Ana Wata ga Wata: Jam'iyyar APC Ta Aika Wasika zuwa Majalisar Dokokin Amurka
- APC ta fara bin matakan neman izini domin tura tawaga majalisar dokokin kasar Amurka kan zargin gallaza wa kiristoci a Najeriya
- Shugaban APC reshen Amurka, Farfesa Tai Balofin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja
- Ya ce bayanan da Amurka ta samu kan matsalar tsaron Najeriya ba haka abin yake ba, domin ya shafi kowane dan kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Jam'iyyar APC reshen Amurka ta bayyana shirinta na gabatar da shaida a gaban kwamitin da ke kula da harkokin Afirka na Majalisar Dokokin kasar Amurka.
APC ta fara wannan yunkuri ne yayin da 'yan Majalisar Amurka suka fara duba matakin Shugaba Donald Trump na sanya Najeriya a jerin kasashen da ke gallaza wa mabiya addini.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa APC reshen Amurka ta bayyana cewa a shirye take ta tura tawaga zuwa Majalisa domin gabatar da hakikanin abin da ke faruwa a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta tura wasika Majalisar Amurka
A wata wasika da suka aikewa shugaban kwamitin, Chris Smith, APC USA ta ce a shirye take ta tura tawaga mai ƙarfi don gabatar da abin da ta kira “hakikacin bayanan sirri,” kan matsalar tsaro a Najeriya.
Shugaban APC USA, Farfesa Tai Balofin, ya tabbatar da wannan a wata sanarwa da aka fitar daga Abuja, inda ya bayyana cewa suna son bayani ya kai ga Amurka ba tare da kuskuren fahimta ba.
A rahoton Guardian, Farfesa Balofin ya ce:
“Muna goyon bayan ’yancin addini ga kowane ɗan Najeriya, amma labaran da ake yadawa a kasashen waje ba sa nuna hakikanin yanayin rikicin da ake fama da shi a kasarmu.
“Tashe-tashen hankulan Najeriya ba addini kaɗai ne yake haifar da su baz akwai hare-haren ’yan bindiga, rikicin ƙasa da albarkatun ƙasa, sauyin yanayi da kuma laifuffukan ƙetare iyaka.
"Dole Majalisar Amurka ta samu hakikanin alkaluma na gaskiya kafin ta yanke hukunci.”
Wane bayani APC za ta yi wa Amurka?
Balofin ya ce shaidar da za su bayar a Majalisar Amurka za ta bayyana abin da suke gani a matsayin ci gaba a bangaren tsaro karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
APC USA ta ce za ta kuma ba da shawarar karfafa haɗin gwiwar Amurka da Najeriya a fannin tsaro, musayar bayanan sirri, da tallafin jin kai.
Balofin ya kara da cewa:
“Hon. Chris Smith ya shahara wajen kare haƙƙin dan adam da ’yancin addini. Muna roƙon a ba mu dama mu taimaka wajen bayar da bayanai na gaskiya da hanyoyin mafita.”

Source: Facebook
Tawagar Najeriya ta dura Amurka
A wani labarin, kun ji cewa tawaga mai ƙarfi daga gwamnatin tarayya ta isa Amurka domin bayyana matsayar Najeriya kan zargin da ake yadawa na kisan kiristoci.
Tawagar da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya jagoranta ta gana da dan majalisar Amurka, Riley Moore.
Gwamnatin Najeriya ta sha kokarin yin karin bayani kan cewa rikice-rikicen da ake fama da su a kasar ba na addini ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


