Yahudawa Sun Kona Masallaci a Isra'ila bayan Rubutun ‘Batanci’ ga Annabi SAW

Yahudawa Sun Kona Masallaci a Isra'ila bayan Rubutun ‘Batanci’ ga Annabi SAW

  • Wasu Yahudawa sun kona wani masallaci a Yammacin Kogin Jordan, inda suka lalata gine-gine tare da rubuta kalaman batanci a bangon masallacin
  • Bidiyon da ya yadu ya nuna masallacin da ya lalace, yayin da hukumomi suka fara bincike, kana shugabannin Isra’ila suka la’anci harin
  • Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da lamarin, inda tashin hankali tsakanin Falasɗinawa, Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi da sojojin Isra’ila ya ƙaru

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jerusalem, Israel - Wasu majiyoyi sun ce Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun ƙone wani masallaci da ke Yammacin Kogin Jordan.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi rubutun cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci, lamarin da ya tayar da hankula.

An kona masallaci a kasar Isra'ila
Fira Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a yayin taro. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

Yahudawa sun kona masallaci a Isra'ila

Rahoton ABC News ta ce rundunar sojin Isra’ila ta ce tana binciken al’amarin, yayin da ba a samu rahoton mutuwa ba, sai hotunan masallacin da ya lalace a faifai.

Kara karanta wannan

Tsofaffin Janar sun nuna fushi kan Wike game da rikici da sojan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun bar rubuce-rubucen batanci da suka fesa da fenti wanda ya saba doka a kasar.

An tabbatar da cewa mummunan lamarin ya afku ne a jiya Alhamis 13 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da muke ciki.

Hukumomi a Isra'ila sun yi Allah-wadai

Shugaban Isra’ila Isaac Herzog ya bayyana harin a matsayin “mai matuƙar daure kai,” yana mai cewa laifin da ’yan ƙalilan suka aikata ya “saba ka’ida.”

Babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Eyal Zamir, ya goyi bayan kalaman Herzog, yana cewa rundunar sa “ba za ta lamunci ayyukan wasu ’yan ƙalilan masu laifi ba.”

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya la’anci harin, yana danganta karin tashin hankali da ya fara tun daga yakin Gaza na 2023.

Yahudawa sun kona masallaci a Isra'ila
Wani Musulmi yana duba barnar da aka yi a cikin masallaci a Isra'ila. Hoto: Mew York Times.
Source: Youtube

Yadda rikici ke karuwa tsakanin Falasdinawa, Isra'ila

Tun bayan wannan lokaci, hare-haren Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi da rikicinsu da Falasɗinawa da sojojin Isra’ila sun ƙaru a Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda New York Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi wa Wike rubdugu kan gardama da sojojin Najeriya a Abuja

Rundunar sojin Isra’ila na yawan fuskantar suka bisa zargin gazawa wajen hana irin waɗannan tashin hankula da ake ce sukan lalata zaman lafiya a yankin.

Batanci dai ga Manzon tsira SAW na tayar da tashin hankali a tsakanin Musulmi wanda suke ganin hakan kamar neman tsokana ne.

Kasashen duniya da dama suna Allah-wadai da irin wannan lamari musamman na batanci ga Annabi SAW da kuma taba wani addini da ake ganin ana neman take musu hakki.

Sojojin Isra'ila sun farmaki Musulmi a masallaci

Mun ba ku labarin cewa rahoton da muke samu daga kasashen ketare na nuni da cewa jami'an tsaron Isra'ila suka farmaki Falasdinawa a Qudus.

Wannan lamari bai yi dadi ba, domin kuwa ya kai ga harbin mai gadin masallacin a ido da harsashin roba wanda ya bar shi cikin rauni.

Hakazalika, rahotanni sun bayyana cewa, akalla mutane 117 ne daga cikin Falasdinawa suka jikkata sakamakon harin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.