Cikakken bayani game da aikin dakarun Soji a yankin Arewa maso gabas – DHQ

Cikakken bayani game da aikin dakarun Soji a yankin Arewa maso gabas – DHQ

Wasu mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP su 11 sun mika wuya ga dakarun rundunar Sojin Operation Lafiya Dole a jahar Adamawa sakamakon matsin lamba da suke fuskanta daga Sojoji.

Shugaban sashin watsa labaru na shelkwatar, Manjo Janar Enenche ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 15 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah Ya yi ma Tafidan Ilori rasuwa

A cewar Enenche ko a ranar 10 ga watan Mayu sai da yan Boko Haram suka jibge iyalansu mutum 72 a daidai kofar shiga karamar hukumar Ngala da misalin karfe 8:30 na dare.

A yanzu haka da mayakan ISWAP 11, da iyalan yan Boko Haram din duk suna hannu, kuma za’a dauki matakan da suka dace akan su.

Cikakken bayani game da aikin dakarun Soji a yankin Arewa maso gabas – DHQ
Enenche
Asali: Original

“Idan za’a tuna tsarin kawar da akidar Boko Haram a kan mayakan da suka mika wuya da rundunar Soji ta kirkiro ya samar da gagarumar nasara ta yadda ya kula da mutane 280, wanda a yanzu haka sun koma cikin jama’a suna rayuwarsu, daga ciki akwai yan Nijar 25.

“A yanzu haka akwai mutane 603 dake samun kulawa, kuma zasu gama a watan Yunin 2020, don haka ake kira ga sauran mayakan Boko Haram su mika wuya domin su samu kariya, kuma ana kira ga iyaye da shuwagabannin gargajiya su kula da yaransu don gudun shiga kungiyoyin ta’addanci.” Inji shi.

Kakaakin ya ce Sojoji sun halaka wasu yan kunar bakin wake guda 3 a garin Limankara cikin karamar hukumar Gwoza, kamar yadda suka kashe yan ta’adda 28 a makon data gabata.

Haka zalika a ranar 9 ga watan Mayu Sojoji sun kashe yan ta’adda 20 a wani musayar wuta da suka yi a Pulka-Ngurusoye gab da garin Bama.

Bugu da kari Sojojin Operation Lafiya Dole sun kashe yan Boko Haram 9 a yankin Mainok-Jakana na karamar hukumar Kaga na jahar Borno, inda suka kwace motocin yaki 2 da bindiga 1.

Sojojin basu tsaya nan ba, inda a ranar 11 ga watan Mayu a garin Tumbun Fulani a karamar hukumar Abadam sun kashe yan ta’adda da dama, tare da lalata motocinsu da sansaninsu.

A wani labarin kuma, dakarun Operation Whirl Stroke sun kai samame a ranar 12 ga watan Mayu a garin Agasha na karamar hukumar Guma inda suka kashe yan bindiga makiyaya guda 4.

Sojojin sun kwato bindigu 2 kirar AK-47 da alburusai da dama, don haka shelkwatar ta nemi jama’a su bata sahihan bayanai game da ayyukan miyagun mutane don yin maganinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel