Turkiyya: An Shiga Zullumi da Mummunan Hatsarin Jirgin Sama Ya Yi Ajalin Sojoji
- Gwamnatin Turkiyya ta tabbatar da mutuwar duka sojojinta da ke cikin jirgin C-130 da ya yi hatsari a kasar Georgia
- Ministan tsaro, Yasar Guler ya ce “jaruman sojojinmu sun yi shahada,” yayin da ake bincike tare da hukumomin Georgia
- Shugaba Erdogan ya nuna bakin ciki tare da taya jaje, yayin da kasashen duniya suka aike da sakonnin ta’aziyya ga Turkiyya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Istanbul, Turkey - Gwamnatin kasar Turkiyya ta tabbatar da mutuwar duka sojojinta da ke cikin jirgin C-130 da ya fadi a kasar Georgia kusa da iyakar Azerbaijan.
Hatsarin ya faru ne a ranar Talata 12 ga watan Nuwambar 2025 bayan jirgin ya tashi daga birnin Ganja na kasar Azerbaijan, kamar yadda Ma’aikatar Tsaron Turkiyya ta tabbatar.

Source: Twitter
An rasa rayukan sojoji 20 na Turkiyya

Kara karanta wannan
Buratai ya gargadi Wike kan rigima da soja, ya nemi ministan Abuja ya ba da hakuri
Rahoton Al Jazeera ya ce ministan tsaro, Yasar Guler, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa “jaruman sojojinmu sun yi shahada,” tare da wallafa hotunansu a cikin kayan soja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar tsaro ta Georgia ta ce jirgin ya bata daga a sararin samaniyarsu ba tare da aikawa da gargaɗin hatsari ba kafin ya fadi.
Jami’an bincike daga Turkiyya da Georgia sun fara nazarin wurin da hatsarin ya faru domin gano musabbabin fadawar jirgin a yankin Sighnaghi.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne hatsarin soja mafi muni da Turkiyya ta fuskanta tun shekara ta 2020, inda jirgin ya fadi kilomita biyar daga iyaka.
Bidiyo daga kafafen yada labaran Azerbaijan ya nuna yadda jirgin ya kama da wuta, ya tashi da hayaƙi, ya bar mutane cikin jimami.

Source: Getty Images
Shugaban Turkiyya, Erdogan ya yi jimami
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana bakin cikinsa, yana taya iyalan mamatan jaje, tare da tabbatar da cewa gwamnati tana tare da su.
Erdogan ya kuma tuna alakar tattalin arziki da soja da ke tsakanin Turkiyya da Azerbaijan, wadanda suka ci gaba da hadin kai tun yakin 2020.
Kasashen duniya da dama kamar Azerbaijan, Georgia, Kazakhstan, Qatar, Masar, Iran, Italiya da Malta sun aike da sakonnin ta’aziyya ga Turkiyya.
Jakadan Amurka a Turkiyya, Tom Barrack, ya nuna goyon bayan kasarsa, yayin da Sakatare Janar na NATO, Mark Rutte, ya aika da sakon jaje.
Kamfanin Lockheed Martin, wanda ya kera jirgin C-130 Hercules, ya bayyana alhinsa tare da alkawarin taimaka wa wajen binciken hatsarin, cewar The Guardian.
An bayyana cewa jirgin C-130 na amfani da injin 'turboprop' hudu, kuma ana amfani da shi wajen daukar sojoji, kayan aiki da sauran kayayyaki a duniya.
Turkiyya ta shiga zaman makoki na kasa, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike domin gano ainihin dalilin da ya haddasa mummunan hatsarin.
Jirgin sama Amurka ya fado kan masana'antu
An ji cewa Jirgin sama mai dakon kaya na kamfanin UPS ya gamu da hatsari jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin Louisville Muhammad Ali a Amurka.
Gwamnan jihar Kentucky, Andy Beshear ya ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin jirgin sun kai tara.
Ya ce a lokacin jami'an kashe gobara na kokarin kashe wutar da ta kama a wurin da jirgin ya fado kuma da yiwuwar a samu karin gawarwaki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

