwamitin harkokin Afirka, inda aka tattauna kan tasirin wannan mataki, haɗarinsa a siyasa da tsaro, da kuma yadda Amurka za ta tsara martaninta.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An kai karar Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya kan 'kisan Kiristoci'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan sanarwar, Trump ya yi barazanar cewa sojojin Amurka za su shiga Najeriya “da makamai” domin kawar da ’yan ta’adda, abin da ya haddasa ce-ce-ku-ce a zaman.

Yadda aka fara zama a majalisar Amurka

Shugaban zaman, Chris Smith, ya kafa tubalin tattaunawar da zargin cewa kaso 89% na Kiristocin da ake kashewa a duniya suna Najeriya, inda ya ce sama da Kiristoci 52,000 aka kashe daga 2009.

Ya yi zargin cewa makiyaya masu tsattsauran ra’ayi suna aikata laifuffukan garkuwa, fyade da kisa “ba tare da ana musu hukunci ba.”

Smith ya ce hare-haren suna da “tushe na addini,” tare da zargin gwamnatin da ta gabata da rage matsin lamba a kan Najeriya lokacin da aka fitar da ita daga CPC duk da shawarwarin USCIRF.

A bangare na farko, Jonathan Pratt da Jacob McGee daga ma’aikatar harkokin waje sun fuskanci tambayoyi masu ɗaci kan yawaitar hare-haren Boko Haram, ISIS, Ansaru da Lakurawa.

Kara karanta wannan

Trump: Wasu 'yan majalisar Amurka sun yi matsaya kan kai hari Najeriya

Pratt ya ce hare-haren da ke kai wa ga Kiristoci na da alaƙa da “gazawar bai wa tsaro muhimmanci,” duk da cewa sojojin Najeriya suna fama da asarar rayuka a Arewa maso gabas.

An yi sabani a majalisar Amurka kan Najeriya

Wani dan majalisar, Bill Huizenga, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da kasa kare Kiristoci,” inda ya zargi kafofin watsa labarai da ’yan majalisa da rage hadarin abin da ke faruwa.

Haka kuma Johnny Olszewski ya nuna cewa gwamnati “ba ta da karfi” wajen kare al’umma, amma ya ce hakan ba ya wanke ta daga alhaki.

Ya jaddada cewa dukkan Musulmi da Kiristoci ne suke fama da hare-haren Boko Haram da ISWAP da sauran 'yan ta'adda.

Donald Trump da Sara Jacobs
Yar majalisar Amurka da ta soki Trump kan batun kai hari Najeriya. Hoto: @RepSaraJacobs|Getty Images
Source: Twitter

Pramila Jayapal ta gargadi masu danganta rikicin da Kiristoci kaɗai, tana cewa hakan “yana saukaka matsalar,” domin bincike ya nuna Musulmi da Kiristoci duk suna shan fama.

Vanguard ta rahoto ta ce tana da damuwa da yadda Trump ya mayar da martani bayan wani rahoto da aka watsa a talabijin.

A nata bangaren, Sara Jacobs ta soki barazanar Trump cewa Amurka za ta shiga Najeriya da sojoji domin “gamawa da ’yan ta’adda.” Ta ce rikicin ba na addini ba ne kacokam.

Kara karanta wannan

Ribadu da manyan Najeriya sun isa Amurka, sun tattauna batun rashin tsaro

Jacobs ta ce juya lamarin zuwa rikicin addini “na iya kara tayar da tarzoma,” tana gargadi cewa barazanar Trump ta riga ta haifar da karin gajiyawa tsakanin Kiristoci da Musulmi a Najeriya.

'Rikicin Najeriya ba na addini ba ne,' Minista

A wani labarin, kun ji cewa ministan yada labaran Najeriya, Mohammed Idris ya bayyana cewa rikicin Najeriya ba na addini ba ne.

Ministan ya fadi haka ne a ranar Laraba yayin da ya ke martani game da harin da aka kai jihar Kebbi da Kwara.

Mohammed Idris ya bayyana matakan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke dauka domin magance matsalar tsaro a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng