Batanci ga Annabi: An tsaurara matakan tsaro yayinda kotu ke shirin yanke hukunci a Kano

Batanci ga Annabi: An tsaurara matakan tsaro yayinda kotu ke shirin yanke hukunci a Kano

- An tsaurara matakan tsaro yayin da kotu ke shirin yanke hukunci kan karar da aka daukaka kan hukuncin da Kotun Musulunci ta yanke wa matasan da suka yi batanci ga Annabi

- Da fari an shirya yanke hukuncin da karfe 12:00 na rana amma sai aka samu tsaiko

- Wadanda ake shari'a a kan su sune Yahaya Aminu Sharif mai shekaru 22 da wani yaro dan shekara 13, Umar Faruk

Wata babbar kotun jihar Kano na shirin zartar da hukunci a kan wasu shari’a biyu na batanci a Manzon Allah da ke gabanta.

An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun wacce ke cike da lauyoyi, hukumomin kare hakkin dan adam da kuma yan jarida daga bangarori daban-daban.

Da farko an shirya yanke hukuncin da karfe 12:00 na rana amma aka dage shi zuwa karfe 1:30 kamar yadda jami’an kotu suka bayyana.

Batanci ga Annabi: An tsaurara matakan tsaro yayinda kotu ke shirin yanke hukunci a Kano
Batanci ga Annabi: An tsaurara matakan tsaro yayinda kotu ke shirin yanke hukunci a Kano Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi zanga-zanga a Akure kan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya na ficewa daga jihar

Shari’ar sune na Yahaya Aminu Sharif mai shekaru 22 wanda kotun shari’a ta yanke wa hukuncin kisa da kuma na wani yaro dan shekara 13, Umar Faruk wanda aka yankewa shekaru 10 a gidan yari duk saboda batanci ga fiyayyen halitta.

A yayin zaman kotu na karshe a watan Nuwamban shekarar da ya gabata, lauyan masu daukaka kara karkashin jagorancin, Barista Kola Alapinni, ya bukaci babbar kotun da tayi watsi da hukuncin.

Ya nemi hakan ne bisa hujjar cewa ba a yi wa wadanda yake karewa adalci ba, kuma shari’ar ta saba da tsarin dokar kasa.

A bangarenta, lauyar jihar, Barista Aisha Mahud ta bukaci kotun da ta tabbatar da hukuncin karamar kotun da kuma watsi da rokon.

Daga baya ne Mai Shari’a Nasiru Saminu ya sanar da ci gaba da shari’ar a ranar Alhamis 21 ga Janairu, 2021, sai dai kuma an dan samu jinkiri lokacin saboda ranar rasuwar da aka yi masa.

KU KARANTA KUMA: Ga abunda yan Igbo ke so daga Nigeria, Ohanaeze ta bayyana

A hukuncinsa alkalin da ke jagorantar shari’ar, Justis Nasiru Saminu, ya sanar da ci gaba da shari’ar a ranar Alhamis 21 ga Janairu, 2021.

A wani labari, kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Jihar Kaduna, KAEDCO, a ranar Laraba, ya yanke wutar gidan marigayi Shehu Shagari, shugaban kasar Najeriya a jamhuriyya ta biyu, saboda bashin sama da miliyan 6.

Tsohon shugaban kasar ya rasu ranar 28 ga watan Disambar 2018, yana da shekaru 93.

Da ya ke tabbatar da lamarin yanke wutar a titin Sama, gidan tsohon shugaban da ke Sokoto, mai magana da yawun Kamfanin, Abdulaziz Abdullahi, ya ce ba a biya kudin wuta ba tun rasuwar Shagari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel