Koriya ta Arewa Ta Yi Barazanar Luguden Wuta bayan Jin Motsin Amurka Kusa da Ita
- Koriya ta Arewa ta yi gargadin ɗaukar matakan kai hari kan abokan gaba bayan isowar jirgin yaƙin ruwan Amurka Koriya ta Kudu
- Rahoto ya ce barazanar ta zo ne kwana guda bayan Koriya Ta Arewa ta harba makamin roka mai gajeren zango zuwa cikin teku
- Kasar ta zargi Amurka da Koriya Ta Kudu da haɗa kai wajen haɗa makaman nukiliya da na wasu kayan yaki don tsoratar da ita
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
North Korea - Gwamnatin Koriya Ta Arewa ta yi barazanar ɗaukar matakan kai hari kan abokan gaba bayan isowar jirgin yaƙin ruwa na Amurka, USS George Washington kusa da ita.
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya isa yankin ne tare da rundunar soji a tashar jiragen ruwa ta Busan, Koriya Ta Kudu.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta rahoto cewa ministan tsaron ƙasar, No Kwang Chol, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da gidan talabijin na ƙasar, KCNA, ya ruwaito a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin ya zo ne a daidai lokacin da Koriya ta Arewa ta harba makamin roka mai gajeren zango a ranar Juma’a, abin da ya tayar da hankalin ƙasashen makwabta da Yammacin duniya.
Barazanar da Koriya ta Arewa ta yi
No Kwang Chol ya ce ƙasarsa za ta dauki matsaya wajen kai hari domin kare kanta daga duk wata barazana.
“Za mu dauki matakin kai hari kan duk wani abu da ya zama barazana ga tsaronmu, bisa ƙa’idar tabbatar da tsaro da kare zaman lafiya da ƙarfinmu,”
- Inji shi.
Ya ƙara da cewa, duk wata barazana da ta shafi yankin tsaron Koriya Ta Arewa za ta samu martani na kai tsaye da magance ta ta hanyar da ta dace.

Kara karanta wannan
'Abin da zan faɗawa Trump ido da ido, idan na haɗu da shi': Barau Jibrin ya fusata
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Amurka ta saka takunkumi kan mutane takwas da kungiyoyi biyu da ake zargin suna da alaka da Koriya ta Arewa.
Zargin Amurka da Koriya Ta Kudu
Ministan ya kuma zargi Amurka da Koriya Ta Kudu da haɗa kai wajen haɗa makaman nukiliya domin haifar da barazana ga Koriya ta Arewa.
“Mun fahimci cewa Amurka ta yanke shawarar tsayawa kai tsaye a gaban Koriya ta Arewa don faɗa, kuma ba za mu ji tsoron martani ba,”
- Inji No Kwang Chol
Rahoton Reuters ya nuna cewa jawabin ministan ya biyo bayan taron shekara-shekara na tsaro tsakanin Koriya Ta Kudu da Amurka.

Source: Getty Images
Haka kuma, zuwan jirgin yaƙin Amurka da kawayensa a Busan ya zo daidai da fara atisayen haɗin gwiwa na soja mai suna Freedom Flag da sojojin Amurka da Koriya Ta Kudu ke gudanarwa.
Amurka ta ce ta san da kai hari Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa Amurka ta bayyana cewa tana da masaniya kan harin da Isra'ila ta kai Iran a Yunin 2025.
Shugaban kasar, Donald Trump ne ya bayyana haka yayin ganawa da wasu 'yan majalisar Amurka a Washintong.
A lokacin da Isra'ila ta fara kai harin, Amurka ta yi ikirarin cewa bata san da shi ba kuma babu hannunta a ciki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
