Bayan Barazanar Trump, Birtaniya Ta Lissafa Jihohi 6 da Ke da Hatsari a Najeriya
- Gwamnatin Birtaniya ta gargadi ‘yan ƙasarta da su guji zuwa wasu jihohin Najeriya saboda ta’addanci, da garkuwa da mutane
- Jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Katsina da Zamfara na daga cikin wuraren da aka hana 'yan Burtaniya zuwa gaba ɗaya
- Birtaniya ta ce ayyukan 'yan bindiga suna ƙaruwa a manyan birane, don haka ta gargadi jama'arta kan halartar tarurruka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Birtaniya - Ofishin harkokin waje na gwamnatin Birtaniya (FCDO) ya sake fitar da sabon gargadi ga ‘yan ƙasar da ke shirin zuwa Najeriya.
FCDO ya fadawa 'yan Birtaniya cewa rashin tsaro ya ƙaru sosai a sassan Najeriya, don haka su yi hattara a duk lokacin da za su je kasar.

Source: Twitter
Birtaniya ta gargadi jama'arta kan zuwa Najeriya
A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnati na GOV.UK ranar Lahadi, jaridar Punch ta rahoto FCDO ta bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Rashin tsaro yana ƙaruwa a duk fadin Najeriya. Ana samun garkuwa da mutane, ayyukan 'yan bindiga da kuma rikicin ƙabilanci a yawancin yankuna.”
Ta bukaci ‘yan ƙasar Birtaniya da su ƙara kula, su sake nazarin hanyoyin tsaro, tare da shirya hanyoyin gaggawa idan an sami tashin hankali.
Jihohin da aka hana 'yan Birtaniya zuwa a Najeriya
FCDO ta hana 'yan Birtaniya zuwa jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Katsina, da Zamfara, tana mai cewa akwai barazanar Boko Haram da ISWAP, musamman a wajen taron jama’a, masallatai, da tashoshin sufuri.
Ta kuma jaddada cewa,
“Ma’aikatan agaji, motoci, da kayan agaji na iya zama abin hari daga ‘yan ta’adda da ‘yan fashi.”
Bugu da ƙari, ta hana 'yan kasar ta zuwa jihohin Bauchi, Kaduna, Kano, Kebbi, Jigawa, Sokoto, Niger, Kogi, Plateau, da Taraba, da kuma wajen birnin Abuja har sai da wani babban dalili.
Birtaniya ta yi gargadi kan ayyukan ta'addanci

Kara karanta wannan
Zargin bai wa 'yan ta'adda kudi: Gwamnatin Kaduna ta fadi yadda ta taimaki 'yan bindiga
FCDO ta ba da shawaear ci gaba da ayyukan soji a Adamawa, Borno da Yobe, inda ta ce akwai yiwuwar hare-haren ramuwar gayya daga ‘yan ta’adda.

Source: Getty Images
A yankin Kudu maso Kudu, musamman a Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River, ofishin ya ce kungiyoyin masu bindiga na kai hare-hare kan matatun mai, tare da yiwuwar garkuwa da mutane da fashi da makami.
A Kudu maso Gabas, ofishin ya yi gargadi cewa kungiyoyin ’yan tada kayar baya suna yin arangama da jami’an tsaro, wanda zai iya shafar baki.
A Kudu maso Yamma — ciki har da Lagos — ta bayyana cewa sata, garkuwa da mutane, da fashi da makami sun zama ruwan dare, musamman a yankin mainland.
Trump zai dauki matakin soja a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya yi barazanar aika sojojin Amurka zuwa Najeriya idan gwamnati ta gaza daukar matakai.
Hakan na zuwa bayan Amurka ta nuna damuwa kan zargin yiwa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, wanda ya tayar da hankula.
Shugaba Trump ya ce zai hana Najeriya tallafin ketare, ya kuma dauki mataki “mai tsauri cikin gaggawa” kan masu tayar da kayar baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

